AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 3'''
✨ *PAGE 10* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
GIDAN ALHAJI SAMINU.
AUNTY HAFSAT: Aida Bakizo ba Farhan tinda rashin lafiyan ba tsanani yayi ba.
FARHAN: Ai Aunty idanba zuwa nayi naga jikinnasa ba hankali nane bazai kwanta ba.
AUNTY HAFSAT: Hakane hankalinki bazai kwanta ba. Amman yanzu ya kwanta don Doctor Ashir Yazo ya dubashi.
Yawan Ayyukane suka masa yawa kuma kinsan Alhaji bayason Hutu.
FARHAN: Allah Sarki Daddy.
AUNTY HAFSAT: Babu abinda zai sameshi Farhan donma ya sami bacci ai da kinshiga kin dubashi.
FARHAN: Babu damuwa Aunty Ina nan harya tashi dama Da Mukazo Da Syed ne yakeso sugaisa.
Amman idan yazo daukana sa gaisa ma.
AUNTY HAFSAT: Thom babu damuwa ya yake kuwa mijinnaki?
FARHAN: Yana Lafia Aunty, Kinsan yana aikin Wannan Estate dinne shiyasa gaba daya shima baya zama.
AUNTY HAFSAT: Ehh Haka Alhaji ya fadamin Allah ya bada Sa'a.
FARHAN: Amin Amin Aunty.
Ina Moh yake kuwa banganshi a gida ba Daddy yana kwance.AUNTY HAFSAT: Ai Baimasan jikinnasa ya tashi ba. Don saidama ya fita tukuna.
Kuma banason daga masa hankali shiyasa ban kirashi a waya ba.
FARHAN: Ehh Hakane.
SABON GIDAN SU DAIBAT.
MOH: Wannan Shine gida wanda zaku zauna a ciki saboda waccen Unguwar tayi hayaniya da yawa Umma.
UMMA: Amman Mohammad wannan ai babban gidane, Sannan Me mutane zasuyi tinani ace mun mallaki irin wannan katafaren gida haka.
MOH: Wato Umma idanka biye ta mutane babu abinda zaka cinma a rayuwa.
Kuma su Mutane Umma kome kayi a duniya sai sunyi magana akai.
To gwara karka kalli abinda zasuce kayi abinda yake gabanka kuma ya dace.
Umma koda banbaku wannan gida ba haka zanyita ajiyarsa karshe na barshi ya lalace kona saidashi donni bana bada gida haya.
UMMA: Hakane Mohammad Amman dai da an duba koda wanda baikai wannan din bane,
Tinda munfi sabawa da karamin dai...
MOH: Umma Banida Karamin gida duka gidajen da Allah ya bani manyane wasuma sunfi wannan.
Karku damu babu wani abu kuma nima baku takuramin ba.
DAIBAT: Baka sanmu ba baka taba sanin labarin muba amman kayi mana irin wannan Halaccin.
Babu irin kalaman da zamuyi amfani dasu da zasu gamsar damu wajen gode maka.
Tabbas kanada mutunci kwarai da gaske.
MOH: Daibat Bansan ko a haka kika kalli abin ba.
Amman maganar gaskia shine bantaba samin kaina a irin wannan yanayin ba.
Ina nufin kune mutane na farko dana fara irin wannan taimakon a kanku.
A wajena ba mutunchi bane kawai wata sabuwar Dabi'a ce a tattare dani wadda nima bansan yaushene ta shigeni ba.
Bazan Boye Miki Yadda kike tinanin haka nake toba haka nake ba.
Tashi MOH yayi tsaye.
DAIBAT: Duk Mutanen Arziki haka suke cewa, Saboda haka kai mutumin kirki ne.

YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Ficção GeralLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.