💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...88*
........Ban kai ga rufe baki na ba kunnuwa na suka jiyo min abinda ya sake firgita ta 'yar natsuwar dake tare da ni, wato kukan jinjiri, wanda zuwa lokacin garin yayi tsit da alamu kowa ya nemi mafakar da zata zame masa garkuwa, banda sautin kukan babu abinda ke ratsa ilahirin dajin dama wani sashi na garin na mu gaba 'daya.
Ido na zaro sosai ina kallon ikon Allah wato ruwan dake bin inda matar ke kwance da kuma jinjirin dake kuka a 'kar'kashin ta.
Baya nayi kokarin ja amma hakan ya kasa samuwa gare ni, fizgar hannu na naso nayi da niyyar gudu amma matar nan sam bata da niyyan sake min hannu.
Ba 'karamin tsorata nayi ba, hakika wani tashin hankalin yafi gaban wani, dama haka ake haihuwa ?
Na tambayi kaina da kaina.Ko kuwa dai ita wannan 'din ce nata yazo ta wannan sigar..ma'ana daban da saura..?
Ina cikin tunani da son tantance gaskiyar lamarin da nake da da bu'katar sani, ji nayi matar nan na sakin hamdala a fili gami da saukar da ajiyar numfashi mai zafi, hakan ma ya sake bani tsoro, still tashi na sake niyyar yi amma dole na koma na zauna sakamakon hannu na da naji cikin na matar har yanzu bata sake ni ba.
Numfashi kawai take sau'kewa sai dai zuwa yanzun ya koma a hankali, banda kallon matar nan da mamaki babu abinda nake yi tunanin nawa ma tuni ya tsaya cak, idan na kalli Babyn sai na kalli matar da har yanzu ta kasa saki na.
Babu wanda ya sake yin wata magana a cikin mu illa ni da ke ta muzurai.
Tsawon mintina sama da biyar muna ahaka sannan naga matar ta fara sake yin wani nishin amma wannan karon babu abinda ya fito...salati ta fara tana kiran sunan Allah da alamu ba 'karamin ciwo take ji ba a yadda naga yanayin ta...
Mun 'dauki tsawon lokaci a hakan sai kuma na rasa takamammai abinda ya kamata na aikata.
Zuwa lokacin na gama fahimtar haihuwa matar tayi, na kuma fahimci irin ciwo da zafin dake cikin haihuwa, ashe mu ganin yara kawai muke muyi farin ciki bamu san wahalar da ake sha kafin a haife su ba, hakika dole mu jinjinawa iyayen mu, dole mu yi musu biyayya muddin ran mu, bamu da komai bamu da wani abinda zamu iya yi ko mu biya su da shi face mu yi biyayya ga duk wani abinda muka san zai sanya su farin ciki.
Na tausaya mata sosai, domin tuni na fara kuka wanda har zuwa lokacin wannan babyn na kwance inda uwar ta haifo ta babu wanda ya ta6a ta har ta yi kukan ta ta gaji tayi shiru.
Da kyar Allah ya taimake ta ta sake haifo wani Babyn wanda hakan shi ya dakatar da nishin da take yi ya kuma dakatar da zafin ciwon da take ciki ta koma sauke wani numfashin tana sakin hamdala cike da galabaita a zahiri.
Shi kam na biyun bai ko motsa ba, kwancen sa yake yadda ya fito kuma ko idanun sa basu motsa ba balle yayi kuka kamar na farkon.
Kallon ta na sake yi na kuma dubi yaran duk biyu ina jan hannu na domin zogi yake min sosai.
Sai da ta dube ni sannan ta saki hannun nawa tana murmushi, da alamu ma mantawa tayi da cewa ta rike min hannu.
" Da na sake ki da tuni kin gudu kin bar ni ko...?"
Matar ta fa'da tana duban fuska ta muryar ta na rarrabewa kuma cike da sanyi.Sam ban bi ta kan maganar tata ba sai ma idanu na da suka 'kara fitowa waje ina yarfe hannun idanu na akan yaran nace...." Sannu hajiya....".
Inda ta ri'ke 'din har sai daya koma ja saboda ba 'karamin riko tayi min ba.
" Na haifi yaran ka Doctor, sai dai ka yafe min a jeji na haife maka su..."
Abinda naji ta furta kenan madadin amsar sannun da nai mata.

CZYTASZ
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....