AHALI GUDA PART 4 PAGE 9

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 9* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

POLICE HEADQUARTER.

OFFICER: Zauna Mana kintsaya kina kallansa.

Karima zaunawa tayi tana kallan Dr sudais cikin mamaki.

OFFICER: Yallabai gatanan saikuyi magana.
Sannan Officer ya fita.

Dr Sudais cire Gilashinsa yayi cikin mutsuwa.

DR. SUDAIS: Kinyi mamakin ganina ko? Toba abin mamaki bane wannan kadan daga abinda zan iya aikata miki kenan.

Domin kema bakisan wayeni ba kallo na kawai kikeyi Karima.

Wannan duka shiri nane domin nasa kigane kurenki.

Saidai sukansu 'yan sanda basusan gaskia ba kuma koda kinfada bazasu yarda ba.

Kindawo rayuwata kinason lalatamin aure kuma kinason rabani da matata.

Mene laifi na? Laifi na shine kawai donnaki aurenki?

Shine zakimin Qazafi.

KARIMA: Amman karasa wane irin Sharri zakamin saina sata yanzu kowa a barauniya yake gani kuma bayan kasan sata ba halina bace.

DR. SUDAIS: Danaki Sharri da nawa wanne yafi muni.

Karki mantafa A gaban matata kika furta cewar ni mazinaci ne, sharrin Zina kikamin kuma haryanzu baki janye ba.

Dr. Tashi tsaye yayi inda yake kallan Karima.

A wannan takardar da kika saka hannu akwai tabbaci da kuma Alqawarin zakifita daga rayuwata nida Ahalina.

Sannan idan har kika shigo rayuwata wallahi tallahi Karima saina daureki kuma babu wanda ya isa ya fito dake.

Ga takarda nan wajen hukuma idanma ni kinrainani.

Sannan yanzu ma ban rabi dakeba har saikin koma wajen matata kamar yadda kikaje kika batamin suna.

Inaso kikoma kifada mata gaskiar abinda kika sani kuma gaskiar abinda ya faru.

Idanba haka ba zan daureki abisa batamin suna da kika kuma kinsan hukuncin yin hakan.

Karima ta kasa kara furta komai domin kuwa tana matukar tsoron hukuma.

DR. SUDAIS: Yanzu zantafi zanbarki anan idan kinyi shawarar zuwa saikisa sukirani.

Idan kuma bakiyi ba shikenan.

KARIMA: A a Dan Allah karka tafi, zanje wallahi zanzo har gidan naka.

Amman Dan Allah karka barni Anan Dr Sudais wallahi nayi dana sani kayi hakuri.

DR. SUDAIS: Bani zaki bawa hakuri ba Matata ce saboda haka nina yafe miki amman kisani itama tanada haqqina.

Kine ki karyata kanki tinda dama ba yanzu kika saba hakan ba.

Envelope ya mika mata, Kudine a ciki.

Haryanzu Inajin Tausayinki, Naira dubu dari ne kiyi kokarin gyara rayuwarki kizama mace ta gari.

Kimutunta kanki sannan sai a mutuntaki, Allah ya yafe mana baki daya.

Cike da kwalla Karima takalli Dr Sudais dukda abinda tayi masa amman ya bata kudi.

Lallai tayi dana sanin bata masa suna...

Fita yayi kansa tsaye domin ya gama magana da ita.

GIDAN SU MAHMOUD.

MUFEEDAH: Toh Alhamdulillah, Nima wannan magana tayimin dadi kwarai da gaske.

Domin kuwa Ya Mahmoud ya fada tana iyayiwuwa duka Abbah yace a hade bikin kawai.

NASIR: Gaskia ne Nima nasan idan har naje da maganar hakan zata iya faruwa shiyasa banje da ita ba.

Kuma kwatsam sai Ya Syed ya fada masa.

Kuma Ya fahimta.

MUFEEDAH: Allah sarki, Ai hakanma yayi Allah dai ya sakawa Abbah da Alkhairy domin babu abinda zamuce masa.

NASIR: Gaskia ne Abbah yayimana Abubuwa da dama wanda bazamu taba kwatanta biyansa ba.

MUFEEDAH: Hakane, Yanzu mene abuna gaba?

NASIR: Hmm Mufeedah kece zaki fadamin ai, sannan da kuma nawa kike bukata na baki a hannunki na kashewa.

Saiki fara shirye shirye kinga gaba daya Sati daya ne ya rage a madadin sati biyu nasu Ya Mahmoud din.

MUFEEDAH: Ehh Hakane.
Amman ni bana bukatar komai fa kawai gyaran jiki ne shima kuma akwai kudi da Ya Mahmoud ya bani jiya.

Zanyi Amfani dasu karka damu.

NASIR: Aa kekuma kudinda Ya Mahmoud ya baki wannan kudin ya bakine a matsayinki na kanwarsa bayason kizauna babu kudi.

Bawai ya baki bane saboda kiyi amfanin bikinki dasu saboda haka ki fadamin kawai saina baki.

Ai daga hannuna kudaden ya kamata su fito bashi ba.

MUFEEDAH: Hmmm.

Sukacigaba da maganar.

HIGHWAY.

Mahmoud ne shida Syed cikin mota.

MAHMOUD: Yanzu yaya kukayi da Shi mahaifinnata.

SYED: Kasan dayake shibabbane kuma yanada fahimta nayi masa bayanin komai.

Kuma ya fahimta don Ahalin da akeciki yace lallai tadawo gida.

MAHMOUD: Gaskia ne kasan Duk inda akace babba to babbanne.
To Amman ita Farhan dinfa kunyi magana da ita?

SYED: Bamuyi magana da itaba Mahmoud, domin kuma har ila yanzu farhan a sama take bazata saurareni ba.

Bakuma zata gane abinda nake nufi ba.

Zanbari ta huce saina sanar da ita karin aurena.

MAHMOUD: Ehh hakanma tinani ne me kyau. Sufa cen gida?

SYED: Babu wanda na sanarwa tukuna inason nafarajin ta bakin Rayheelah first shiyasa yanzu zamuje wajenta.

Idan har naji ra'ayinta akai saina sanar dasu a gida.

Kuma abinnema ya hademin gashi akan bikinku duka Abbah nine ya dora akan komai nima kuma ga maganar nawa auren yanzu.

MAHMOUD: Hmm Kaine babban yaya ai Chairman sannan kuma maganar aurenka wannan kaine ka jijjibowa kanka.

Saboda haka Allah ya zaba mana abinda yafi zama Alkhairy a garemu baki daya.

SYED: Amin don Alfarmar Annabi Mahmoud.

Zamuje Wajennata ne kokuwa zaka ajiyeni saika wuce Office din?

MAHMOUD: No babu damuwa muje kawai mugama saimu wuce Office din tare.

Sukaci gaba da tafiyarsu a mota.

GIDAN DR. SUDAIS.

Rayhan ce saikuma Salma tareda Karima a zaune a kasa cikin nadama ta sunkuyar da kanta.

SALMA: Kince kinzo da ma

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now