*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART ONE'''
*PAGE 1️⃣*
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''GIDAN ALHAJI SALEH.
SYED: Ai Abbah ya matsa akan Auren nan Cewar Syed.
NASIR: To ai gwara ya matsa din Ya Syed kasani fa saika samu kayine tukuna nima zansamu na Motsa.
Kuma kunrigada kunfuskanci juna da ita to jiran me za'ayi?
Syed ne ya sami waje ya zauna kan kujerar dakinsa sannan yace
SYED: Tabbas Munfahimci juna Nasir.
Kuma Tabbas ina kaunar Farhan sosai, Amman ina bukatar lokaci yanzu bayan dawowa ta domin kara fahimtar inda ta dosa.
NASIR: Hakane To Ai hakanma lissafi ne mai kyau ni yanzu zan sauka kasa kasamu kayi wanka muna jiranka muci abinchi.
SYED: Ok! Nasir I'll Be right there Syed ya fada.
Syed ne ya kulle dakinsa inda yaketa tinaninnika kafin daukan wayarsa da danna kiran Babban Abokinsa Mahmoud
Ringing takeyi, Dagawa Mahmoud Din yayi dacewa
MAHMOUD: "Tin dazu nake kiranka sai yanzu zaka kirani?"
SYED: Kaga kayi hakuri mana Kaima kasan a halin da nake ai yanzu shigowa na fa gida kenan.
MAHMOUD: "Nagane yanzu yaya ka sauka lafiya?"
SYED: Lafia lau Alhamdulillah kana ina haka?
MAHMOUD: "Ina Office wallahi naje Alhaji ya turani wani Cike cike ne"
SYED: Oh Understood! Yanzu abinda za'ayi inaso karakani ne zanga Farhan?
MAHMOUD: "amman daga dawowarka ko hutawa bakayi ba?"
SYED: Kawai inaso naganta ne nayi mata alqawarin ina dawowa zanje na ganta.
MAHMOUD: "Ok Toh ai na kusa kammalawa abinda za'ayi zanzo nan gidannaku saimuje ko?"
SYED: Shikenan babu damuwa, Kafin Syed ya kashe wayar Mahmoud wata kirance take shigo masa.
An rubuta RAY.
SYED: Dagawa Syed yayi Yace Raheelah ya kike?
RAY: "Na'am Syed ya gida ka sauka kuwa?"
SYED: Ehh kinganni yanzu na shigo gida How's Mom?
RAY: "She's fine Syed"
SYED: Good My regard Please.
RAY: "Zataji Syed, dama kacemin yau zaka sauka shine nace barina kiraka naji ka sauka lafia?
SYED: Allah sarki Raheelah na sauka lafia lau kuma ina lafia lau.
RAY: "That's good Yanzu kahuta Take Care ok?"
SYED: Yeah Thanks Ray I'll call you later cewar Syed.
Syed kashewa wayar yayi shiga wankansa.
GIDAN ALHAJI SAMINU BABA.
Alhaji Saminu Baba Babban Aboki ne ga Alhaji Saleh Ansari tare suke kasuwancin su.
Alhaji Saminu Baba Shine Mahaifin Farhan Da kuma yayanta MOHAMMAD Anace Masa MOH. Alhaji Saminu da Alhaji Saleh jira sukeyi Syed ya dawo daga karatu kawai don ayi masa baiko da kuma aure tareda Farhan.
Farhan tana matukar son Syed haka shima yana matukar kaunarta.
Shikuwa Babban Da wajen Alhaji Saminu Moh, Bayajin Magana kokadan Yakan shiga rigingimu kala kala sannan domin jin kansa yakan barnatar da kudi sosai.
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Aktuelle LiteraturLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.