AHALI GUDA PART 4 PAGE 1

2 0 0
                                    

AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART 4'''

✨ *PAGE 1* ✨

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

AL'AMURA SUNFARU BAYAN RIKICE RIKICEN DA AKA SHIGA. AN DAURA AUREN DR. SUDAIS DA RAYHAN. NASIR YA KOMA BAKIN AIKIN SA KAMAR YADDA YAKE A BAYA. RAYHEELAH TA CIGABA DA RAYUWARTA A GIDANSU. ALEX YACI GABA DA SHIRYA TUGGU WA RAYHEELAH AKAN LALLAI SAITA AURESHI.

BAYAN SATI BIYU.

GIDAN DR. SUDAIS.

Wani Hamshakin Gidane nagani na fada. Gidane mai Asalin kyau da daukar hankali.

Tin daga cikin gidan har waje babu wata makusa komai sai Godiyar Allah.

RAYHAN: Yanzu shikenan tafiya zakayi kabarni?

DR. SUDAIS: Hmm Rayhan kenan tsawon sati biyu fa ina tare dake a cikin gidan nan.

Cen kuma marasa lafia sunata jirana.

RAYHAN: Dukda Haka ai ni bangaji da ganinka ba, yanzu idan kafita kabarni nini kadai mezanyi a gidan?

DR. SUDAIS: Karki damu ai bazan jima ba kuma Salma tacemin yau zatazo donma Safiya ne yanzu shiyasa amman da tini tazo.

RAYHAN: Nima tacemin zatazo, Babu damuwa Allah ya kiyayemin kai ya tsaremin kai.

DR. SUDAIS: Amin Amin Matar Mijinta.

Rayhan Murmushi ta watsa masa mai shiga rai sannan ya shiga motarsa ya kunna domin tafiya.

Bye Bye tayi masa da hannun kafin mai gadi ya kulle gate din. Ita kuma tashiga ciki.

GIDAN ALHAJI SALEH.

MAHMOUD: To ai duka wadan nan sunyi Khairyya Wanne kikeso ayi fadamin?

KHAIRYYA: Ni Wannan Golden din nakeso muyi Ya Mahmoud yafi kyau.

MAHMOUD: Shikenan shi za'ayi Khairyya ni zabinki shine nawa kinjiko.

Khairyya Murmusawa tayi Gefenta Namrah ce.

NAMRAH: Ya Mahmoud ai wannan bikin naku sai an dade a garin nan ba'ayi mai kyaun saba.

MAHMOUD: A ah Fa Namrah kin manta bikin Syed ne?

NAMRAH: To ai ko bikinsu Ya Syed din ankwana biyu yanzu naku sai yafi nasu.

Kuma naku anyi modernizing abubuwa.

KHAIRYYA: Ko Iya Outfit ma ba iri daya bane.

MAHMOUD: Hmm Kunga ni kun isheni da wasu Outfit dama dai abinda zaki nunamin kenan ko?

KHAIRYYA: Ehh shikenan abinda zan nuna maka saikuma ganinka da nakeso nayi

Kuma na ganka.

MAHMOUD: Hmm Thom Kin kyauta yanzu zan koma Office kafin Syed ya fara kirana donnabar masa ayyuka a gabansa.

KHAIRYYA: Thom Muje na rakaka wajen Motar.

Tashi sukayi sukafito suna hirarsu har suka karaso wajen mota.

KHAIRYYA: Thom Saika dawo Ya Mahmoud Allah ya kiyaye.

MAHMOUD: Amin Khairyya ta kikulamin da kanki.

KHAIRYYA: kaima ka kulamin da kanka Ya Mahmoud.

Fita yayi da motarsa ya nufi Office dinsa.

GIDAN SU DAIBAT.

WASILA: Yaufa Kusan Sati Biyu kenan rabonsa da zuwa.

UMMA: Kodai munyi masa wani laifi ne?

WASILA: babu wani laifi da mukayi masa Umma.

Kawai nafi tinanin ayyukane suka masa yawa fa.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now