💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)**Wattpad@*
_Serlmerh-md_🅿️ *...74*
........Zaitoon kam 'daki ta koma tana sake duban hannun ta...har a lokacin Amrah na zaune tana kallon Zee world...ko inda take bata ma kalla ba haka itama ta wucewar ta bata damu da wanzuwar ta cikin palorn ba....
Hannun ta nada saurin yin zufa hakan yasa tana shiga ta nemi abin rubutu da 'kyar ta samu 'yar takadda wacce ake zubo magani a ciki sai dai babu abin rubutu sam dan bata da shi ba amfani take da shi ba....
Hankalin ta taji ya fara tashi saboda ita kanta tana so ta san manufar rubutun da yai mata a hannun...kuma ita bata iya karatun hausa sosai ba ka'dan- ka'dan ta iya shima 'din Marwa ce ta koya mata duk da haka sai ta nutsu sosai take iya ha'dawa da 'kyar.
Bincike ta hau yi hankalin ta atashe, kamar an ce mata wani abin tashin hankali ne ya rubuta mata, tasan ba hakan bane amma haka kawai taji zuciyar ta ta 'kagu da son sanin abinda ya rubuta 'din dan tasan a halin da yake ciki dole ne ya kasance abu mai muhimmanci ne.
Da 'kyar ta ci karo da brown eyes pencil cikin drawer wanda ake zana gira da shi bata da mu ba ta koma ta zauna....Mufee na 'kananun kuka ma amma bata damu ba da yake tasan wanka take bukata ba komai ba, karo na farko kenan da taji wani abu daban ya 'dauki hankalin ta akan 'yarinyar ta akaf din rayuwar ta.
Jikin ta ta jawo Mufee ta kwantar da kanta saman 'kafa'dar ta...da 'da'd'daya 'da'd'daya ta fara 'dauko rubutun nasa tana ajiye wa saman papern nan...wasu ma har suna fara gogewa saboda yawan zufan dake hannun ta.
" K a r k i f a d i m a w a k!...."
" Subahanallah 'karshen ya goge wallahi".
Ta fa'da cikin ranta tana mai jin babu da'di.
Sam ta kasa gane menene a wurin, duk iya kokarin da tayi wajen ganowa amma ta kasa ganewa haka ta ha'kura da wanda ta samu ganewa.Tana bubbuga bayan Mufee a hankali take nazartar rubutun...da manyan harruffa ne ma zata fi saurin gane su da kyau amma 'kananun haruffa na bata wahalar ganewa gaskiya, dan bata kai ga bambance su a makaranta ba har ta bar garin nasu...wannan ma bisa taimakon Marwa ne da take 'dan nuna mata wasu abubuwan yasa har ta iya ha'dawa.
" _K...kar..kak...kar ki..fa' dima k..."_
Abin sai ya kasa bata ma'ana guda 'kwa'k'kwara.
Ta maimaita fin sau bakwai kafin ta fahimci ka'dan ahakan ma " Kar ki fa'dima ko..."Shiru tayi ta shiga nazarin rubutun sosai..sam ta kasa 'karasawa, a cewar ta sai take ganin kamar sunan mutum ne ya rubuta amma duk gidan batasan wani da sunan shi ya fara da kalmar _ko_ ba.
Har taje tayiwa Mufee wanka itama tayo nata ta fito abin na ranta kuma ta kasa fahimtar in da maganar ta dosa.
Tana shirya Mufeeda tana sake duba rubutun nata.
Ganin bata da masalaha yasa ta kawai ta 'karasa da kanta, in dai har zaice kar ta gayawa wani to ai akwai dalilin sa na fa'din hakan, dan haka kawai gara ta 'karasa da "kowa.."
Kenan kawai inja baki na inyi shiru yake nufi in dai na fahimta dai- dai.
Cikin.ranta take ta zancen zucin ita kadai...ta sa'ka wannan ta kwance wannan har dai ta gama yanke shawarar da taga shine mata dai- dai.Baki ta kya6e tana tura bakin ta gaba, a fili na furta ai na riga na fa'dawa Ammi toh kaima meyasa baka sanar da ni tunda wuri ba....."
" Toh ai kuma Ammi ce, ya ma ya isa yace har ita kar in fa'dawa ne, bayan yasan tafi kowa damuwa da rashin lafiyar tasa.
Yanke wannan hukuncin ne ya sani ta shi da rubutun nata ta wuce bayi, mitsi-mitsi tayi da shi ta kora shi a rariya.
Luf kuwa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai wani 6oyayyan farin cikin da ta san duk na taya Ammi murnar tashin 'dan ta ne...matar na matu'kar bata tausayi musamnan idan taga tana zubda hawaye akansa, haka take zama ta tayata kukan itama tana sake rungumar Mufeeda a kirjin ta da tunanin idan akace ita ce a wannan halin ni ya zanji.
YOU ARE READING
BINTEEE ( 'Yata ce)
General FictionSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....