AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 3'''
✨ *PAGE 6* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
GIDAN MR PETER.
MR. PETER: Akanme Alex zai aikata wannan? Meyasa yakeson jawomin rigimane.
CSP JARMA: Ahalin yanzu Yallabai idon kowa akan wannan case din yake domin Rayheelah ta sanarwa da 'yan jarida komai.
Kuma jira suke suga matakin da doka zata dauka akansa.
Mr Peter tashi yayi tsaye,
MR PETER: Rayheelah ce tayi haka? Why would she do that?
Ohh My God but what happened ya akayi sai yanzu nake sanin wannan?
CSP JARMA: Rayheelah tacemin tin kafin case din yazo yanzu taso tayi maganin abin.
Alex ya sauke dan sandan data dora akan case din yayi masa barazana sannan kuma ya rabashi da aikinsa.
Hakan yasa tazo ta sameni dubada tana bukatar wanda zata yarda dashi.
Yallabai idan da akwai yadda za'ayi maganin wannan matsalar to a hanzarta yinta.
Domin karamin abinda muke rainawa yana iya zuwa yafi karfinmu.
Domin bama 'yan jarida ba idan duniya harda gwamnati maici kowa idonsa yana kanka yaga abinda zakayi.
Mr Peter tsaye yake cikin fushi da bacin rai yarasa me yake masa dadi.
MR PETER: Deborah tasan da wannan?
CSP JARMA: Rayheelah ta cemin tasani Yallabai.
MR PETER: Shikenan zaka iya tafiya sannan kasanarwa da Headquarter a maida Dan sandan da Alex ya cire daga aiki.
Inaso ya koma aikinsa nan take.
Tabbas zan dauki mataki akan Alex, zaka iya tafiya Jarma.CSP JARMA: Shikenan Yallabai nagode.
Tsaye Mr Peter yake yana kallan Hoton Alex dayake jikin bango.
WATA UNGUWA.
Moh ne ke tafiya a mota yana waya.
MOH: Nakusa karasowa Office din ai na dan fitane ma.
Yauwa Thank You.
Wata Budurwace tazo wucewa kawai ya bugeta da mota yana waya.
Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un.
Cikin Sauri ya fito daga Motar tasa kan kace kwabo mutane ne suntaru.
MUTUM 1: Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un wannan ai Daibat ce.
MUTUM 2: Wallahi itace Malam kamata muje a kaita Asibiti.
MOH: Bude Motar sa yayi aka sakata a ciki.
MUTUM 1: lukman aje a sanar a gidansu zamuje Asibiti a kaita.
Muje Malam Kaimu Asibiti, shiyasa akace kudinga tafiya a hankali.
Yanzu kalli yadda ka bugeta yarinya nitsatstsiya mai hankali.
MOH: Tsautsayi ne kawai Malam Banga shigowarta ba wallahi.
MUTUM 2: kataka mota kawai muje a kaita dan Allah.
GIDAN ALHAJI SALEH:
NAMRAH: Ai shine abinda nake fada miki tintini Khairyya kikaki ki fahimceni.
Yanzu shi Ya Mahmoud din meyace?
KHAIRYYA: Yacemin kawai nacigaba da sauraron sa wai zaiyi maganin komai kawai na jira zanga abinda zaiyi.
NAMRAH: Nima dai nasan muddun yana raye babu wani abuda zaizo yasa yanaji yana gani ki kubuce masa.

YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Ficção GeralLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.