AHALI GUDA PART 4 PAGE 3

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 3* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

DA DADDARE.

GIDAN ALHAJI SAMINU.

Moh ne yashigo cikin gidan Farhan ce zaune tana jiran Mijinta yazo ya dauketa.

FARHAN: Sannu da zuwa Ya Mohammad.

Ko kallanta baiyi ba ya shige izuwa dakinsa.

Farhan Kallan Aunty Hafsat tayi Alamun meyake faruwa.

Tashi tayi ta bishi izuwa dakinsa.

Moh zaune yake kan kujera ya dafe kansa Alamun ya gaji.

FARHAN: Meyafaru Ya Mohammad ko haryanzu fushi kakeyi dani akan auren Syed?

MOH: Uban wayace kishigomin daki ko sallama babu.

Bakida Hankali ne?

FARHAN: Kayi Hakuri Ya Mohammad.

MOH: Fita to...

FARHAN: Amman Ya Moh...

MOH: Kifita Banason Ganinka Dallah Malama.

Farhan Kallansa takeyi cikin tausayinsa sannan ta fitan bata kara cewa komai ba.

Farlo ta dawo ta zauna kusa da Aunty Hafsat.

FARHAN: Wallahi Aunty Hafsat tausayin Ya Mohammad nakeyi.

Gani nakeyi kamar akwai abinda yake damunsa.

Domin gaba daya wannan Dabi'ar tasa tayi tsauri da yawa.

Kuma babu wanda ya kyale sai Daddy.

AUNTY HAFSAT: Hmm Farhan kenan, Wallahi Nima tausayi yake bani.

Saboda Kamar akwai damuwa a kasan zuciyarsa.

Kuma yaki yadda yayi magana da kowa ballan tana aji meyake damunnasa.

Randa nashiga zan tambayeshi ma katseni yayi yacemin ya gode baimaji abinda zance ba.

Haka na baro dakinnasa.

FARHAN: Toni yanzu kai tsaye ma yacemin na fitar masa daga daki...

Kuma kinsan fa ni dama haushina yakeji akan na auri Syed.

Saboda baya sonsa sunsami matsalar kasuwanci tin kafin auren namu.

AUNTY HAFSAT: Allah dai ya kiyaye ya kuma yaye masa koma mene.

FARHAN: Amin Amman Daddy ne ya yakamata ya yi masa magana.

AUNTY HAFSAT: Toba sai in suna haduwa ba. Kina gani Mahaifin yanzu fa ba ishashshiyar lafia gareshi ba.

Ni banason sanar dashima duk wani abu da zai daga masa hankali.

FARHAN: Hakane Gaskia. Allah ya baiwa Daddy lafia dai.

AUNTY HAFSAT: Amin Farhan.

GIDAN MS. DEBORAH.

MS. DEBORAH: I don't really know what's your problem again Rayheelah.

Bakyason Muzauna lafia daga kijawo wannan rigima sai wancen?

Me Christianity yayi miki da zaki fita daga ciki?

Shin me kika rasa a tattare dashi ko ahalinki.

RAY: Kwanciyar Hankali Mom.
Ina rayuwa kullun Amman hankalina ba'a kwance yake ba.

Daga wannan yaci Amanata sai wancen ya yaudareni yau ina fada dake gobe munshirya jibi munkara fada.

Haba Mom, ke Hankalinki a kwance yake Amman banda nawa.

MS. DEBORAH: Rayheelah, Duk ba wannan bane, Wannan duka wani abune daban.

Rayheelah kada kifita zakka a cikinmu. Mune Family dinki kuma mune muke sonki. Meyasa kikeson barin cikinmu?

RAY: Mom ba barin cikinku zanyi ba, ina tare daku.
Kawai zan sauya Tsarin rayuwata ne.

Wallahi Mom Islamic Religion nakeso na gano shine Addinin daya dace dace.

Ba ina nufin Christianity bayada kyauba.

Issa believe ku bautawa abinda kukeso nima na bautawa abinda nakeso kuma na yarda dashi.

MS. DEBORAH: Oh My God! Rayheelah They Charmed you.

Sun asircekine bakya fuskantar komai

But Addininmu Is the best kinsani kema Rayheelah is just that idonki ya rufe.

RAY: Ba haka bane Mom, Wallahi Duk abinda nake gani hakane.
Babu wanda yayimin Asiri thats the real truth.

Mom Don Allah kibarni idanke bazaki musulunta ba.

Wallahi i don't like being Christian anymore, please I'm beggin you mom.

MS. DEBORAH: Give me your phone Ray.

Ms deborah kwace wayar Rayheelah tayi.

MS. DEBORAH: Laifi nane da na barki tinfarko kike mu'amala dasu.

Babuke babu Lubabatu, Syed da duk wani Muslim Friend na rabaki dashi yau.

As from today, Sannan Zaki zauna a gida na tsawon 1Month bazaki fita ba doctor zaizo ya dubaki.

Sannan Zanturo daga church za'ayi miki Addua.

Donna fahimchi bake bace.

Idan kuma kinsami sauki to zan hadaki da DSS Masu karfi ta yadda duk wani wanda ya tinkareki idan Musulmi ne zan basu umarnin su harbeshi har lahira.

Kinji na fada miki Try me and see kinsanni ai.

Mahaifiyar wucewa tayi izuwa dakinta dake sama.

Rayheelah ce tsaye gabanta tana zubar da hawayenta domin Matakan sunyi tsauri akanta.

GIDAN DR. SUDAIS.

DR. SUDAIS: Wallahi Rayhan Bansanta ba, Bansan daga ina take ba bantaba ganinta ba. Banda wata Alaqa da ita wallahi.

RAYHAN: Kodama ace kasanta Meyasa bata fito tinda dadewa tazo gareka ba sai yanzu?

Dataga kayi aure sannan shine zatazo don kawai tasaka mana kokonto cikin rayuwar aurenmu.

Na yarda da kai Doctor, kuma na yadda da kaina Doctor babu wanda zai shigo tsakanina da kai In Shaa Allah.

DR. SUDAIS: In Allah Ya yarda Rayhan, Wallahi Tinani nake akan wacece ita? Kuma waya turota?

Idanma ba turota akayiba nime nayi mata? Da take Kusantata da wannan sabon?

RAYHAN: Manta da ita Doctor Muje muci abinchi dama kai kadai nake jira kadawo.

Yunwa nakeji sosai.

DR. SUDAIS: Thom Rayhan, Nima Yunwa nakeji dama.

Tashi sukayi suka nufi Dining Table doncin Abinci.

BAYAN KWANA BIYU.

GIDAN MS. DEBORAH.

Rayheelah Ce Cikin dakinta kwance Talabijin din bangonta tanatayi.

Gefe kuma Laptop dintace a kunne rufda ciki dake a kangado tarasa me yake mata dadi.

Knocking kofar dakinta akeyi.

RAY: Come in...

Shigowa Hanne Me Aikinsu Tayi tareda Drinks a hannunta.

RAY: Mom tafita ne?

HANNE: Eh Ta fita..

RAY: Okay Ajiye to...

Ray Hanne kawai tabi da kallo tana tinani..

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now