💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*Wattpad@
Serlmerh-md🅿️ *...36*
.......Bayan da aka gama komai, zaman makoki ya kare kafin Adam ya 'dan sake, domin ranar da akai addua'n bakwai an yi nasiha sosai musamman ga Adam kan tawakkali da imani da kaddara.
Ya kuma fahimta ya rike ta hannu bibbiyu, yasan cewa kowa lokaci daman yake jira, mutuwan nan dole ce.
Abu guda dake sanyaya masa zuciya ma shine rabuwa lafiya da suka yi da mahaifin nasa, domin har ya koma ga Allah yana sakawa rayuwar sa albarka da fatan dacewa.Wannan kadai idan ya tuna yakan kara masa karfin gwiwar cigaba da walwalar sa kamar baya, addu'a ce dai bazai fasa yi masa ba har 'karshen nasa numfashin, duk da bai da tabbacin yana da tsawon rayuwa shima.
Washe garin da akayi bakwai ya shirya shi da Hajiya Talatu da Hafeez da a cewar sa shima baza'a barshi a baya ba da shi za'a yi wannan tafiyar, haka suka yiwa Jahar Yobe dirar mikiya, ba'a kwan da su ba aka tashi dasu, ba'a san da zuwan su ba sai ga su, ba'a san da wanzuwar su ba ma a duniyar suka bayyana gare su kamar shigar mashi.
Farko gidan sarkin garin suka nufa da da bincike da komai aka gano dangin mahaifin nasa da ba laifi suna da yawa ga kuma karamci irin na dattawa.
Anan suka samu lbr ashe 'Dan Maliki tun yana yaro ya gudu ya bar garin, karatun almajiranci aka sanya shi sai kuma ya kasance malamin na da saurin hannu ga zafin duka kusan duk dukan da zai musu in dai da dorina ce toh sai ya fasa mk jiki.
Abin yana kona rana 'dan Maliki gashi kullun duk dole ne musamman idan baka kawo hadda daidai.
Da wani dare bayan sun tashi karatun dare 'Dan Maliki yasha dorina har sai da ta masa shati biyu ya damtsen hannun sa, 'daya ya fashe hadda jini 'daya kuwa bai fashe ba duk akan aya 'dayan karshe suratul Taghabun da bai kawo ba.
A zuciye ya bi bayan malam har turakar sa ya kwada masa dutsi aka ya gudu abinsa ya bar garin ya bar malam cikin azaba da tsiyayar jini har sai da akai masa dinki aka.
Cike da azaba yana dafe goshin sa yake fadin" Kai Jibrila ramuwa kazo kayi, ni ban isa in hukunta ka ba kenan, 'dan iskan yaro shaidanin banza, insha Allahu sai ka gani ai, sai ka bi dunia ka lalace...".
Sosai wannan lamari ya sosa ran Malami har ya yiwa 'Dan Malaki mugun baki kasantuwar sa mai kanbun baka sai kuwa bakin sa ya kama 'Dan Maliki.
Duk da duk da wani mai imani yasan cewa komai sai da nufin Allah, amma mun kuma san cewa littafi ko hdithi bai 'karya ta Kambun baka ba, ha'ki'ka Kambun baka gaskiya ne.Koda aka nuna wa Adam Malamin murmushi kawai yayi suka gaisa a mutun ce dan Malamin ya tsufa jigif amma still tabon na nan a goshin sa bai 6ace ba.
Tun kuma fitar 'Dan Maliki wancan lokacin bai sake dawowa ba har sai da ya 'dauki shekaru masu yawa sannan ya waiwayo gida, a lokacin tuni mahaifin sa ya rasu saura mahaifiyar sa da kishiyoyin ta, su uku ta haifa 'daya ta rasu 'dayar kuma tayi aure cikin fulanin tashi sun kuwa tashi da ita har yau ba ita babu labarin ta, sai shi ka'dai, hakan yasa ya 'dauke mahaifiyar sa ya tafi da ita.
Tunda kuwa da ya 'dauke ta bai sake waiwayen kauyen ba har ya koma ga mahaliccin sa.
Duk yadda zan misalta muku yanayin tarin farin cikin da Adam ya tsinci zuciyar sa a ciki bazaku fahimta ku misalta da kanku.Abu ne da ya jima yana muradi sai a yanzun Allah ya nufe shi da shi.
*****
Tun shigowar Rayyan gidan ta fahimci a yanayin da yake amma ta basar, tana kitchen taje daukan ruwan sha ta hangi.bayan sa ya shigo sai da ya zauna a parlour ya'dan huta kafin ya tashi ya 'karasa bedroom 'din sa.Baki ta kya6e sam bata jin yau zata iya yi masa komai da yake da bukata, gaba 'daya ma jinta take tamkar wata marar lafiya tsabar wahalan da Sultan ya gana mata ayau din.
Tarasa mecece matsalar sa da Rayyan a rayuwa, abinda ya mata yau din ta fahimci kamar duk huce takaicin sa yake yi akanta da bashi da wata hanyar sai ita, ba yau tasan halin sa ba, duk lokacin da ransa ya 6aci da Rayyan akan ta yake sauke duk fushin sa sai ya tabbatar ta jikkatu kafin yake barin ta.

VOUS LISEZ
BINTEEE ( 'Yata ce)
Fiction généraleSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....