AHALI GUDA PART 2 PAGE 1

3 0 0
                                    

*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 2'''

✨ *PAGE 1* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

'''DA DADDARE.

BAYAN MOH YA DAWO GIDA DA DADDARE DA SANIN ANYI BIKIN BUDURWAR SA NAJMA TAREDA FAYZ. SHIN YAYA KUKE GANIN LAMARIN ZAI KASANCE?

SHIN MEYA FARU DA RAYHAN?
SHIN ZA'A YARDA MAHMOUD YA AURI KHAIRYYA? KUBIYOMU CIKIN LITTAFIN AHALI GUDA PART 2.

GIDAN ALHAJI SAMINU.

MOH: Haba Daddy yanzu shikenan duka abinda na dauko bazaka taba goyamin baya ba.

Nasanar dakai cewar yarinyar nan nakeso a nemamin aurenta amman yanzu...

ALHAJI SAMINU: Kaga ni a kullun wannan fushin naka shine yake sawa kona tashi zanmaka wani abu saina fasa.

Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, akan mace guda daya duk kabi ka daga hankalinka mene hakane?
Moh.

ALHAJI SANI: Nasami Alhaji Barau munyi magana dashi ya tabbatar min da cewar yarinyarsa babu wanda takeso.

Bata fada masa cewar kuna tare ba duk yadda akayi kayi treating dinta yadda ka sabawa mata ne hakan yasa ta hakura da kai.

Kuma a halin da mukayi magana dashi ya sanar dani cewar anyi mata baiko da wanda ta aura yanzu.

MOH: Amman Daddy tin tuni na sanar dakai akan aje a nemamin aurenta haba Daddy.

Moh ne tsaye cikin fushi da fusata yake magana da mahaifinsa.

ALHAJI SAMINU: Kaga Idan mata kakeso gasunan a gari a kasa a duniya baki daya sai wadda ka zaba za'a aura maka.

Shin meyasa kake irin wannan ne sannan yarinyar nan da kakeson lallai saika aureta bafa Asalin 'yar Alhaji Barau bace.

Marainiya ce ya riketa..

MOH: Ni bandamu ba koma wacece Daddy ni kawai ita nakeso fita Moh yayi daga Wajen mahaifinsa cike da kunci a fusace.

Auntyn su ce cikin farlon ta ta tambayeshi lafia?

Shiru yayi mata bai kulata ba yayi fitarsa.

Farlon tazo wajen Alhaji Saminu Baba.

AUNTY HAFSAT: Meyake faruwa ne naganshi ya fita ranshi a bace?

ALHAJI SAMINU: Alhaji ce mata yayi bansan ina Moh yasamo wannan halin ba na zuciya da rashin fahimtar zance.

Wai budurwarsa aka aurar yau shine yazo yake neman dagamin hankali.

Idan har tana sonsa zata bari ta auri wanine idanba shiba aikin banza kai.

Kullun ana nusashshe dashi amman baya ganewa.

AUNTY HAFSAT: To ai sai hakuri kafi kowa sanin halinsa.

ALHAJI SAMINU: Inbana hakuri dashi har makawo yanzu?

Kawomin Ruwa ni.
Fadar Alhaji.

GIDAN CHAIRMAN FAYZ.

Fayz ne shida Amaryarsa zaune kan gado.

FAYZ: Nasan cewar yadda nabi umarnin mahaifina haka kema kikabi umarnin mahaifinki Najma.

Najma kamar yadda ahalin yanzu nake a matsayin mijinki haka kema kike a matsayin matata.

Wato Najma babu abinda ya hadamu sai Alkhairy idan kika dubi irin haduwar mu.

Nasan cewar iyayen mu bazasu tabayi mana zabin da bai dace damu ba duka.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now