💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...50*
......" In baka shawara?"
Cak ya tsaya da tafiyar duk da kuwa naga alamun cikin hanzari yake kasantuwar shigan lokacin da ya riske shi ya kuma haifar masa da makara, yana da ba'kin da zasu gana da wannan safiyar ne shiyasa kuma hanzarin nasa ya sake ta'azzara.
Ban jira ya juyo ba na 'dora da fa'din " Kar ka hau motar nan taka yau ka fara bincika ta tukunna...".
Cikin tsanaki ya juyo ya dube ni cike da tsananin mamakin jin kalaman baki na, yayin da zuciyar sa ke sake shiga ru'dani amma ya basar.Yayin da ni kuma nayi 'kasa da kaina dan bana san 'kwarin gwiwa ta ta barni.
" Hakan shawara ce...?"
Da kai na bashi amsa alamar" erh".".. _Bisa wani dalili kenan?_
Sai kuma ya girgiza kansa ya canza maganar da fa'din" _I mean hujja_ ...?"Shiru nayi, na rasa ma me zance masa ne.
Da gaske ya kamata ace ina da hujja kafin bashi shawarar saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo amma..amma ai hujja ta tanadaddiya ce, tabbbas ina da hujja amma shin idan na fada zai fahimce ni ko kuwa..?"
Na tambayi kaina.Toh ma idan bai fahimce ni ba rayuwar waye take cikin ha'dari..? shine!
Idan bai 'dauki shawara ta bama kansa ya yiwa ba bani ba.
Wata 6arin zuciyar tawa ta ayyana hakan.Sai dai bazan so faruwar hakan ba sam, ko bakomai shi jinin Ammi ce, bazan so ganin ta cikin 'kunci dai- dai da 'kwayar zarra ba, kuma na tabbatar duk ranar da akace babu shi na tabbatar Ammi sai ta shiga wani hali.
" Ni dai dan Allah.."!
Na tsinci la66ana na motsawa wajen furta hakan cike da marairai ta batare da na shirya ba.Kallo na ya tsaya yi batare da ya furta wata kalma ba.
A hankali kamar bansan maganar nace" ka canza masu kulawa da ku.."
Bansan meyasa ba amma haka kawai naji zuciya ta bata amince da su ba, duk da bansan inda 'karshen maganar zai tsaya ba amma ni dai inaji araina in fa'da masa koda hakan zai iya sanadin tawa rayuwar ne, zan yi ne saboda Allah da kuma Ammi.'Dan ha'de rai Rayyan yayi da alamun wani sabon mamakin kuma, sai dai maganar tata ya hana mamakin nasa bayyanuwa.
Wai.. _masu kula da kai..._
me yarinyar nan ke nufi?Tana nufin su Huzaifa zan canza ko me?..
Ya tambayi kansa.
Yaushe ma na basu damar bibiya ta, yaran da a yini bai fi mu hadu sau biyu ba, gidan ma yaushe suke shigowa sam bai amince da cewar su bayyana kansu matsayin masu bashi kariya ba, a ganin sa babu kariyar da tafi ta mahallici, amma duk da hakan bazai watsawa Ammi kasa a idanu ba kamar yadda ta bukata, hakan yasa ya barsu a matsayin da suke kai ake kuma biyan su.Kawar da kansa gefe yayi batare da ya sake furta komai ba.
Hannun sa ya 'dago ya dubi agogon sa sai kuma ya saka yayi waje.Nayi tsayuwar fin mintina ashirin bayan fitar ban iya na sake motsawa ba, tunani na ma sai ya hargitse gaba 'daya.
" Me ma na fa'da ne?"
Na tambayi kaina a fili.
A hankali duk abinda na fa'da masa suka fara dawo min.Ro'kon Allah nake Allah yasa ban furta abinda zai zame min matsala anan gaba ba.
Tsabar shiga ru'du ban ma san lokacin da ya bar gidan ba, sai uban sara da kaina yake.
Tuno wani abun ya sani fita da sauri na fito harabar gidan...wajen ajiyan motoci na duba ga mamaki na motar bata nan.
Wani sara naji kirjina ya min.
Kar dai bawan Allahn nan bai 'dauki shawara ta ba..?"Wata zuciyar tawa ce ta amsani da fadin..." baki fa'di abu da 'kwakkwaran hujja ba taya zai 'dauki shawarar ki..?"
Innalillahi amma ai ni na gani da ido na, naga mutum 'karkashin motar sa sannan kuma ya fito yayi 'yan dube dube kafin ya 6acewa gani na.
Sai da safiyan nan ne ma dana zurfafa tunani naga yanayi da zubin sa kamar 'daya daga cikin ma'aikatan sa ne, duk da bawai sanin tsab nai musu ba amma yau da gobe ta wuce wasa.
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....