💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...62*
.......Bai sha wani wahalar samun abinda Rayyan din ya bu'kata ba dayake akwai a gidan su wani abokin sa, dan haka batare da 6ata lokaci ba ya nufi gidan Anty Madeena da fatan Allah yasa ba shirin sa Rayyan ke son wargazawa ba, inko hakane tabbas nesan sa zata matso kusa kwanan nan.
" Assalamu Alaikum..."
Ya furta abakin 'kofan parlon yana shafa kan magen dake rungume gefen hagun sa yana 'yar murmushin da shi ka'dai ya san ta mecece.Sallamar ya sake gami da 'dan buga 'kofan hakan yasa Anty Madeena mi'kewa taje ta bu'de.
Idanu ta runtse sosai da ganin abinda ke hannun san, kanta na fara sarawa, a hankali ta bu'de idanun tana fa'din " Sultan har ka iso...?"
Tayi maganar gami da juyawa domin bazata iya jure yanayin da take jin jikin ta ba tuni ta fara jin sanyi can cikin jikin ta.Gaba tayi Sultan ya biyo bayan ta bayan ya tura 'kofar, yayin da Rayyan ke nan kishingi'de har a lokacin bai yadda ya kalli inda Sultan din yake ba.
Sai da har ya iso gaban sa ya tsaya yana gaida shi kafin ya 'daga kai ya dube shi, cak idanun sa suka sauka akan magen sai ya 'dan bu'de idanu.
" Sultan haka ka taho da shi a hannun ka...?"
" Erh Yayah, ai babu wani abu thought yanzu zan sake komawa da shi".
" Duk da hakan ai da ka sako shi cikin wani abu taya zan ri'ke shi haka nan bacin kasan meke faruwa..."
Ya 'karasa maganar ne yana fitar da numfashi da 'kyar sbd yadda numfashin sa ke neman sarke shi...Sultan idanu ya zuba masa zuciyar sa cike da mamaki da kuma tunanin asalin dalilin da ya sanya shi sawa akawo magen bacin yasan jinin sa ba so yake ba.
Yasan dole dai akwai babban dalili da ya sa aka kawo din amma tunanin sa ya kasa bashi komai.
" Where is the ointment nd the drugs...?"
Tambayar da Rayyan yayi masa kenan da ya dawo da shi hayyacin sa, tuni ma Rayyan kam ya fara sakin atishawa akai- akai idanun sa sun koma jajaye.Sultan da sauri ya matsa kusa da shi bayan ya saki magen..'ko'karin tallabo shi yake yana fa'din" Haba Yayah, dama me yasa zaka ce akawo mage bayan kasan irin hakan ne dama zai faru...?"
Yayi maganar cike da nuna tsantsar kulawa kamar gaske.Rayyan 'ko'karin cire hannun sa yake daga jikin sa domin zafi hannun Sultan 'din ke masa tamkar wuta.." Kar ka damu Sultan, komai zai daidaita ai, yi maza kaje ka kawo min maganin ka dawo..."
" Yayah taya zan tafi in barka acikin wannan halin...ai hankali na ma bazai kwanta ba...".
Jajayen idanun sa ya sanya cikin na Sultan, nace kar ka damu ko...baka ganin jikina ne..." kalli kaga"
ya nuna masa jikin sa gaba 'daya.
" and the more u sit here d more the condition is worsening...pls kayi sauri ka dawo, Insha Allah babu abinda zai same ni..."Dole Sultan ba dan ya so ba ya mi'ke tsaye sau 'daya ya kalli magen ya kawar da kansa ya nufi 'kofa, 'ko'kari yake yaga yayi sauri kamar yadda Rayyan yace amma duk yadda 'kafafun sa ke son cika umarnin Rayyan 'din zuciyar sa taki mara masa baya, damuwar sa yasan asalin dalilin da ya sa akawo magen.
Yanda ya juya baya yake tafiyar haka Nuwaira dake sakkowa take takowa rungume da Mufeeda a hannun sa.
Wani sanyi Rayyan yayi da ganin nasara sa da ya samu na kora Sultan kafin suka fito, baya san kowa yasan wannan batu tunda bai tabbatar ba tukunna, kai koda ya tabbatar 'din ma in dai ba gaskiyar maganar ya tono ba bazai bari kowa nashi yaji ba illah Anty Madeena da aka faro da ita.Sultan na shirin bu'de 'kofa ya 'kara waigowa dan ganin Rayyan, sai dai kafin idanun sa sukai ga Rayyan kan Nuwaira suka fara sauka dake ri'ke da yarinya amma sam baiga fuskar yarinyar ba...a hankali ya 'daga 'kafar sa yayi waje yana sake jan 'kofar har da 'kara le'kowa amma still bai ga fuskar yarinyar ba ballantana ya fahimci manufar su.

YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....