*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 2'''
✨ *PAGE 8* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''GIDAN ALHAJI UBAID.
RAYHAN: Wannan shine dalilin dayasa nace zanjirashi kuma na yarda zan aureshi da mata Salma.
Rayhan ce tabaiwa Salma labarin komai dangane da soyayyarsu da Fayz.
Ruwa Salma tasha cikin nutsuwa SALMA: Tabbas na fahimceki.
Amman Shiga Gidan Fayz a wannan Yanayin bashine lokacin daya dace ba Rayhan.
Keda bakinki kinfadamin kince Bayason Batama Matarsa rai.
RAYHAN: Ehh amman baya sonta Salma, Ya yarda ya aureta ne kawai saboda Mahaifinsa.
SALMA: Hmmm Lallai kuwa Bayasonta Injiwa ya fada miki haka?
Koshine ya fada miki yace bayason matarsa?
Shiru Rayhan tayi
RAYHAN: bai fadamin amman inada tabbacin Fayz nini kadai yakeso a zuciyarsa.
SALMA: Rayhan Da dai ba haka kikeba amman yanzu bansani ba ko Sone ya rufe miki ido yasa bakya ganin komai?
Rayhan yauda gobe tafi karfin wasa...
Rayhan kinmanta dayaya kuka fara soyayya dashine wai?
Kinmanta irin rashin mutuncin da kikayi masa?
Rayhan babu kalar rashin mutunchi da kuma kalmomin marasa dadi da baki kira Fayz ba lokacin dayace yana sonki.
Shin kinkula da yaushe kika fara Sonsa?
Daga tausayi!
Rayhan idan kinmanta barina tina miki kinfara son Fayz ne daga lokacin da kika fara tausayinsa akan duk abinda kike masa.
Kingano laifi kike aikata masa hakan yasa bakiji dadi ba kika fara sakar masa fuska a karshe kika nemi yafiyarsa kika karbi soyayyar sa.
Kuma daga baya kikazo kina masa irin sonda koshi baiyi miki ba a baya.
Hmm Rayhan kenan, Gaba daya bakiyi Shekara kina wulakanta Fayz ba amman kikaji tausayinsa saboda ba halinki bane.
Tokiyi tinanin akanshi da matarsa da kullun suke kwana tare suke tashi.
Ta kyautata masa yau ta kyautata masa gobe ta kyautata masa a koda yaushe kumashi kice baya sonta.
Shin bakya ganin wata rana zaiji abinda yakeyi ba daidai bane ya fara tausayinta.
Daga nan yazo ya fara son nata kuma yazo yaki aurenki?
Kawai Tinani zakiyi fa abune na tinani Rayhan.
Abinda yasa nakawo miki wannan misalin saboda shine misalin dayafi dacewa kuma shine misalin da zakifi fahimtarsa cikin sauqi.
Domin dake ya faru.
Rayhan shiru tayi domin kuwa taga a cikin maganganun Salma lallai akwai abin dubawa.
Dogon Numfashi taja.
RAYHAN: Gaskia Salma Zuwanki yayimin Amfani sosai ba kadan ba.
Domin kuwa yanzu ne kaina ya kara budewa wani lissafin ya kara shigomin.
SALMA: Amman fa bance miki baya sonki ba Rayhan.
Kuma wannan hangen nesa ne kawai tana iya yuwuwa kuma tana iya yuwuwa yaki faruwa just an imagination.
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
General FictionLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.