AHALI GUDA PART 2 PAGE 7

4 0 0
                                    

*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 2'''

✨ *PAGE 7* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

'''GIDAN HUTAWA NA ALHAJI SALEH.

Alhaji Saleh ne shida Alhaji Barau Ga Kuma Alhaji Sani saikuma Alhaji Saminu.

Tare suke da wasu Manyan bakinsu suna tattaunawa

ALHAJI SANI: Ni Ina Ganin Alhaji Saminu yadda Alhaji Saleh ya fadi shine abinda ya kamata ayi.

Yanzu Prof. Adamu kana ganin akwai shawarar data wuce hakanne?

ALHAJI SAMINU: Hmmm, Alhaji Sani kenan.

Kaifa bakasan takan tafiyar aiki irin wannan ba domin kai ba'a kasar nan kake lamuraka ba.

Sannan duba da irin wannan Babban Gini dole ana bukatar sanannu daga fanni da dama.

Cewar Alhaji saminu.

ALHAJI SANI: To aini ina ganin wannan ba maganace ta kana rayuwa a kasa ko akasin haka ba.

Kasancewar ka dan kasa ma kadai ya isa Alhaji Saminu.

Sannan fa yanzu idan ka duba zakaga babu kamfanin da acikin mu da baizuba kudinsa ba.

ALHAJI SALEH: Ahh Hakane. Alhaji Saminu da Alhaji Sani kunyi Magana.

Domin wannan aikine babbah.

Kuma ni ina ganin a yadda aka dauko aikin nan kawai a tafi a hakan.

Kokuwa Alhaji Barau?

ALHAJI BARAU: Tho aini idan kuna magana Banacewa komai domin kunsancewar matsayarku da kuma Ra'ayinku shine nawa a koda yaushe.

ALHAJI SALEH: Hakane Alhaji Barau, Amman a lamari irin wannan ya kamata kaima kadan dinga cewa wani abu koyaya ne dai kaima yakasance kace.

ALHAJI BARAU: Hmm Alhaji Saleh Aini banida tacewa.
Inji Alhaji Barau.

Prof. Adamu yanzu mene abinda ya kamata ayi?

PROF. ADAMU: Toh Abinda ya kamata shine, tura maganar izuwa gaban gwamnati.

Idan harta yarda ta amince to shikenan za'a iya fara aiki daga nan zuwa kowane lokaci.

ALHAJI SALEH: Ahh Prof. Adamu Narigada na tura wannan maganar gaban Shugaban kasa.

Kuma jiya munzauna duka da manya harda mataimakin shugaban kasa da Ms. Deborah Michael.

Kasan aiki irin wannan Ana bukatar tsaro a cikinsa.

Kuma don madai Shugaban kasa na London kuma kaga saida ya tafi aikin ya taso.

Yanzu maganar da nake muku anan shine Mataimakin Shugaban kasa ya bamu takardar APPROVAL da aikin.

Sannan Ms. Deborah ta bamu 'yan sanda da Mopol domin kulawa da aikin.

Inji Alhaji Saleh Ansari ya fada.

Cikin Fara'a dukansu sukayi mamaki domin bai sanar dasu hakanba.

ALHAJI SANI: Gaskiya Alhaji kayi kokari amman da ka sanar damu ai anyi zamantare kokuwa?

Alhaji Sani ya fada.

ALHAJI SALEH: Aa ai dayake wannan ba wata babbar Magana bace shiyasa sannan babu wani aiki da zankai gaban Wannan gwamnati da zatayi rejecting nasa.

Domin koda na gama gina wannan kamfani tofa rage musu Matasa zamuyi.

Duk wani wanda yakeda karatu kuma ya cancanta zamu daukeshi aiki domin a rage marasa aikinyi a kasa.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now