AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 4'''
✨ *PAGE 2* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
GIDAN DR. SUDAIS.
Kan Kace kwabo ya karaso a motarsa cikin hanzari ya shigo cikin gidan bayan Rayhan ta kirashi a wayarta.
KARIMA: Sannu da zuwa Dr. Sudais.
Dr kallanta yayi cikin rashin sanayya yace.
DR. SUDAIS: Yauwa Sannu.
Salma da Rayhan ne zaune Rayhan hankalinta a tashe da idonta dukya ciko da kwallah.
DR. SUDAIS: Meyafake faruwa ne Rayhan kinkirani ina Office kince na dawo gida.
Rayhan shiru tayi takasa magana.
SALMA: Ya Sudais kasan wannan baiwar Allah?
Dr Sudais kallanta yayi cikin tinani.
DR. SUDAIS: Bantaba ganinta ba sai yau Salma shinda wani abune kumin bayani mana naga Rayhan bata yanayi me dadi.
Meyake damunta Salma kisanar dani Dan Allah.
SALMA: Dr. Sudais Wannan Baiwar Allah tace tasanka kuma Wannan 'yar da take hannunta yanzu 'yar kace.
Cikin firgici ya kalleta.
DR. SUDAIS: Whatttt!!??
Kara kallan Matar yayi.KARIMA: Koka Mantane Doctor?
DR. SUDAIS: Kinga Kiyi hakuri, yaune Satinmu biyu da aure don Allah idan turoki akayi donki rabani da matata kiyi hakuri.
Kifada musu gaskia cewar niba mahaifin 'yarki bane.
KARIMA: Karka rainawa Kanka Hankali mana Dr. SUDAIS. Kanaso na canja magana saboda kada aurenka ya mutu.
Nikuma nayi yaya da wannan yarinya.?
Yau wannan yarinya tazo gidan mahaifinta saboda haka dole ka karbi 'yarka.DR. SUDAIS: Mekike fadane haka? Shin menayi miki ta ina na cutar dake kifadamin.
Meyasa kikeson lallai saikin rabani da matatata?
RAYHAN: Babu wanda zai rabani da kai Mijina.
Rayhan ta fada cikin goge hawayen fuskarta.Babu wanda ya isa ya rabani da kai, domin bai aureka ba saida na tabbatar da ingancinka.
Da kuma sanin duka wasu halayenka, tayaya zan yadda da wata dare daya tacemin kaine Mahaifin 'yarta.
Kinga kitashi kifita daga cikin gidan nan... kafin nayi miki abinda baki taba tinanin zanyi miki ba.
KARIMA: Idan har baki karbi wannan a matsayin 'yarki ba shikenan zan tafi amman zan dawo.
Kallan Dr Sudais tayi cikin Harara.
Kaikuma saina tona maka Asiri da duk wani biye biyen matanka da kakeyiwa ciki wallahi sai asirinka ya tonu.
Daukan yarinyarta tayi ta fita cikin fusata.
DR. SUDAIS: Rayhan zauna, Zauna dan Allah kidena daga hankalinki.
Rayhan, wallahi bantaba aikata zina ba, wallahi bantaba sanin wata 'ya mace a waje ba. Wallahi Rayhan bantaba soyayya mai karfi ba sai a kanki.
Wallahi banci Amanarki ba.
Rayhan tashi kawai tayi ta koma cikin daki.
SALMA: Yayana Karka damu nida Rayhan duka munsan halayenka.
Kuma wannan Yarinyar turota akayj jikina ya bani, Babu wani wanda zai yadda da ita bama muba kowa.
Tasaka kabaro Office dinka kana aiki. Ka koma zamuyi magana da ita.
![](https://img.wattpad.com/cover/354890165-288-k167984.jpg)
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Fiction généraleLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.