AHALI GUDA PART 1 PAGE 7

2 0 0
                                    

*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART ONE'''

*PAGE   7️⃣*

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

'''SHOPPING MALL.

FARHAN: Gwara ka dauki wannan ai yafi kamshi.

SYED: Thom saminshi a nan.

Farhan ce itada Syed suna siyayya.

Aini nama gama saidai ke idan kina bukatar wani abu.

FARHAN: No ni bana bukatar komai gaskia am craving muje musha ice cream mubar wajennan.

Okay, karasawa sukayi wajen Biyan kudi.

Syed mika ATM dinsa yayi domin a ciri kudin.

Saka masa kayansa akayi a leda sannan ya karba suka fito.

FARHAN: Bani key din naka najamu.

Syed mika mata yayi sannan ta bude motar baya ya saka kayan ya shiga.

Wayarsa ya duba yace
SYED: Namanta ma zan turama Khairyya kudi.

FARHAN: tana ina?

SYED: No kawai na bata motanta ne dazu so nace zantura mata kudi tasa mai.

FARHAN: Okay nagane, Allah sarki Khairyya ai tanada hankali meyasa ka kwace motan da.

SYED: Aa ba kwacewa nayi ba kawai dai ta hutane.

FARHAN: Hmmm wane hutu itada take School ma.

SYED: Kawai dai banason ya zamana koda yaushe tana hanya driving ne ita kadaice mace da muke da ita.

Kuma munada Plan akanta sosai so banason wani abu ya sameta koyaya ne.

FARHAN: Hakane kuma amman babu abinda zai faru da ita sai Alkhairy, Allah ya barmu tare baki daya.

SYED: Ameen thumma ameen.

GIDAN MS. DEBORAH.

Kawartace Luba, tsaye waje tana kiranta domin ba kowa ake bari ya shiga cikin gidan ba.

Kiranta tayi a waya,

RAY: Baiwa Security din.

SECURITY: "Hello Hajia?"
RAY: Yauwa Itadin kawana ne kubarta tashigo.

SECURITY: "Okay Hajia, zakiyi iya shiga"

Luba shigowa cikin gidan tayi Abinda yasa bata fiya zuwa wajen Luba a gida ba saboda duk zuwa saita kirata.

Ray ce zaune ita kadai a Garden din gidansu.

Hanne mai aikin suce tazo takawo Drinks wa Luba tinkan takaraso.

Luba karasowa tayi ta zauna.

Ray rungume Luba tayi
RAY: Sannunki da zuwa Luba.

LUBA: Yauwa sannu Rayheelah.

Kina gida yau baki fita ba kenan?

RAY: Ehh Luba banfita ba kinsan Mom bata zama, ba koyaushe take zama ba.

So shiyasa ni nake zama saboda kar adinga barin gidan sai masu aiki da kuma Securities babu kowa.

LUBA: Yeah sure, you're right.
Luba ta fadi.

RAY: Ehmn Amman nayi mamakin ganinki fa.

LUBA: Haba? Kinsan naje nan bayan quaters dinnan naku ne stretching so kawai nace barina karaso.

RAY: Mugani Ai Sun iya Gyaran kai sosai nima nan nake zuwa.

LUBA: Wallahi sun iya kuma wajen babu hayaniya ba kamar cikin gari ba.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now