*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART ONE'''
*PAGE 6️⃣*
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''GIDAN ALHAJI SAMINU.
ALHAJI SAMINU: Shikenan Babu damuwa Dama Yau Mun zauna da Mahaifinsa kuma Ansaka ranar bikinku nan da karshen watan nan in Allah ya kaimu da rai da lafia.
Wani farin ciki Farhan taji fal zuciyarta.
Taji dadi matuka dama batada buri irin ace yau za'ayi bikinsu itada Syed.
Tashi kije Allah yayi miki Albarka.
Duka wani abuda ake bukata zanyi magana da Hafsat inyaso sai ayi duk abinda ya kamata.
FARHAN: Thom shikenan Daddy nagode Allah ya saka da Alkhairy.
ALHAJI SAMINU: Karki damu Kinji Allah Yajikan Mahaifiyar ku.
FARHAN: Ameen ameen Daddy.
Farhan tashi tayi tafito daga Farlon mahaifinta sannan ta nufi dakinta.
Moh da yake tsaye ne ya bita cikin dakinta.
MOH: Wai shin meyake damun kune keda Daddy?
Idonku ya rufe ku dole saikun hada zuri'a da Wancen Yaron?
Farhan ce tsaye tace
FARHAN: Ya Mohammad me yafaru?MOH: Kinfini sani ai, Bakida labarin abinda yayimin yau?
Yadda yacimin mutunci?
FARHAN: Ya Mohammad baka fahimceshi bane amman Allah Syed bayada wulakanci.
MOH: Kimin shiru dallah karna bibbigeki anan idonki ya rufe ana wulakantani bakya gani.
To bari kiji na fada miki ni babu hannuna a aurenki kuma bana goyon bayan wannan auren naki.
FARHAN: Ya Mohammad wai meyayi zafi ne haka?
Shin me Syed yayi maka da baka sansa?
MOH: Wannan tsakanina dashi ne tinda duk baku gani ba.
Sai da safe.
Cikin fushi ya fita daga dakinta ya wuce izuwa dakinsa.
Zama Farhan tayi kan gado tayi shiru kiran wayar Syed ne ya shigo wayarta.
Kalla tayi sannan ta daga.
FARHAN: Hello,
SYED: "Assalamu Alaiki,"
FARHAN: Amin Wa'alaika Assalam Mijina abin alfahari na.
SYED: "Kin wuni lafia matata?"
FARHAN: Nawuni lafia lau Alhmdullh, Kaifa ina fatan kana lafia dai?
SYED: "Ehh yanzu dai ina lafia tinda nasamu naji muryanki"
FARHAN Toh Alhamdulillah! Tinda har yanzun kana lafia.
Ya gida yasu Mama da Abbah.
Khairyya da Nasir?SYED: "Duka suna lafia lau ya mutan gidan?"
FARHAN: Suma suna lafia.
SYED: "Toh Masha Allah. Yanzu Abbah yake sanar dani kancewar An saka ranar bikinmu nidake karshen watan nan"
Cikin jin kunya Farhan tace
FARHAN: Nima Yanzu na dawo daga Farlon Daddy ya fadamin.SYED: "Toh Alhamdulillah, Na Matukar jin dadin yadda aka saka nan kusa bada dadewa ba."
FARHAN: Nima haka Dama banada buri irin na dinga ganinka koda yaushe a tare dani.

YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
General FictionLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.