💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*_Wattpad@_
_Serlmerh-md_🅿️ *...31*
......Koda ta idar da sallar bata tashi a wajen ba, komawa tayi ta kwanta bisa daddumar ta lumshe idanu, tunanin rayuwar ta ne yake dawo mata daki daki, 'kwalla ne suka fara gangaro mata tayi saurin goge su.
" Ya isa haka nan!, kukan nan ya isa"
Ta furta cikin ranta cike da bawa kanta 'kwarin gwiwa.
" Mene ma ribar shi?"
Ta sake tambayar zuciyar ta.
Bude idanu tayi ta sauke su kan Mufee dake wasa da 'dan 'karamin kwalin waya da bata san ko wacce iri ba ce ba ta dai tabbatar da kwalin waya ne duba da ganin hoton wayar da tayi a jiki, daga hannayen yarinyar fuskar ta maida duban ta har kullum kaunar ta sake ninkuwa mata yake a zuciya ita da kanta tana mamakin kanta lokuta da dama.Daidai da rana guda bata ta6a ji yarinyar ta ishe ta ba, bata san meyasa ba, duk da irin tarin qalubale da ta fuskanta amma bata ta6a jin sa6anin 'kauna game da yarinyar ba..ko meyasa?
Wani 6ari na zuciyar ta ne ya bata amsa da fa'din.." Saboda ita 'din marainiya ce.."
" Tabbas hakane!
Ta tabbatarwa kanta.
" Mufee na marainiya ce..ni kuma uwa ce zan kuma zame mata uba da kowa data rasa a duniyan nan...".
kusan kowani lokaci alwashin da Zaitun ke ci kenan ko bata furta a fili ba takan ayyana cikin ranta ta kuma tabbatarwa ranta cewar tabbas zata iya.Kwanan ta biyu cikin gidan bata samu matsala ta kowani fanni ba, babu wanda ya takura ta ko ya shiga rayuwar ta, babu wanda take hira da shi sai Mufee duk da yake dama ita ba gwanar surutu ba ce amma haka kawai sai taji zaman shirun ya ishe ta, bata da matsala wajen abinci sbd sau uku ukun nan kullun ake bata abinci Hajja Ladi ke wannan hidimar wanda ta tabbatar bisa umarnin Hajiyar gidan ne.
'Bangaren Mufee ma bata samu matsala da ita ba dan tana cin duk abinda ta bata yanzu ko da babu yawa, dan har ayanzun Mufee ba cin abincin kirki take ba, 'dan banzan za6e ne da yarinyar, kuma in abu bai mata ba bata ta6a cin sa shiyasa a cewar Zaitun har yanzu bata da kumari tana nan 'karama da ita amma matukar zata ga yarinyar cikin walwala da kuzari hankalin ta kwanciya yake ta mance da duk damuwar da take ciki, sam ita bata ta kanta ma.
Sai dai kuma tana jin bazata iya zaman gidan nan ba, bata son takura ko damuwa yanzu a rayuwar su bata son karin wata matsala makamanciyar wadda ta fito cikin ta kwanaki 'kalilan baya...aiki take so tayi burin ta taga ta fara tara ku'din mota dan hankalin ta ya fara komawa gida, burinta kafin cikar lokacin da ta 'debar musu na komawa ga ahalin nata ya zaman ace tana da isashshiyar ku'din motar da zata kaisu ba tare da wata gargada ba.
Duk da yake har cikin zuciyar ta taji ta yadda da matar da ta dauko tan amma ai tun ranar da ta kawo ta ta fita bata sake ganin ta ba balle tasan matsayin zaman ta tare da su.
Shiyasa wasi- wasi ya kasa barin zuciyar ta, ta riga ta yanke cikin ranta cewar barin gidan shine maslaha a gare ta da ma rayuwar ta.Sai dai wani 6ari na zuciyar ta na jin shakka, wancan daren tsoron faruwar makamanciyar sa take, tana tsoron mummunar 'kaddarar da zata iya fa'da mata tunda ta jima da lura rayuwar ta cike take da 'kaddarori masu matukar yawa, amma duk da haka tana matukar so da 'kaunar mutuncin ta, tana kuma iya 'ko'karin ta wajen kare shi..a kullum fatan ta shine Allah ya bata kariya ta wannan fannin, ya basu ikon cinye dukkan jarabawar su batare da sun cutar da wata halitta tasa ba, ba kuma tare da sa6a wa umarnin sa ko keta haddin islama ta kowacce fanni ba.
Ko cikin dare bacci na yanke mata dalilin tunani da damuwar makomar ta da kuma kaddarar ta ta gaba, fatan ta kawai shine Allah ya sassauta mata koda wata kaddarace yasa komai yazo mata da sauqi..bacci 6arawo ne yayi gaba da ita batare da ta sani ba sakamakon 'karancin bacci da take fuskanta a kwanakin shiyasa kusan duk lokacin da ta samu natsuwa ta zauna shiru bacci ke kawo mata hari.
![](https://img.wattpad.com/cover/319462577-288-k576859.jpg)
ESTÁS LEYENDO
BINTEEE ( 'Yata ce)
Ficción GeneralSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....