AHALI GUDA PART 4 PAGE 7

1 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 7* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

GIDAN DR SUDAIS.

ANTAFI LABARI.

SHEKARU UKU DATA WUCE.

ASIBITIN DR SUDAIS.

KARIMA: Nazone domin ayimin wani aiki Doctor.

DR SUDAIS: Thom mene aiki? Kuma suwaye wakilanki domin ayi miki aikin?

KARIMA: Doctor banida wasu wakilai.
Doctor ni Ba 'yar garinnan bace kuma nazo garinnan karatu ne.

Hawayene suka zubo daga idanuwan Karima.

DR. SUDAIS: Meyafaru meyasa kike kuka?

KARIMA: Bansan tayaya zaka fahimci abinda zan fada maka ba...

DR. SUDAIS: Karki damu kisanar dani matsalarki don ragema majinyaci radadi likita yake saboda haka fadamin mene matsalarki.

KARIMA: wasu bata garine sukayimin fyade Doctor!!!

Cikin fashewa da kuka Karima ta fadi haka.

DR. SUDAIS: Subhanallahi! Garin yaya haka ta faru?

KARIMA: Ana Birthday din wata kawata ne munje nida kawaye na suka bamu abinsha nasha duka suka bugar damu.

Sukayi amfani dani da qawata.

DR. SUDAIS: Amman tin a lokacin meyasa baki shigar da kara ba wajen ganin an bimiki haqqinki?

KARIMA: Ni dalibace Doctor, idan case yaje wajen 'yan sanda a matsayina na daliba hakan zai taba karatuna sannan bansan taya zan kalli iyayena ba.

DR. SUDAIS: Dukda haka ai kaddara ne kuma iyayenki zasu fahimceki Baiwar Allah.

Da kinsanar dasu da ankamosu suma an hukuntasu daidai da abinda suka aikata miki.

KARIMA: Hakane amman tsoro naji Doctor.

DR. SUDAIS: Yanzu wane taimako zan iyayi miki?

KARIMA: Bayan kwanaki Nagano inada juna biyu, Qawayena sunbani shawara akan a zubarmin dashi naki yadda.

Yanzu kuma anyi hutu zankoma gida kuma bazan iya tinkarar iyayena da wannan cikin ba Doctor.

Domin dama babu irin maganganun da ba'ayi ba kafin barina nayi karatu a garinnan.

Dan Allah Doctor ka taimakeni ka zubarmin da cikinnan.

Dan Allah Doctor.

DR. SUDAIS: Subhanallahi! Wani laifin kuma kikeso na aikata miki bayan wanda aka aikata miki?

Ehm baiwar Allah mene sunanki?

KARIMA: Sunana Karimatu.

DR. SUDAIS: Karimatu kiyi hakuri Bana zubar da ciki a Asibiti na, Asibiti na, na iya bada magunguna ne da haihuwa operation da sauransu.

Banyi miki Adalchi ba ace na zubar miki da ciki sannan kuma sabon Allah ne yin hakan haka kuma cin Amanar Aiki nane.

KARIMA: Dan Allah Doctor kataimakamin da kuma halin da zanshiga.

Wallahi bazan iya zuwa gida da wannan abinba a jikina iyayena kasheni zasuyi wallahi.

DR. SUDAIS: Indai Akan wannan ne nikibarmin komai a hannuna zan iya miki Alfarma muje dake har garin naku kuma nayima iyayenki bayani da kuma halin da kike ciki.

Zasu fahimta amman zubar da ciki ba shine mafita ba Karima zaki iya samin matsala nima kuma ta bangare na ba aikina bane domin bantabayi ba kuma ina tsoron Allah ya kamani da laifin kisa.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now