AHALI GUDA PART 4 PAGE 5

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 5* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

WASHE GARI.

GIDAN CHAIRMAN SYED.

Tashi yayi daga bacci yaga baiga Farhan ba.

Zunbur ya mike daga kan gado, dube dube ya duba ko ina baisameta ba.

Ya tabbatar da cewar tatafi gidane saboda rashin fahimtarsu ta jiya.

Zama yayi zuciyarsa babu dadi kwata kwata

SYED: Meyasa Farhan meyasa bakya fahimtata ne?

GIDAN SU DAIBAT.

DAIBAT: Kamar yadda na sanar dakai a baya kayi hakuri banajin amsata zata sauya daga yadda nake.

MOH: Yanzu daibat bazaki hakura ba?
Yanzu dukda kasancewar na baki lokaci still bazaki amsheni ba?

Kinaji niba mutum ne wanda yakeda takura akan abuba.

Amman wallahi Tallahi tinda kikaga nace zan dawo yau kuma na dawo wallahi da gaske nake ina kaunarki.

Wannan har zuciyata ta yarda dashi.

Bantaba fadama kowace mace ina kaunarta ba kai tsaye amman ke na fada miki.

DAIBAT: Bansan meyasa lokaci daya ka sauya ba, amman kayi hakuri bayan abinda ya faru tsakanina da kai wancen lokacin.

Wallahi saida nayi tinani na kara tabbatar da cewar kanada gaskia a duk kalamanka.

Yanzu mubar wannan maganar dan Allah.

Moh shiru yayi yana kallan Daibat.

MOH: Wannan shine karo na farko danakejin wani abu dana farajin zuciyata namin kuna saboda mace.

Wannan shine karo na farko da mace tayi rejecting dina kuma dukda hakan ban daina sonta ba.

Allah kenan, nikuma tawa Jarabawar akan soyayya ce.

Daibat bariki na fada miki, Wallahi bazan daina sonki ba kisani a shirye nake da duk wani abuda zakimin amman wallahi bazan daina zuwa wajenki ba.

Kuma saina mallakeki saidai idan sonkine zaiyi ajalina.

DAIBAT: Subhanallahi! Bana fatan ace yau wani ya fadi ya mutu saboda ni kuma Inn Shaa Allah baza'a taba samu ba.

Ballan tana kaida kayimana abubuwa wanda bazamu taba mantawa ba.

Dan Allah kayi hakuri wallahi banayi don bata maka ranka bane.

Cikin wani yanayi Moh ya tashi tsaye.

Zandawo gareki Daibat kisake tinani amman kisani ina kaunarki.

Fitowa yayi daga farlon ya bude kofar waje ya fita.

Daibat dafe kanta tayi cikin damuwa.

DAIBAT: Allah ya yake maka sona Mohammad.

Abinda kawai ta fadi kenan.

KAMFANIN ALHAJI SALEH.

Mahmoud ne Zaune kan kujera suna magana da Syed.

MAHMOUD: Yanzu kai kaje wajennata?

SYED: Banje ba Mahmoud... lamarin Farhan fa sai itadin don nagaji.

Kullun akan abu daya haryanzu takasa yarda cewar ita nakeso ita na aura.

Kullun itadai batason ganina tareda Rayheelah nina rasa laifin me Rayheelah tayima Farhan.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now