P16

76 10 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...16*

   
      _Shiiit_ ...shine abin da ya bayyana daga sautin muryar sa at same time yana me bugan sitiyarin motar da hannun sa 'daya...da alamu bai so tsayawan ba...amma kunnen sa sun jiye masa kukan yarinya 'karama.

Baya ya dawo da motar ya bu'de ya fito, sai a sannan ma yaji ashe ba yarinya kadai ke kuka ba har da wata mace sakamakon jiyo sauti bibbiyu da yayi.
Da hanzari ya nufi inda suke domin yana iya hangosu daga inda yake tsayen, dai dai lokacin ne kuma wadannan matasan suka tarwatse kowa yayi hanyar sa, bai bi ta kansu ba hankalin sa na ga mata da yarinyar da ya gani durkushe a wurin ne yake kuma jiyo kukan su, lokaci 'daya 'kwa'kwalwar sa ta basa abinda ke shirin faruwa a wurin duba ya yadda yaga duk sun hargitse riga a rabe, wanda ga dukkan alamu kiris ya rage mai afkuwa ta afku in ba dan ikon Allah da ya kawo su ba.

Baya baya ta fara ja tana me sake sakin kuka sbd a halin nan da take ciki bata iya banbance mugu da wanda yake sa6anin haka.
"....Dan Allah!... dan Allah..."
Take ta fadi batare da ta iya karasa abinda take da niyyan furtawa ba.

Ganin kamar shima tsoron sa take yasa shi daka mata tsawa" _Nutsu da Allah..._ "!
'Dif Zaitun ta shanye kukan ta tare da rintse idanu da karfin gaske.

Batare da yasan wace ba ya jefa mata tambaya yana me kokarin kare ma fuskar ta kallo"..Me kk yi waje da wannan uban daren..?"
Shiru ba amsa illa baya da ta kara saurin matsawa sakamakon tsawar da ya sake mata, gaba 'daya ta firgice.
Jin ta iso kusa da Mufee yasa tai saurin rarumo ta ta gurme ta tamkar zata maida ta cikin ta...

Ido ya tsura mata cike da mamaki wanda sai alokacin ma ya fahimci wace ita gami da tunano inda ya santa, in bai manta ba ya ga wannan fuskar tare da wannan 'yar yarinyar a mabanbantan wurare har sau biyu.
...Ido ya 'dan zaro cike da mamaki yana nuna ta yatsa"...You!..what ar u doing here?..ina zaki je da wannan lokacin?"

Zaitun dai ba fahimtar sa take ba dan har a lkcn bata dawo hayyacin ta ba, d fact that za'a raba ta da Feefy da kuma fyaden da aka so yi mata shine ka'dai ya tsaye mata.
Hijab 'din ta dake yashe gefen kafarcsa ya dauka ya jefe mata.." sa mayafin ki..".
Ya fa'da da murya mai 'dan sanyi..hakan ne ya sa ta lalu6i abinda taji ya jefa matan ta suturta jikin ta da shi, ita kanta tafi son hakan duk da yake tana cikin yanayi na rudu amma data suturta jikin nata sai ta dan ji dama..kuma har a wannan lokacin bata bude ido ba balle ta ga wanda ke mata maganar.
Fatan ta kawai shine taji yayi tafiyar sa shima batare da ya cutar da ita ko Mufeeda ba.

Muryar da take ji nayi mata maganr yai mata kama da wata murya da ta ta6a ji sai dai a a wannan halin bata da nutsuwar iya tuna inda ta san muryar bazata iya tunawa ba.

Kokari tayi ta 'dan bude ido kadan jin shiru na wasu sakanni ne ce komai ba kuma bata ji alamun ya tafi ba, hakan yasa ta 'dan 'dago dan duban fuskar sa cikin rashin sa'a idanun ta suka sauka akan hannun sa na dama dake ri'ke da 'karamar bindiga.." Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un abinda Zaitun ta furta kenan cike da kidima gami da sake rintse idanu ta kame jikin ta kamkam Mufee kanta dake rungume da ita sai da ta saki dan kara bayan tuni ta bar kukan tana sakin ajiyan zuciya.
Komai sai ya tsaya mata cak.
Sauran mutane uku da ke zaune cikin motar ne sukai saurin fitowa, dama duk hnkulan su na gareshi gudun kar wani abu ya sami shugaban nasu.
Yana jin fitowar su, kuma yasan da fitowar tasu me zasu yi next bindigogi zasu ciro dan attacking koma miye, sanin hakan da yayi ya  sanya shi saurin 'daga musu hannu dan dakatar da su ba tare da ya bari ta gani ba, amma ina ba mamaki mantuwa yayi da cewar shima akwai a hannun sa.

Ita kam hankalin ta duk ya bar jikin ta banda 'kyarma babu abinda jikin ta keyi, tunanin ta kaf ya tafi ne ga tunano amfanin bindiga...abu biyu kacal ke dawo mata...ranar da aka harbe Nadia, da kuma daren da 'yan fashi suka shigo gidan Hajjaju wannan ma ta gansu da bindigogi a hannayen su.
Kafin ya sake yun'kurin yi mata wata tambayar tuni Zaitun ta sume a zaune.
Tsaye yaran san suke cirko cirko yayin da shi kuma ya durkushe gaban Zaitun yana sake kare mata kallo dan tabbatarwa idanun sa cewa ita din ce dai ba wata ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now