P25

81 8 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...25*

              .....A hankali ya sau'ke labilen windon 'dakin nasa yana sakin 'karamar ajiyan numfashi wacce zahiri a hakan zaka iya kiran  ta amma a badini shi ka'dai ya san zafin da hakan yake masa a kirji da cikin zuciya, rabon da yayi farin ciki da wahala tun rabuwar sa da Zaitun na farko, raban da aga cikakkiyar fara'a kan fuskar sa koda ta ya'ke ce tun ranar da yaji sunan wanda mahaifi yake gareshi a kotu matsayin shugaba kuma mai 'daukan nauyin ta'addanci, duk da yake ba wata kwakkwarar ala'ka ko shakuwa ke tsakanin su ba amma sosai abin ya dame sa ya kuma tsaye masa a zucia..wannan kalma ta iyaye mahaifi da mahaifiya ba 'karamin tasiri suke da shi azuciyar kowani halitta ba, duk yadda yakai ga tsanar halayyar mahaifin nasa amma deep down yana jin kauna da kewar rashin shakuwa dake tsakanin su, sai dai munanan halayen mahaifin nasa su suka han komai yin tasiri game da shi.

Gaba 'daya sai ma ya kuma ji mutumin ya sake fice masa aka, musamman da ya kasance dalilin damuwar halayyar sa yasa ya sake rasa damar ganawa da Zaitun a karo na biyu, meyasa a ko wani lokaci da gi6i yake barin zuciyar sa ne? meyasa koda wani lokaci rashin nasara ke gilmawa tsakanin sa da mahaifin nasa? meyasa son zuciya da son kansa sukai masa yawa? meyasa sam bashi da tausayi cikin zuciyar sa? meyasa, meyasa abubuwa da dama?

Idanu ya lumshe fahimtar da yayi cewa hawaye ke bin fuskar sa, aikin kenan, abinda a mafi yawan lokuta ke faruwa matukar haduwa ta hada shi da mahaifin nasa shine zubda kwalla, kusan a kaf 'din rayuwar sa mahaifin nasa shine mutun na farko da ya kasance me sashi zubar da kwalla, in dai kaga Adam na hawaye toh yaci karo ne da takaicin 'daya daga cikin halayyar mahaifin sa dalili kenan da ya sa a mafi yawan lokuta yake kalubalantar ha'duwa da shi.

Akan mutun me irin wannan 'dabi'a shine Hajiya zata yi iya bu'dan baki har tayi tutiya da alfahari dan sun kasance makusantan sa?, shin mancewa Hajiya tayi ne da wuri haka?
Xuciyar sa ke zayyano masa wannan tambayar yana dafe da kansa.
Mutun irin wannan shine Hajiya take kafa hujja dashi cike da ya'kini ta shiga tsakanin sa da Zaitun a wani dalili...?
Sam bai san ma miye ya canza Hajiyar tasa har haka ba, ba mamaki kwata- kwata ta mance ne da waye asalin Jibrin 'Dan Maliki a gareta, may be ta mance ba'kin cikin da ya dasawa zuciyar ta abaya.

Da bayan yatsar hannun sa manuniya ya 'dauke 'kwallan da ke bin idanun sa yana me zama bakin gadon sa ha'de da lumshe idanu...tunanin rayuwar sa ta baya ya fara dawo masa cikin kwakwalwa.

           ~~~~Cikakken sunan sa shine _Adam Shaheed Jibrin 'Dan- Maliki_ , ya kasance 'da kwara 'daya tilo ga mahaifin sa da ake kira 'Dan Maliki tun zamanin kuruciya, shi kadai kuma ya mallaka a fa'din duniya baki 'daya, duk da yake bai taso gaban mahaifiyar sa ba amma bai ta6a kokawa saboda rashin gata ko kan wani abin ba, hasalima bai taso yaga mahaifiyar sa ba sai dai a photo, bai ta6a jin sautin muryar ta ba sanadiyyan rasuwa da tayi tun bayan da ta haife shi duniya tace ga garinku nan.

Yana taso ne gaban makwafi agare ta, domin bayan dangataka ta jini akwai tarin kama  'kak'karfa tsakanin mahaifiyar sa da Hajiya Talatu.
      Hafsat macece mai tarin ilimi, hakuri, natsuwa da nagarta, ta kasance 'kanwa ga Hajiya Talatu wanda su biyu kacal iyayen su suka haifa kafin su bar dunia, sun kuma koma ga mahaliccin su sanadiyyar ambaliyar ruwa da ya afka da su a wasu shekaru can baya wanda a lokacin Hafsat da yayar ta sunje hutu wajen wani Baffan su ne wato 'kanin mahaifin su kafin dawowar su ne lamarin ya auku.

Sun yi kuka sun kuma shiga damuwa gami da tsananin alhini saboda rashin mahaifan nasu amma daga baya duk suka dangana suka fawwalawa Allah komai, haka suka cigaba da rayuwa cikin maraicin uwa da uba, sun ga kalubale da dama wajen dangin su saboda mahaifin su asali ba wadata bane dashi sosai amma akwai cikakkiyar wadatar zuci, basu gaji komai daga mahaifin nasu ba sai gona guda 'daya sai dai tana da girma ba laifi.
             Basu tashi sanin basu da cikakkiyar gata ba sai da suka rasa mahaifan nasu aka kuma rasa cikakken wanda zai kar6e su da hannu bibbiyu ya rike su ya kuma basu gata da kulawa, 'karshe karatu ma gagarar su tayi saboda rashin wanda ze biya musu kudin makarantar, haka kuma batun gonar mahaifin su ma basu samu cikakken bayani akan ta ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora