*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 2'''
✨ *PAGE 3* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''GIDAN LOBBY.
RAY: Zanje yanzu ki saurareni kinjiko?
Zanje zan hadu da Alex din Ray ta fadi cikin Tashin hankali.
LOBBY: Okay Madam, Lobby ta fada cikin biyayya.
Ray ce tafito cikin sauri tashiga Motarta.
KAMFANIN ALHAJI SALEH.
Mahmoud ne shida Syed zaune suna tattaunawa akan kasuwancin su.
MAHMOUD: Shin yaya akayi dasu ne wai muntura musu da takarda akan sukawo mana takardar shaida amman sunki haryanzu.
Mahmoud ya fadi cikin rauni.
SYED: Kaga Mahmoud nidai bansan tayaya ma Logo dinmu ya fita ba.
Sannan bansan dawa suka zauna a kamfani sukayi magana ba.
Amman kabari zamunemi zama dasu dai.
MAHMOUD: Gaskia dai don wannan ba kananun kudi bane Syed ya kamata ace munkara lura munkuma sa ido.
SYED: Gaskia ne In Shaa Allah hakan za'ayi.
GIDAN ALHAJI SALEH.
Alhaji Saleh ne shida Alhaji Saminu suna Shan Fruits suna magana.
ALHAJI SAMINU: To ai Alhaji Saleh duka abin da za'ayi kaine zaka tsara.
ALHAJI SALEH: Aa Alhaji Saminu bazaiyu ace komai nine zance ayi ba.
Kaimafa kanada Alhaki a wannan Alaqa kuma kaima yarinyar nan 'yarkace.
Fiye da komai muda muke nema mune ya kamata ace muna tambayar komai bawai muzartar da hukunci ba.
ALHAJI SAMINU: To ai Alhaji Saleh gani nayi Farhan kaima 'yar kace kuma duka wani abudaka yanke a kanta daidai ne.
Koda ace ba Syed zata aura ba kaine zaka aurar da ita Alhaji Saleh.
ALHAJI SALEH: Hakane, Toshikenan Nagode da wannan Matsayi daka bani Alhaji Saminu.
Ina ganin a daura din a babban Masallacin zaifi tinda kaga akwai mutanena da zasuzo daga Kasar waje.
Sannan kaga Mai Girma Shugaban Kasa zai halarta.
ALHAJI SAMINU: Gaskia ne.
ALHAJI SALEH: wannan shine dalilin dayasa nakeso naji ta bakinka.
Kasan ita shawara tanada dadi.
Kuma mai shawara baya dana sani.
Amm wannan kuma katin Senator Abdulhadi ne da kuma Gwamnan Jihar Gurun.
Inaso zanje da kaina duka na kai musu saboda kasan bazaiyu nayi musu aike ba.
ALHAJI SAMINU: Hakane Gaskia, sannan kuma kaga dama Senator Abdulhadi mutumin kane sosai.
Kunkuma dade baku hadu ba,
ALHAJI SALEH: Gaskia ne to ai kaga shima kafin zabe ya shiga rububi kuma sannan akazo akayi zabe.
Haryanzu ko Allah ya sanya Alkhairy bansamu nayi masa ba.
Nima Abubuwan nawane sunada yawa. Sannan shigashi mutum ne mai son hira.
ALHAJI SAMINU: Gaskia ne, da kanka ya kamata kaje saboda hirarku dashi tanada yawa.
ALHAJI SALEH: Zansamu naje.
![](https://img.wattpad.com/cover/354890165-288-k167984.jpg)
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Ficción GeneralLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.