*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART ONE'''
*PAGE 1️⃣3️⃣*
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''GIDAN ALHAJI SANI.
ALHAJI SANI: Allah yayi maka Albarka Faizu.
Yadda kake farantamin Allah Ubangiji ya cigaba da faranta maka.
Yadda kake sani farin ciki Allah Ubangiji yaci gaba da saka cikin farin ciki.
In Allah ya yarda bazaka taba kuka da zabin danayi maka ba Faizu.
Fayz kansa kawai yake girgidawa domin yana kara wata kalma kuka zaiyi.
Cikin biyayya yace saida Safe Alhaji.
Dakinsa ya nufa zuciyarsa babu dadi.
Bai taba tsintar kansa a irin wannan yanayin ba.
Lallai yau kwanan bakin ciki Fayz zaiyi.
Wayarsa ya dauka yake kallan hoton Rayhan da fadin
FAYZ: kiyi hakuri Rayhan.Allah baiyi zamu rayu tare ba yana fadi hawaye na zuba a fuskarsa.
Allah yasani nasoki kuma naso rayuwa tare dake.
Saidai Allah baiso hakan ba, Ina kaunarki Rayhan ina kaunarki sunkuyar da kansa kawai Fayz yayi cikin kuka da takaici.
Domin ba'a taba macen dayaso irin Rayhan ba.
Haka ya kwanta yana kallan Hoton Rayhan ya kasa bacci.
WASHE GARI.
GIDAN CHRISTINA.
'Yan Sanda ne ta ko ina.
Jini ne a kasa a cikin gidan.
Kawar Christina ce tazo Lobby.
Dpo ne tsaye yana waya.
Kuka Lobby takeyi da fadin
LOBBY: Where is Christina?Dpo katse wayarsa yayi
DPO SHAGARI: wacece ita?
SERGEANT: kawar tace Sir.
DPO SHAGARI: Turomin ita nan.
SERGEANT: Okay sir.
Lobby ce takaraso wajen Dpo.
DPO SHAGARI: Mene Alaqarki da ita?
LOBBY: She's my friend, she's my best friend cikin kuka inji Lobby.
DPO SHAGARI: Shin batada iyaye ne anan?
LOBBY: Batada su itaba 'yar garinan bane.
Karatune ya kawota kuma data gama ta zauna.
DPO SHAGARI: But tayaya bayan tagama karatu zata zauna anan?
ko tana wani aiki ne?Sannan wane makaranta tagama?
LOBBY: Bata aiki kuma Cavendish University ne yallabai.
Lobby take fada cikin Kuka.
DPO SHAGARI: Okay, wannan gidan waye?
LOBBY: Wannan gidan tane,
DPO SHAGARI: Kamashi tayine ko siya tayi?
LOBBY: Saurayin tane ya siya mata Yallabai lobby tana fada tana kuka.
DPO SHAGARI: Saurayinta?
LOBBY: Yes sir she has a boy friend.
DPO SHAGARI: To wannan Motar fa?
LOBBY: Itama tatace duka komai na gidan nan natane yallabai.
Saurayin tane ya siya mata komai.

YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Fiksi UmumLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.