P27

82 8 3
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
*Serlmerh-md*

🅿️ *...27*

           ......Haushin fatali da 6arnatar masa dukiya da akai batare da wata 'kwak'kwarar dalili ba ya sashi yanke shawarar zuwa ga 'Dan Maliki suyi magana ta fuska da fuska, yana so ya fito masa a mutun ya nuna masa gaskiyar cewa ya gaji ya kuma kai 'karshen bango, yana so a sarara masa haka nan, kuma inda hali baya so ya 'kara shiga sabgar rayuwar sa, shike da ikon za6arwa kansa duk irin  sana'ar da yake so ya kuma ga ta kwanta masa dan haka ya 'kyale shi, ko kwasar kwata zai yi babu ruwan kowa da shi.
Sun tattauna da Hafeez kan hakan lokacin da yazo yi masa jajen lamarin ya kuma so dakatar da Adam 'din kan cewa da yayi zai sami 'Dan Malikin tunda a zahiri babu wata alama da ta bayyana da sa hannun sa ciki.
Amma Adam sam ya ki amincewa da batun Hafeez domin acewar sa shi ya san waye 'Dan Malikin da duk shirin sa, dan haka in zai raka shi toh bismillah in kuwa baza shi ba ma duk ba matsala bace agare shi zai iya zuwa shi ka'dai.

Da wannan tunanin ya ringa kwana yana tashi har zuwa ranar da ya samu lkcn zuwa ga 'Dan Maliki domin ganawar bisa tursasawar sa ga Hafeez dole sai da ya raka shi.

Unfortunately sai basu je kan sa'a ba sakamakon katari da mugun gani da suka yi shi har Hafeez 'din babu wanda bai tsinci kansa cikin tashin hankali ba.

Duk wa'danda ke aiki tare da mahaifin nasa zuwa lokacin sun riga da sun san kakkarfar alaka da ke tsakanin sa da Adam dan haka koda ya nemi ganin sa bai samu wata matsala ba, sai dai cikin rashin sa'a sun same shi ne tare da wasu watsatstsun 'yan mata, ba sai an fa'da masa ba domin a yanayin da ya gansu amsar shi ta riga ta bayyana a fili karara, ya kuma san already matar da yake aure tana can Abuja da zama kuma ita babbar macece ba kamar 'yan matan da ya gani tare da shi ba, wa'danda yana da tabbaci ba dan ku'di da suke samu daga 'Dan Malikin ba da bb abinda zai sa su saurare shi ma sbd shekaru da suka bayyana  gareshi 'karara.

Fa'din halin da Adam ya tsinci zuciyar sa a wannan ranar ma 6ata lkc ne, abin ya matukar ka'da shi, sosai yayi masa ciwo a zuci, yayi ba'kin ciki irin wanda ya jima bai yi irin sa ba, haka ya fito batare da ya tsaya bi takan hatta Hafeez ba ma balle ya jira su yi maganar da ta kaishi da Alhajin, tafiyar ma yin ta kawai yk amma dishi dishi yk gani, baya so ya 'kara koda minti guda cikin gidan baya ga haka da babu abinda zai hana shi samawa kansa hutu, sai dai yafi bukatar barin gidan akan hutun da yake ji kamar yana da bukata saboda tsananin yadda bugun zuciyar ya karu yake kuma masa barazanar 'dauke masa numfashi.

Yana jin yadda 'Dan Malikin ke kwala kiran sunan sa da nufin dakatar da shi amma bai ko waigo ba bai ma nuna alamun yaji kiran ba, kuma baya da niyyan tsayawa kamar yadda bashi da burin sake ganin fuskar 'Dan Malikin gaban idanun sa.

Kallo 'daya zakai masa ka tabbatar ba cikin hayyacin sa yake ba, tafiya kawai yake bama ya sanin ina yk jefa kafar sa balle yasan inda ya dosa, haka kawai sai yaga kamar harabar gidan ya 'kara fa'di da tsayi ne, duk 'ko'karin da yake wajen ganin ya fitar da kansa cikin gidan amma abin ya faskara, bai ta6a fahimtar girman da gidan ke dashi ba sai a wannan lokaci.
Gaba 'daya fuskar sa da idanun sa sun koma jajaye, jijiyoyin kansa da gashin jikin sa sun mimmike, banda wani dun'kulallen abu da ya tokare masa kirji yai masa nauyi sosai...cikin ransa yk ji tamkar ba zai yi tsawon rayuwa ba aduniyan nan, kuma shi akaran kansa ma yafi son hakan da ya cigaba da rayuwa yana cin karo da irin wagga lamari daga mahaifin sa gara ace bashi ma a duniyar yafi a ganin sa kenan.
" Har sai yaushe? sai yaushe ne zai canza? Duk da wannan shekarun amma har yanzu bb abinda ya canza game da shi? Sai yaushe zai samu cikakken farin ciki daga mahaifin nasa? sai yaushe zai fuskanci rayuwa ya san cewa annabi ya kafu, sai yaushe tsoron Allah zai dasu masa a zuciya? sai da wani lokaci zai san cewa shi 'din yanzu ba yaro bane shekarun sa sun ja sosai, sai yaushe ne shi kansa zai samu cikakkiyar adalci daga mahaifin nasa? tun yana cikin mahaifiyar sa bai samu kula da adalci daga gareshi yadda ya kamata ba sai yaushe ne zai samu hakan wai? Yaushe wannan mutumin zai bari ta6on da ya dade cikin zuciyar sa ya warke gaba 'daya?"

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now