💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)**Salmerh MD*
🅿️ *...13*
Wani 'daki aka kai ta babu komai a dakin sai katifa da walldraw din bango sai wata kofa data ke kyautata zaton bayi ne kamar na asbitin da ta baro da safiyar yau din.
Suna shiga Na'eema ta wuce ciki murafen waldraw din ta bude gaba daya ta wangale a gaban Zaitun tace" ga Ghanar ki anan ga kuma can bayi.."
Tayi maganar da nuna kofan bayin sannan ta cigaba..." Ko ba'a fada miki ba ai kinsan jikin ki na bukatan ruwa ko..? Zan je in dawo yanzun nan..".
Daga haka tayi waje abinta.Daga nan sakon Hajjaju ta mika na kiran Muhibba sannan ta dawo wajen Hajjajun tana me dan 6ata rai.
Hajjaju da tasan kwanan zancen sai murmushi kawai take yi tana duban fuskar Na'eeman..." Wlh Hajjaju wannan tayi local da yawa...baki na har tara yawu fa yake idan na je kusa da ita..."
" Na'eema kenan...bazaku gane bane, wannan da kike gani ba karamar kadara bace bari ta wanku zaki sha mamaki...".
'Karamar tsaki Na'eeman ta saki kawai ta kawar da kai gefe.
'Bangaren Zaitun kuwa wanka tayi ta kuma yiwa Mufee wanda cikin sa'a da bude pampo ga mamakin ta ruwan dumi taji yake zubowa hakan ba 'karamin farin ciki ya sanya ta ba, take tai wanka ta kuma yiwa Mufee ta wanke musu kawunan su duk, dan dama sosai ya ishe ta hakuri kawai take da dauriya saboda rashin sukuni kuma babu yadda zata yi.
Ko da ta fito wankan jakan kayan sun kaf ta zazzage bisa wannan katifar, rigan Mufee guda 'daya tak ta rage mara datti sai kuma pant dinta guda biyu amma sauran kayan duk masu datti ne ita kan ma bata ga na sawa cikin nata kayan ba dole suna bukatan wanki.Man shafan su ta ciro suka shafa wanda tun ranar da ta bar gidan Hajiya Talatu jikin su bai sake ganin mai ba sai yau...shiyasa suka kokkode.
Sai da ta gama shirya Mufeedan sannan ta tattari kayan su masu dattin ta shiga bayin dakin da yake tana da ragowar sabulun ta da omo da ta taho da shi daga gidan Hajiya da su tayi amfani ta wanke musu kayan su kaf wanda tana cikin wankin ne Na'eema ta dawo ganin hakan yasa tace.." aww dauraya kike toh in kin kammala akwai igiya ta bayan kitchen, ta cikin Kitchen din zaki fita.."
" ai ban san kitchen din ba..."
" Ina Parlour idan kin gama.."
Cewar Na'eeman kenan ta sake ficewa.
Zaitun sai ta rasa wannan su wasu irin mutane ne da basa bawa mutun abinci..tunanin yarinyar ta take damma tayi bacci yanzun amma ai inta tashi dole bukaci cin abinci.Koda ta kammala wankin bata je wajen shanyan ba zama tayi wajen Mufee cike da lalla6i ta bi ta kitse mata gashin kanta, ba wani iya kitson tayi ba amma da yake gashin yarinyar mai kyau ne kuma ya hadu da hasken fatar ta sai kitson ya dan fito yarr ya kuma yi mata kyau...murmushi tayi cikin ranta tace _" Ya dai fi babu.."_ .
Sai lokacin ta dauko bucket din da ta tara kayan shanyar ta fito...Na'eeman ce ta nuna mata hanyar kitchen ta bi ta kofar baya ta shanya kayan tas.
*****
Wasa wasa yau ga Zaitun tana cikin kwanaki na sha uku a gidan Hajjaju...tuni sunyi fes da su daga ita har Mufeeda dan basu da matsalar komai.
Na'eema kuwa bakomai yass aka hada ta da Zaitunan ba illa ganin shige da ficen ta, yanayin rayuwar ta da yarinyar ta, gefe guda kuma kula da tsabta da cimar su...jikin su duk yayi kyau yanzu bazama kace Zaitunan nan bace ta wajen Mabarata.Abu guda da ta lura da shi kuma yake yawan faruwa a gidan shine yawan shige da fitar maza, wanda lokuta da dama idan sunzo din sukan fita da wata daga cikin 'yan matan Hajjajun ne wadanda suka tasamma goma sha 'daya.
Itama ba rana guda ta fahimci hakan ba sai a hankali, kuma ta fahimci Hajjajun ba ita ce ta haifi 'yan matan nan ba kawai ita ta kasance ne tamkar shugabar su.
Ita dai har yau din bata samu matsala da kowa daga cikin su ba har gara ma Shaheeda itace sam ta tsani ganin su bata kuma san dalili ba.
Bata da lokacin saka damuwar kowa aranta a yanzu dan haka itama banza ta bawa ajiyar ta..damuwar ta yanzu daya ce tuno gida da take yawan yi tana kewar su sosai tana kuma san ganin ahalin ta..abu guda dake taka mata birki shine kasancewar Mufeeda tare da ita.
