AHALI GUDA PART 3 PAGE 13

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 3'''

✨ *PAGE 13* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

GIDAN ALHAJI SAMINU.

MOH: To ai kofan a bude yake shigo.

Aunty Hafsat budewa tayi ta shigo cikin Sallama.

Kallan ta yayi sannan ya tsaya da aikin.

AUNTY HAFSAT: Tinjiya ai naso nazo to kuma baka shigo da wuri ba sai yau.

MOH: Jiya Naje Wani wajene, yanzu Ina aiki Meyafaru?

AUNTY HAFSAT: Ai Magana nakeso muyi ne kuma zata dan dauki lokaci ko zaka ajiye aikin kabani mintina Talatin haka.?

MOH: Banda Mintina Talatin dinda zan iya baki kinada Minti goma fadi meya kawoki wajena yanzu a daren nan?

AUNTY HAFSAT: Dama Magana ce
Akan mahaifinka, abinda yake faruwa tsakaninka dashi nace bari nazo nayi maka magana.

MOH: Shawara ce Ko Umarni?

AUNTY HAFSAT: No shawara ce kawai.

MOH: Tinda shawara ce zaki iya bayarwa,

AUNTY HAFSAT: Shin meyake faruwa ne? Meyasa kakeyi masa haka Moh? Shifa mahaifinka ne.

Kuma yanason cigaban ka, duk wani abuda zai cutar da kai Yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya hanashi zuwa wajenka.

MOH: Kina cinye lokacin naki da magana ki bada shawarar da zaki bayar ki tafi Ina aiki na fada miki.

AUNTY HAFSAT: Dan Allah Moh Kadainama Mahaifinka abinda kakeyi masa.

Wallahi babu kyau yiwa Iyaye irin wannan abin.

Ka tina Mahaifin kane shidin.

MOH: Shikenan Nagode Zaki iya tafiya saida safe.

Aunty Hafsat tashi tayi domin kuwa Moh katseta ma yayi bata kaiga fadin abinda takeso ba.

AUNTY HAFSAT: Allah ya tashemu Lafia.

MOH: Amin.

aikinsa yaci gaba dayi.

WASHE GARI.

CAVENDISH UNIVERSITY.

KHAIRYYA: Wallahi Bakaji zuciyata ba da Abbah yace wani yayi masa magana ta.

MAHMOUD: Kinfiya Gajen hakuri ai nace miki zanyi fixing komai ai.

Shin kina ganin zan zira ido a kwacemin ke? Ai bazaiyu ba kema kinsani.

KHAIRYYA: Nayi mamakin yadda kayi komai cikin hikima Ya Mahmoud.

Shifa Abbah baisan cewar mundade muna tare ba duk a tinaninsa yanzu ne ya hadamu.

MAHMOUD: Hhh Nasani Ai, kuma ina sane da hakan shiyasa na lissafa komai a nitse.

Kinyi tinanin sai lokaci ya kure ko? Ina ai babu wannan maganar.

KHAIRYYA: Gaskia ina cikin farin ciki marar misaltuwa Ya Mahmoud.

Jina nakeyi tamkar wadda ta sami 'yan cin kai.

MAHMOUD: To ai kusan hakanne Khairyya.

KHAIRYYA: Ya Syed Ya Sani Kuwa?

MAHMOUD: Hmm To ai shine wanda ya bani karfin gwiwar tinkarar Abbah a wancen lokacin.

Kinzata yayan naki kamar sauran yayyi ne toshi na musamman ne.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now