AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 2'''
✨ *PAGE 13* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''GIDAN ALHAJI SALEH.
Syed ne tareda Mahmoud saikuma Alhaji Saleh a zaune.
Syed zuciyarsa kamar ta fashe domin ba kananun kudi Nasir ya gudu dasu ba.
Alhaji ne zaune ya rasa ta cewa.
Mahmoud ne yake waya.
MAHMOUD: Okay, Thank You Detective Habu.
Kashe wayar yayi sannan yace Ba'a sami Nasir ba ya daina amfani da layinsa.
Ya ajiye motarsa, Mai Gadi yace yaganshi shida wata farar yarinya dazun da zaibar gida.
SYED: this is really heartbreaking, why Nasir why meyasa? Me kamfani yayi maka mezakayi da wannan kudin haka masu yawa.
this isn't you Nasir Come back.
ALHAJI SALEH: Banso kukai maganar ga 'yan sanda ba, naso mu bunne wannan maganar duka anan gida tare daku.
Sata ba halin Nasir bace, kunsani nasani.
Yarinyar da take tare dashi ce tasashi wannan ko tantama babu.In this case banaso duka wadanda sukeda hannun jari a wannan aiki susan abinda yake faruwa.
SYED: amman Abbah dukiyoyinsu ne a ciki yazamuyi idan sukaga tsayawar aiki?
ALHAJI SALEH: Aikinku bazai tsaya ba Syed. Wannan aiki za'aci gaba dashi kajiko.
Sannan wani abu da baka fahimta ba shine sanar da wadannan Masu hannun jari tamkar daukar wukane ka dabama kanka da kanka da kuma kamfani.
Dalili shine na farko Zakaja Darajar kamfaninmu tayi kasa.
Zakaja A daina yadda da duk wani abu daya shafi ANSARI GLOBAL RESOURCES.
Zakaja Mutuncinmu da kimarmu da komai da muke takama dashi Al'umma ta takeshi.
Mutanen nan akan kudinsu babu ahinda baza sumuku ba.
Sannan duka martabarmu da komai zata tabu, gwamnati bazata goyi bayan kuba karku kalli kamfanina ne.
Yanzu rijistar takace nakane.
Abinda nakeso da kai shine ka kwantar da hankalinka ka nutsu.
A abinda narasa daga fara kasuwancina zuwa yanzu wannan ba komai bane.
Kasani akwai kamfanunuwan daka hana wannan kwangila baka ganin bazasu fito su taya sauran kamfanunuwa yaki akan haqqin suba?
Domin haushi da rasa wannan kwangila, kasani fa wannan aiki ne da idan angama yana dauke da duk wata martaba kima da daraja a duniya baki daya ba iya wannan kasar ba.
Haka idan aka sami akasi, martabar kamfanin da suke kan wannan aiki ce za'a jata a kasa karshema kamfanin ya salwanta.
Saboda basussukan Mutane.
Abinda nakeso dakai ka kwantar da hankalinka domin ta hanyar kwantar da hankalinka ne kadai zaka fahimci abinda zanyi yanzu.
Shin nawane gaba daya kudin?
SYED: Dari Takwas ne Abbah sai Dari biyu da Kamfanin Alhaji Sani suka tura mana dazu da muka zauna dasu.
ALHAJI SALEH: Tayaya kuka shirya zaku biya kamfanunuwa wannan kudade?
SYED: Bamukaiga wannan tinanin ba Abbah, amman koma yaya ne zan bada duk wani abudana mallaka ne don ganin anbasu kudadensu kawai.
ALHAJI SALEH: Duk bazata kaiga wannan matakin ba.

YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Ficción GeneralLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.