💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...80*
........" Sai yau aka ga daman zuwa duba ni...?"
Yace yana duban fuskar ta bayan ya amsa sallamar da tayi.
Zaitoon baki ta 'dan tura gaba tana mai kawar da kanta gefe.
" even once Zaitoon..? ko mafarkin ki bai raya miki cewar kizo ki duba ya nake ba? kika mance da ni baki tunanin cewa akwai wani bawan Allah da ya dace ki san halin da yake ciki ba? ya nk ya na kwana? lpy ta ko babu duk ba shine gaban ki ba yarinyar kice kawai damuwar ki ko?
Ni yadda nake ganin kk 'kaunar Mufeeda ma yana sa inji na rasa hope kwata kwata, sai inga kamar bb wani wanda zai iya sake samun gurbi cikin zuciyar ki makamanciyar ta Mufeedah...tunda gashi ina shirin mutuwa ma amma ba'a damu da ko zuwa gani na ba.."
" Ba kaine kace baka son Mufee na akashe min ita ba.."
Ta bashi amsa da dukkan gaskiyar ta da sanyin sauti.
Rayyan yace
"..akan hakan kk ta fushi dani dama..?"
Ya tambaya yana 'dan waro idanu akan ta.
Kanta ta 'dauke..cikin sanyin murya me cike da jin haushi tace" cewa fa kayi su kashe min ita, me yasa ba kace ni ba a lkcn? kasan yanda naji cikin zuciya ta ne a daka furta hakan? ji nayi tamkar kaina zai tsage gida biyu Allah kamar raina baya jiki na, da ace sun kashe min ita a wancan ranar da ban san halin da zan iya tsintan kaina ba..."
Ta 'karashe maganar hawaye na gangaro mata sosai.Jikin sa sanyi 'kalau yayi, gaba 'daya yaji mutuwar jiki ta ziyarce shi da jin kalaman nata, domin ya fahimci da iya gaskiyar ta take maganar.
Tasowa yayi ya zago ta bayan ta ya tsaya yana duban ta sosai.
So yake ya janyo ta ya rungume amma baya so ta fassara manufar sa zuwa ga wani abu daban.Hannun sa ya 'dago ya janyo nata da shi zuwa bakin gadon da ya taso sai da ya koma ya zauna sannan a hankali ya shigar da ita cikin jikin sa ya zagaye ta da hannuwan sa.
Jin ta cikin jikin sa ya sa ta fara 'ko'karin fita 'kwantan kanta amma ta kasa, a kunne ya ra'da mata " Shiiii...calm down please, u ar still my wife remember..?"
Bata fahimci abinda yace 'din ba sam amma haka kawai sai ta ji ranta na raya mata tamkar garga'di yai mata, a fili ta saki ajiyar zuciya tana mai cigaba da 'kara sautin kukan ta.
Tsawon mintina biyu suna a hakan tana a jikin sa yana ayyana irin wannan 'kaunar, ganin kamar bazata sarara bane ya sa da sigar rarrashi yace"...i'm sorry..ba nufi na kenan ba kinji...but nasan bazaki ta6a fahimta ta ba? amma in zaki min adalci ki kwatanta da kanki if akace ki za6a tsakanin ni da Mufeedah wa kk ganin zaki za6a..?"
Wani kallo ta 'dago tayi masa da ita kanta bata san ma'anar ta ba...
Bai damu ba ya 'dan yi guntun murmushi yana duban idanun ta da frawning nd crying face 'din ta yace" I know...na riga na sani...ni bani da wannan darajar in dai a wurin ki ne but yadda zaki ji a zuciyar ki idan za'a rabaki da Mufeedah nima hakan naji koma fiye da naki a lokacin, kuma akan kowanne daga cikin ku ba wai mutum 'daya ba, kawai nabi dacewa ne, na kuma cire son zuciya...i can't afford loosing u both sbd mabambantan matsayi da kuke da shi a wuri na, but a rayuwa akwai cancanta da halacci, sharri kansa ba'a mancewa da shi cikin sauki balle khairin da ka tabbatar domin Allah aka yisa, manufa ta rama khairan ne Zaitoon ba wai dan bana so ko kaunaf Mufeeda ba, nasan ko da na rasa ta Insha Allah watarana zaki haifa min wasu kamar ta...amma ke 'din idan na rasaki shikenan na rasa ki kenan har abada, na rasa wani 6angare ne na rayuwa ta, na kuma yiwa 'ya'ya na hasarar uwar da ta dace...ki fahimce ni ki fahimce ni...."Kawar da kai tayi tana mai share hawayen da ke sau'ko mata, sosai ya 'daure mata kai da kalaman nasa, yayin da ta wani 6angaren ta fahimce shi ta kuma fahimci girma da darajar da take da shi a wurin sa, wanda take kyautata zaton bakomai yasa hakan ba face bautar da tayi masa har yake ikirarin khairan ya kuma so maida mata da takuicin sa ta hanyar bata damar cigaba da rayuwa a dunia, ha'kika ta ji dadin hakan domin ta fahimci shi kansa yasan ta bautu akan sa, duk da domin Allah tayi, amma kayi a yaba maka ma wata sabuwar nasarar ce.
CZYTASZ
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....