P78

126 14 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...78*

               ........Shiru Zaitoon tayi tama amsar da ta dace ta bashi, cikin ranta take ayyana" wannan wace iriyar tambaya ce? 'kauna kam ai Allah ke dasa ta cikin zu'kata, kuma shine ya sanya musu 'kaunar Mufeeda ba wai ita ta sa ba, me yasa hakan zai zam abinda har sai an nemi hujjar da za'a kare shi da shi, shin laifi ne dan sun so Mufeeda ko kuwa wani abin daban suke nufi da ita bata sani ba.

Shirun da tayi tana duban da tunani ba 'karamin 'kona ran sa yayi ba.

Ganin kamar bazata amsa shi ba ne dan bai ga alamun tana da niyya ba, hakan ya sa ya fisgo Mufeeda dake jikin ta, wata irin fuzga ne.da ko kadan babu 'digon imani ko tausayawa tattare da shi.

Mufeeda kuka ta sanya har tana kokarin shi'dewa, ai da sauri Zaitoon ta zabura ta koma kan gwiwoyin ta tana kuka ta fara ro'kon sa da ban baki.
" Dan Allah kayi min rai ka bar min 'diya ta, wallahi dana san amsar tambayar ka babu abinda zai hana ni sanar da kai amma ban sani ba, tamkar kana tambaya na ilimin gaibu ne fa.."
" In dai kina son cigaba da ganin ta araye toh amsamin tambayoyi na yanzun nan..."
Yayi mata magama da wata bu'da'd'diyar muryar da babu alamun wasa a ciki, sautin ta kadai ma na iya hargitsa lissafin matsoraci.

" Dan Allah kayi hkr, wallahi babu wata ala'ka tsakanin mu da su fa, kawai dai ha'duwar jini ya sa suke sonta amma na rantse maka babu komai...."
" Toh ina mahaifinta yake...?"
" Ya rasu! ya rasu tun ma kafin a haife ta...."
Ta sake bashi amsa jiki na mazari idanun ta akan Mufeeda dake hannun sa tana kuka.

Gefe ta karya wuyan ta tana jin babu dadi, kukan take itama cike da tausayin 'diyar ta, rikon da yayi mata kadai abin a tausaya ne, domin tamkar wani sa'an sa ko kuma wani abin cutar wa ya damko haka yayi, hala ya mance ne cewar 'yar yarinya Mufeeda ce a hannun sa ba wani daban ba.

Tasan sarai yana sane tunda ba makaho bane shi ba kuma hauka yake ba cikin hankalin sa yake komai.

Wannan wace iriyar rashin imani ne haka wai...?"

Magana akayi masa cikin wata 'yar abin magana dake ma'kale jikin kunnen sa, hakan yasa ya ajiye mata 'diyar ta da ya fizgo ya fita.

Tamkar jira take ta janyo yarinyar jikin ta ta rungume sosai suna sakin wani sabon kuka atare...Mufeeda na fadin..." Mammi..." Zaitoon na fadin Mufee na...Allah yana gani, kuma nasan zai saka mana tunda ba komai muka yi musu ba.."

          Can gida kuwa hankula duk sun tashi an rasa Zaitoon da 'diyar ta ba 'a san inda suka yi ba, 6at babu su sama ko 'kasa ba'a gansu ba.

Babu wanda hankalin sa bai tashi ba kowa kuma tunanin da zuciyar sa ta basa daban, kowa tunanin 6acewar Zaitoon 'din fassara ya bashi na daban in ka 'dauke Ammi ka'dai da sam zuciyar ta ya kasa bata takamamman dalili guda da zai sa arasa su gaba 'daya.

Kar ma ka tona zuciyar Rayyan da Anty Madeena da masu ra'ayin fassarar ya bambanta da na kowa, banda luguden gudu gami da fargaban abinda ke shirin tunkaro su da yai tsaya musu karan tsaye a 'kirji tamkar suyi bindiga haka suke ji cikin zuciyar su... _wannan shine ta leko ta koma._

Marwa kam kuka take sosai, bata ta6a sanin sha'kuwar su ta kai har hakan ba sai yanzun da aka rasa su.

Gida yayi zugum gaba 'daya,  hatta Raihana da sauran 'yan uwa tuni labari ya iske su, domin da yawan su sun san Zaitoon musamman lokacin rashin lafitar Rayyan da suka zo dubiya a wannan lkcn da yawan su suka santa...yanzu kuwa da akace babu ita babu wanda bai jimanta ba illa 'kalilan da suka kasance mahassada daga cikin su.

Wani bin Ammi har na mamakin yadda damuwar Anty Madeena ya kasa 6oye kansa, bata san dalili ba amma yanayin damuwar ta ta sosai ya sa Ammi dasa ayar tambaya akan sa, ba zallan sha'kuwa take ganin alamun tasirantuwar sa akan fuskar Anty Madeena ba, zallan damuwa ce dake tasowa tun daga 'kasan zuciya, bata iya dannewa damuwar ta dai- dai da 'kwayar zarra ba, dan ko Marwa bata kai ta shiga tashin hankali a zahiri ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora