AHALI GUDA PART 4 PAGE 8

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 8* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

STARVIEW HOTEL.

Rayheelah ce tareda Syed a cikin mota.
Cikin wani irin kallo na rauni da tausayi ray ta kalli Syed daya furta maka kalmar aurensa.

SYED: Nasani cewar zakiji abin wani iri Rayheelah domin baki taba tsammanin zakiji wannan maganar daga bakina ba.

Amman inaso kifahimceni kikuma amince tareda yarda dani.

Rayheelah Ina Sonki kuma bada wasa nake miki ba.

Dagoda Kanta tayi dukda kasancewar tarasa mezatace masa saidai akwai abin fada.

Cikin sassanyar murya..

RAY: Syed bansan wane iriyar amsa zanbaka ba domin kazomin da maganar da bantaba tinaninta ba.

Syed kanada mata kuma nasanta, shin dawane ido zan kalleta ace na auri mijin ta?

Sannan iyayenka shin tayaya zasu yarda ka auri Christian? Shin kai abin baiyi maka wani iri da yawa ba?

SYED: Look Rayheelah ni bana kallan komai idan harna tinkari abu kalubale ko madadinsa sam basa bani tsoro yayin tafiyar da lamuran gabana.

Rayheelah Farhan tasanki kuma hakan bashine zaisa idan ina sonki naki aurenki ba saboda ita.

Allah ya halartamin da in auri mata hudu muddun zan samar da Adalchi a tsakaninsu.

Tabbas inason Farhan kema kinsani kuma tabbas ina sonki Rayheelah.

Idan har Farhan bazata iya zama dakeba tonima ban cancanceta ba saboda batason abinda nakeso.

Rayheelah Keba abin gudu bace keba abin kyama bace kinada duka abubuwan da namiji yakeso a tattare dake.

Sannan bantaba haduwa da mace mai irin halayyar kiba badon a gabanki nake fadan wannan ba.

Cikin wani irin yanayi Rayheelah ta kalli Syed.

RAY: Shin zaka aureni Saboda kanajin tausayina ne kokuma zaka aureni saboda kana sona?

SYED: wata soyayyar takan farawa daga tausayi kuma ta girma.

Daga wunin mu tare a yau zuciyata ta aminta dake kuma tafara kwadayin aurenki a matsayin matata.

Bugu da kari zakishigo Addini na addini mai haske inaso na karasa ladana na aureki domin kasancewa tare dake na har abada Rayheelah.

RAY: Abbanka da Mama? Family dinka yazasu kalli abin? Ko shekara bakayi ba da aure.

SYED: Nasan suwaye Ahalina Rayheelah kece bakisansu ba.

Amman zantabbatar miki da cewar yadda kike tinaninsu ba haka suke ba.

Nidai kawai kibani dama Dan Allah.

Rayheelah shiru tayi domin bazata iyacewa Syed Aa ba.

RAY: Saida Safe Syed.
Rayheelah ta fita daga cikin motarsa a yanayi na tinani.

Syed kuwa kallo kawai ya bita dashi domin kuwa har zuciyarsa yake sonta.

WASHE GARI.

GIDAN ALHAJI SALEH.

Alhaji Saleh ne shida Syed Da kuma Detective Habu sai Mahmoud da kuma Nasir.

D. HABU: Wannan Shine dalilin dayasa nace barinazo domin tin farkon aikinnan kaine ka dorani.

Kuma gasu Syed ma baki daya don tin ajiya shi Nasir yace bama za'a saka wannan kudin a asusunsa ba domin ba kudinsa bane.

Dubada takardu da cike cike kotu ta umarci a mayarwa da kowa kudinsa da ita yarinyar ta damfara.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now