💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*Wattpad@
Serlmerh-md🅿️ *...26*
.......Haka tayi ta lalla6awa, shima Jibrin 'din sai ya 'dan canza kamar gaske, ya kan 'dan bata kulawa ko da bana kirki bane ya dai fi baya da yake babu kulawar gaba 'daya, ya kuma daina kawo mata gida da 'yan mata ya rage tsawon dare da yk yi ya kuma sassauta time din da yk dawowa, taba ce dai bai daina zaman sha a parloun ba amma bata kulashi, haka in ya gama zata tattare tsab ta sanyawa 'dakin turare faman da ta tayi kenan har zuwa lokacin da Allah ya sake bata wani cikin watanni bakwai bayan fitan na farko.
Wannan karon kam Hajiya Talatu sai ta tsaya tsayin daka tana kula da ita, kusan kullun sai ta zo gidan in ma bata zo ba takan kirata a waya taji ya take karshe ma data ga hankalin ta yaki kwanciya ta nemi Hafsat din ta dawo gidan ta har zuwa lkcn da zata haihu amma Jibrin bai amince ba dole ta hakura da batun domin bata da ikon tilasta shi.
Lokacin da cikin Hafsat ya 'dauko tsufa a daidai lokacin harkokin Jibrin suka sha kansa, sanadiyar za6e da ya gabato, shi kuma yana 'daya daga cikin na hannun daman wani 'dan takarar ne a wancan lkcn, sam Hafsat ta rage yawan ganin sa, sai tayi wasu kwanaki ma bata sashi a idanun ta ba, kuma bata da bakin tanka shi.Ranar wata Laraba tatashi da nakuda cikin rashin sani ta cigaba da harkokin ta na cikin gida batare da bawa abin muhimmanci ba.
Kafin fitar Jibrin a gidan ne sai abin yaso yai mata tsanani ta nemi ya kaita asbiti amma yace mata ta 'dan daure dai bari yaje wani 'dan taro ana jiran sa ne zai dawo.
Da haka yasa kai ya fice a gidan batare da damuwar komai ba balle ya damu da halin da ya barta a ciki.Sosai abin ya damu Hafsat, gashi bata da ko sisi a hannun ta, wayar ta ma rabon ta da kati har ta mance balle ta kira yayar ta Talatu ta sanar da ita halin da take ciki.
Cikin sa'a kuwa daidai lokacin da take gab da galabaita a dai- dai lokacin Hajiya Talatu tayi kiran ta kamar yadda ta saba a kullun dan jin lafiyar ta, da 'kyar ta iya amsa wayar maganar ma sai ta gagare ta yi sai nishi da take saukewa kasa kasa.
Hajiya Talatu ma da jin yanayin da ta ke hankali tashe ta fara shirin tahowa.
Cikin sa'a kafin isowar ta wata makwabciyar su ta shigo gidan dan duba ta dayake tana zaman mutunci da kowa, so kafin ma Hajiya Talatu ta iso har matar ta taimakawa Hafsat, ba daman zuwa asbiti a lokacin dan haihuwar ta riga ta taho gadangadan ne.
Tare suka taimaka mata ta haifo 'dan ta namiji kyakykyawa dashi me kama da mahaifiyar sa sak har hasken ta bai bari ba.
Ta galabaita sosai dan hk koda suka gyara ta suka ce asbiti zasu kaita a duba lafiyar su tukun na.
Suna niyyar tafiya asbitin jini ya 6allewa Hafsat cikin lokaci kankani kuma ya galabaitar da ita ta fita hayyacin ta gaba 'daya, da gudu Talatu tayi waje ko zata sama musu abin hawa at same time tana kiran wayar Jibrin amma baya 'dagawa...ta 'kira numbern mijin ta shima ya bar wayar a mota ya shiga meeting.
Da 'kyar ta samo mota ta dawo gidan da gudu-gudu sauri- sauri tana fa'din kamata mu tafi asbitin na samo abin hawa.
Duk yadda makwabciyar Hafsat taso yi mata bayani kasa fahimta tayi tace sam suje asbiti ita dai bata ji ta ydda ba, taya zata wani bata numfashi sai dai in doguwar suma tayi dan haka ita dai su je asbitin.
Abin yazo ne gaba daya cikin 'kan'kanin lokacin da duk cikin su babu wanda yy zato.
Hajiya Talatu da ta kasa yadda sai da suka dangana da asbiti kafin, acan aka tabbatar musu da cewar already ma ta rasu, dan zuwan su asbitin ma ko ciro ta cikin motar ba ayi ba aka duba aka kuma sanar da su dan haka suka juyo gida, Talatu ji take kamar tayi ta ihu tana fada musu cewar Hafsat din ta tana nan a raye bata mutu ba amma tasan ko ta fada karya take, mutuwa dole ce akan kowa kuma kowa nada nashi lokacin..a karo na biyu ta sake rasa makusanciyar ta.

ESTÁS LEYENDO
BINTEEE ( 'Yata ce)
Ficción GeneralSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....