Gefe guda kuma ga Adam..bawan Allah mai kyakkyawar zuciya, bata san ya zai ji idan yazo ya tarar Hajiyar sa ta kore su ba..irin yadda ya nuna yana tausayin su tsawon zaman su da shi ya sanya a kullun sai ta tuna da shi...gefe guda kuma Mmn Abdul...kullun fatan alkhairi take binta da shi ita da zuri'ar ta._Bayan kwanaki ashirin da biyar._
Yanayin yadda rayuwar gidan ke guda na sai yazo ya fara bawa Zaitun tsoro dan zuwa yanzun ta gama fahimtar su wanene Hajjaju da kuma manufar ajiye ta tare da su.Sosai abin ya razana ta dan haka sai ta fara tunanin yadda zata yi ta rabu da su tun kafin wankin hula ya kaita ga dare...ita ba kalan rayuwar da take da burin aikatawa ba kenan...ba shine a gaban ta ba.
Tana cikin tunanin mafita kwatsam da wani dare sai ga 'yan fashi sun shigo musu gidan aka tattaro su gaba daya zuwa babban parlourn gidan inda 'aka ritsa Hajjaju da bindiga saitin kanta...daren ba wai ya raba bane dan dududu bai wuce karfe sha 'daya bane. na dare, kuma a yanayin da 6arayin suka zo sun zo musu da sigar bakin da ke zuwa musu, har Hajiya na murnar tayi manyan bakin kwana bisa ga yadda taga shigar su babu karanta a ciki sai kuma akayi rashin dace ashe sa6anin tunanin Hajiyan ne.Ita kanta Zaitun da ace bata ga bindiga ganin idanun ta ba da bazata ta6a yadda cewa 'yan fashi bane, sai dai tace abokan huldar su Hajjajun ne kawai suka zo, amma ganin bindiga ya sa jikin ta tsuma ta rungume Mufeeda sosai idanun ta kuwa ko bude su bata sake iyawa ba saboda tsoro.
Bata san me ya faru ba kuma, ta dai farka ta ganta kwance a dakin ta na gidan ga Mufeeda rungume da jikin ta kadan..suna baccin su.
Saurin mikewa tayi zaune tuno abinda ya faru sai dai kuma bata ga alamun 6arayin nan a gidan ba hakan ya sa ta gyarawa Mufee kwanciya ta tashi, hutun sallah takeyi shiyasa koda ta shiga bayi ta fito bata nemi abin sallah ba kawai tayi waje.
Can babban Parlour ta hango su Hajjaju zaune sun yi jigum- jigum.
Nan take jin labarin yadda abin ya kasance daga abikin su, anan ne ma ta fahimci cewar ita din doguwar suma tayi.
Gwala- gwalan Hajjaju duk suka kar6e inda suka kuma bawa Hajjajun sati biyu kacal ta nemi wurin shiga ta bar musu unguwar su in bahaka 'kone gidan za suyi gaba daya kowa ma ya huta.Babu wanda bai shiga tashin hankali bisa ga bayanan 'yan fashin ba gashi duk sun rasa dalilin wannan lamari.
Dole bayan kwana biyu da abin ya dan bar jikin su Hajjaju ta fara tunanin mafita yadda zatayi da 'yan matan ta...a fizge Zaitun take jin sabon tsarin da Hajjajun ta yanke musu dole sai ta rarraba su ga kawayen ta magajiyoyi irin ta kafin tayi settling sabon waje ko garin da zai fi dacewa da su.
Bayan shu'dewan kwanaki biyu Hajjaju na ta hada- hadan rarraba 'yan matan ta, duk kuma abinda suke yi basu saka Zaitun cikin sabgar su dan a har lokacin bata gama sakan jiki da su ba amma Hajjaju ba karamin tattalin ta take ba, duk wani abu na jin dadin rayuwa takan wadata Zaitun da shi saboda ta kwantar mata da hankali hadda Mufee take hadawa.
Ranar wata Juma'a ne Zaitun na a 'daki ita da Mufee tana yanke mata farcen ta sai da ta gama na Mufee kafin ta fara yanke nata ma.
Sanye take da wata doguwar rigar abaya peach colour wanda Hajiyar ta sai mata sai mayafin rigar data yafa a kanta, yayin da Mufee ke sanye da wata riga irin ta yara armless iya gwiwan ta sai takalmin ta baki mai igiya har baya.
Cak ta tashi da irin tafiyar ta da har yanzun bai gama warwarewa ba ta dauko goran ruwa da yake emty tana jijjigawa..." Mam..mi..u..wa..".
Ta fadi hakan tana tahowa wajen Zaitun...Zaitun bata sha wahalar fahimtar abinda yarinyar ke bukata ba dan haka take ta mike ta 'dauke ta suka nufi hanyar kitchen dan nema ruwan da take bukata.
Kadan ya rage su karasa babban Parlour kunnuwan ta suka jiyo mata abinda ya 'dugunzuma hankalin ta baki daya.
Muryar Shaheeda ta tsinkaya cike da tsiwa mai tafe da rainin hankali tana fadin..." Kai Hajjaju Zaitunar...amma dai sai an.......Salmerh😘

VOCÊ ESTÁ LENDO
BINTEEE ( 'Yata ce)
Ficção GeralSome people succeed because they ar destined to, but most people succeed because they ar determined to....