AHALI GUDA PART 4 PAGE 11

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 11* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

GIDAN MS. DEBORAH.

SHO'AIB: Don't be surprise Deborah aikinsan ina raye dama ban mutu ba.

Ms. Deborah dai cikin mamaki take kallonsa domin ta rasa abin fada.

ALEX: I gotta go Mom,
Alex ya fice daga farlon shima cike da mamaki a fuskarsa.

SHO'AIB: Zan iya zama?
Ms. Deborah tayi masa alama da hannunta akan ya zauna.

MS. DEBORAH: Nasan cewar kazone domin kaga abinda yake faruwa a yanar gizo cewar Rayheelah ta musulunta.

Shine kazo ka dauke 'yarka, karabani da ita.

SHO'AIB: No Sam ba haka bane, Nazone nakara Nusashshe dake gaskia da kuma iko na Allah a kowane irin lokaci.

Deborah kin raba aurenmu dake saboda kawai na karbi addinin Musulunchi, kina ganin idan 'yarmu ta girma zata iya bina kekuma a barki.

Hakan yasa kika raba aurena dake dukda kasancewar Rayheelah tana bukatar mahaifinta a wannan lokacin.

Kika saka mata akidar cewar mahaifinta ya rasu donma kada wata rana tayi tinanin ganinsa.

Sannan kikace ai Lokacinmu babu na'urar daukan Hoto ballan tana ki nuna mata ni.

Sai abu guda daya da kika kasa ganewa shine deborah shifa rabo idan Allah ya kudirta da kai to tabbas da kaidin.

Dukda kasancewar bama tare kuma Rayheelah bata sanni ba gashi abinda dai kike gudu saida ya faru.

Abu guda daya dana kasa ganewa shine shin mene Laifi don mutum yatafi izuwa addinin dayaga yafi dacewa dashi.

Shin mene laifi don mutum yaje kokuma yayi sauyin addini da rayuwarsa.

Deborah karki manta fa ni Pastor ne a church kuma duk wani sirkulle nasanshi.

Amman da bincikena yayi bincike saina gano cewar ba'akan daidai nake ba.

Hakan yasa nayi converting Immediately saboda kada lokaci ya kuremin.

Deborah Dan Allah kufahimchi wannan. Kibar Rayheelah tayi Addinin da takeso kamar yadda kasa tabar kowane dan kasa yayi addinin da yaga shine daidai.

DAN ALLAH.

MS. DEBORAH: DANIEL, Ohh Shoaib I'm sorry. Rayheelah made her Choice since.

Batayi tinanina ba kafinta yanke hukunchi. Babu abinda na ragi Rayheelah dashi tana cikin duk wata daula da wadata ban haneta da komai ba.

Amman tayimin butulchi ta gujeni.

SHO'AIB: Kafin kasancewar Rayheelah karkashinki cikin daula kunkasance a karkashina keda ita cikin daula.

Kada kimanta a baya nine Pastor Daniel, wanda yafi kowane pastor dukiya da tarin arxiki a fadin kasar nan.

Amman hakan bai hanani komawa inda nake ganin shine daidai ba.

Deborah duka dukiyata da komai dana mallaka kece na bawa domin inason tsarkake zuciyata.

Inaso kamar yadda kuka saba da farin ciki da walwala kucigaba koda bana tare daku.

Yanzu kidubeki Kece Minister of defense gaba daya tsaron kowa a kasarnan a karkashinki yake.

Amman Rayheelah duk bata kalli wannan ba bata kalli tarin dukiya da kike da ita ba yasa tatafi tabarki don kawai ta karbi Addinin Musulunchi.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now