P23

87 8 2
                                        

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...23*

          ...... _Alhaji Jibrin Adam 'Dan- maliki_ matsayin ubangidan sa kuma me 'daukan nauyin duk wasu  makaman da yake amfani da shi.

Sosai kowa yy mmk, take kotun ta 'dauki surutai da kananun maganganu da 'kyar aka samu komai ya daidaita, Adam dake zaune ta gaba- gaba kusan suman zaune yayi da jin wannan furucin, ba 'karamin shiga tashin hankali yayi ba, duk da cewa baya shiga harkar sa amma ai jini ba karya bace..kuma duk inda akaje aka dawo dole dai jini yafi ruwa kauri...baya ga haka ma burin shi fa? mutumin da yake da burin samin sa kan saka hannu cikin maganar dan ya taimaka wajen wanke laifin Zaitun sai kuma yaji sunan sa...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..kawai yk iya maimaitawa.

Karshe dole aka 'dage shari'ar har sai zuwa nan da wasu kwanaki kimanin goma sha hudu, domin sake kaurara bincike game da sabon furucin na Dr Rasheed.

Hankulan jama'ah duk ya dauku ga sunan da Rasheed ya ambata, kasancewar sa wani kusa ne a gwabnati bayyananne kuma sananne ga mafiya yawan al'ummar jahar, kuma da yawa ba'a yi masa kallon gur6attace shiyasa akai matukar mamaki.

Tuni an mance da zancen su Zaitun an koma kan 'Dan- maliki, dama haka jama'ah suke, abu 'kalilan ke 'daukan hankulan su ga abu haka kuma wani 'kalilan 'din ke sake juyar da hankalin su zuwa wani waje.

Wannan karan wata ma'ajiya aka maida su a Prison dake babbar karamar hukumar jahar tasu...wuri mafi tsamani da muni ga jikkunan su kuma illa ga numfashi da lafiyar su.

Irin kukan da Zaitun tayi ranar baya ta6a misaltuwa, tayi kuka kuka me tsamanin gaske, ganin kwanakin shan wahalar tasu a kullun da'da yin gaba yake yi bbu kuma alamun sassautawa balle suyi tunanin 'dan lokaci ne.
Kullun sassauci baya zuwan musu sai dai tsanani...
Haka kawai in tana zaune sai kaji tana fa'din" Allah! Yah Allah!!, Yah Malikal mulk Yah Zuljalal wal ikhram...tsabar yadda damuwar ta takai ma'kura sai ta rasa mai ma zata furta ne, me zata roki ubangiji yayi mata a wannan halin, kawai sai ta saki kuka me karya zuciya mai azabtar da ruhi da gangar jiki, ita ka'dai tasan halin da zuciyar ta take ciki...wai ita ce yau a prison, itace tayi zaman cell tsawon kwanaki itace akai ta jiba bisa tuhuma akan laifin da ko cikin mafarki bata fatan ta tsinci kanta a ciki balle a zahori, itace yau dubban al'umma ke mata kallon mai laifi, itace ake shari'ah da ita a kotu da bata tunanin ya wanzu a doran 'kasa ba, itace itace abin da yawa fa...hakan kadai idan ta tuna yakan yi mata zafi matuka, zafi ma me kona zucia....

Abu biyu ke mata kai kawo, bata san inda Mufeeda take ba bata kuma san wa zata tambaya game da yarinyar ba, dan rashin ganin Mufeeda shine ya sake ta'azzara yanayin da take ciki.

Kamar almara kamar a mafarki abubuwan ke ta faruwa mata daki- daki duk cikin kankanin lokaci.
Cikin kalilan 'din watanni ta tsinci kanta a waurare da kuma yanayi daban- daban wa'danda ko cikin tarihi bata ta6a jin su ba iya tsawon shekarun ta na dunia, bata ta6a tunanin faruwar haka ga rayuwar ta ba, shekara 'daya tak baya in ance mata zata fuskanci wadannan abubuwa bugan kirji zata yi ta karya ta amma abin mamaki sai ga shi karshen ta ma yau ga inda kaddara ta jefo da ita.
Ta kuma rasa shin waye me laifin, iyayen ta ne ko kuma ita? ko kuma Mufeeda.
Shin Iyayen ta da suka kasa rike ta sbd kaddarar data same ta ne ke da laifin ko kuma ita da ta kar6i kaddarar tata ta rungume hannu biyu..?"
    
Haka suka cigaba da kwana cikin prison 'din, basu da banbanci da dabbobi, domin kowa baya musu kallon arziki, kowa kallon su yake kamar ba 'yan Adam da Allah da kansa ya karrama su ba.

       Kafin cikar kwanaki Sha hudun nan Zaitun sun koma sai 'kashi idan ka dube su, banda katon kai babu komai, duhu sosai suka yi suka jeme, ba ma kamar Hameeda da ake 'dan 'kara gyara jikin da lafiyayyan mayuka da supplements tsadaddu, yanzu da ya kasance babu shi komawa tayi kamar wata Hameeda ta daban.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now