Gudu take tamkar ranta zai fita, burinta bai wuce taje gida ta hana faruwar abinda ke shirin faruwa ba, domin ta san abu ne da zai iya tarwatsa rayuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba, sai dai kuma tana ƙarasawa tayi turus taja burki a ƙofar gidansu ganin an fito da makara wanda ko shakka babu ta san gawar mutum mafi soyuwa a cikin ranta ne. A ƙasa ta zube tana gunjin kuka tare da damƙo ƙasar dake ƙasan duk da dattin dake gurin bai hanata ɗebo ƙasar ta kalla ba.
"Zeenat...!" Taji muryar ƙaninta dake bi mata, ta ɗago jajayen idanunta tana kallon sa "Ka bar nan Usama, domin na tabbatar ni ɗin a yanzu bani da maraba da gawa."A fusace ta miƙe tamkar mahaukaciya, fuskarta gaba ɗaya a wanke take da jini, jikin ɗaga murya ta ce "Meyasa ba zaka kashe ni ba, ni ce nayi maka laifi amma kuma dangina kake yiwa ɗauki ɗai-ɗai bayan ƙawayena da muka aikata maka laifin ka kashe su meyasa ba zaka haƙura ba? In kuma fansa kake so, ka kashe ni mana, amma ka daina kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba"
"Ke abar ƙaunata ce, ko kin manta yanda kika riƙa nuna min soyayya, har kuka kika saka nayi a kanki, shiyasa ba zan kasheki ba, amma ki sani zan ta kashe kowa naki har sai da kanki kin ji kin tsani duniya, har sai da kanki kin kashe kanki saboda tsanar kanki, bana so mutuwarki ta rataya a kaina so nake ki kashe kanki dan ki dawwama a baƙin ciki duniya da lahira...!"*_Zai zo muku nan ba da daɗewa ba._*
_Alƙalamin Sadiya S Adam_
_SaNaz deeyah_
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Ficción históricaƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...