AHALI GUDA PART 2 PAGE 5

2 0 0
                                    

*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 2'''

✨ *PAGE 5* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

'''GIDAN CHAIRMAN FAYZ.

Najma ce zaune ita kadai kusan Karfe Sha daya na dare Fayz baidawo ba.

Sallama yayi, ta amsa masa cikin nutsuwa.

NAJMA: Sannu da zuwa ta fadi cikin biyayya.

FAYZ: Yauwa sannunki dai ya sami kujera ya zauna.

NAJMA: Cike da damuwa a fuskanta ta kalleshi. 'yan kwanakin nan baka dawowa da wuri ina fatan dai lafia?

FAYZ: Wallahi lafia, kawai dai na karbi wata kwangila ne, to dole sainaje na biya idanna tashi daga Office naga yanayin tafiyar aikin kafinna dawo gida shine kawai.

NAJMA: Nagane, Kuma na kira wayanka ma domin naji daga gareka amman baka dauka ba.

FAYZ: Ohh ehh wayana na Mota kuma banma duba ba ciro wayarsa yayi ya duba.

Aikuwa gashinan 4missed calls.

NAJMA: Yanzu kashiga kayi wanka ga Abincinka nan fadar Najma.

FAYZ: Ai bazan iyacin abincin nan ba gaskia.

NAJMA: Meyasa?

FAYZ: Kawai banajin yunwa ne.

Najma kallansa tayi cikin rashinjin dadi.

NAJMA: Yau fa bakayi breakfast ba ka fita Kuma yanzu kace bazakaci abinchi ba?

FAYZ: Hmm danaje Office ne Abbas ya kawo mana Breakfast saboda munfita tare dashi.

Sannan da yamman nan ma munje munci abinchi a Green Square shiyasa.

Kinci abincin ne?

NAJMA: Bazan iyacin abinci ba indai har mijina baici abinci ba.

Nima na koshi.

FAYZ: Kinga Banason kizauna da yunwa gaskia kinjiko.

Zomuje kici abinci.

NAJMA: Ai nima abincin ya fita a raina tinda bazakaci ba.

FAYZ: Aa baza'ayi haka ba kinjiko, muje nida kaina na baki da hannuna.

Najma dai ba haka taso ba.

Tasocin abincin tareda mijinta.

GIDAN ALHAJI SALEH.

MAMA: Ai Gaskia Alhaji kayi kokari duk wani abuda akeyi a biki kayi kokarin yinsa.

Alhaji Saleh ne shida Mama suna zaune suna magana.

ALHAJI SALEH: Auren babban Dana ne kinga Jama'ar dana tara dole nayi bakin kokari na wajen fita kunyar su.

MAMA: Gaskia ne Alhaji ga bakinka na kasar Germany ma.

ALHAJI SALEH: Ehh dayake su Hotel dina na basu kawai su zauna a ciki saboda kinga turawa ne kuma bazasu so ace na hadasu da wasu ba kinsan mutumin da akace ba irinka ba.

Amman da nine ai babu ruwana ko ina aka bani zan zauna tinda ba zama nazoyi ba.

MAMA: Hmmm Alhaji kenan kaima kamar baka sansu ba.

Harka tinamin da mukaje kasar France akace ga daki nan ciki da farlo wai muda wasu turawa sukace bazasu zauna ba.

Kaikuwa kace a baka duka ka kama.

Na dade inacin dariyar wannan rana.

ALHAJI SALEH: To ai Hajia Kinsan su haka suke bakowannen sune keson mu'amala da irinmu ba bakar fata.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now