AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*'''PART 4'''
✨ *PAGE 12* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
PRIVATE HOSPITAL.
Moh ne tareda Ahalinsa a cikin daki kowa zuciyarsa babu dadi.
Daibat ce a kansa gefen gadonsa.
Inda yana farkawa itace ya fara gani.Yinkurin mikewa yakeyi ta dakatar dashi daga tashi.
DAIBAT: Karka tashi... ka koma ka kwanta, fuskarta cikeda damuwa ga idanuwanta sunyi jajawur tasha uban kuka.
Moh dinma wani hawayene ya kara fitowa daga idonsa.
MOH: Haryanzu Bakya sona ko?
Haryanzu bakimanta da abinda nayi miki ba...Zayyan matsowa yayi kusa dashi cikin murmushi.
ZAYYAN: Daibat tana sonka Moh, Tabbas tana sonka. Kuma Daibat zata aureka.
Moh kallan Daibat din yayi cikin wani yanayi inda ta girgida kanta alamun ehh hakane abinda Zayyan ya fadi.
MOH: Kifadamin Gaskia gaskia da bakinki Daibat shin gaskia ne abinda Zayyan yake fadi?
Kin amince dani a matsayin wanda kikeso kuma zaki aura?
Goge hawayen fuskarta takeyi da jan numfashi cikin tausayin Moh din.
DAIBAT: Ina kaunarka Mohammad, ina matukar kaunarka.
Daibat ta fadi cikin damuwa da rashinjin dadi a zuciyarta kasancewar duk itace silar kwanciyarsa a Asibiti.
Moh yinkurin tashi yake inda yake murmushi dukda cewar akwai hawaye a fuskarsa.
ZAYYAN: A a kada katashi baka gamajin sauqi ba Moh.
MOH: A a Zayyan Nasami sauqi ai, Nasami Magani. Daibat ce maganina.
Wallahi nasami sauqi banajin ciwon komai yanzu.
Daibat din kallonsa takeyi a yanayi na shagwaba da hawayenta.
DAIBAT: Bakaji sauqi ba Dan Allah ka kwanta Banason wani abu ya sameka.
ZAYYAN: Ka kwanta Dan Allah barina sanarwa da Likita cewar kaji tashi.
Zayyan bude kofa yayi ya fita.
Moh kwance yake inda suka hada ido da Daibat suna kallon kwayar idon juna.
MOH: Wallahi Ina sonki Daibat, Ina matukar kaunarki, Daibat ina rasaki mutuwa zanyi kinga alama tinyanzu.
DAIBAT: Kadaina fadin haka Dan Allah zuciyata zafi takemin.
MOH: Dole na fadi haka, Domin bantajin son wata mace a rainaba saiyanzu kuma akanki.
Bantaba sanin ya akeji ba a soyayya saiyanzu kuma akanki.
Sannan bantaba shiga irin wannan halinba saiyanzu kuma akanki.
Wannan kadai ya isa hujja kiyadda da cewar ina matukar kaunarki.
DAIBAT: Nasani Mohammad, nasani cewar kana sona, Nima inaso kasani cewar ina sonka fiye da yadda kake sona.
Duka abinda nayi maka nayi makane don kawai ka fuskanci mene soyayya.
Domin ka dauketa da gaske Amman wallahi bantabaji na daina sonka ba.
Moh da yake kwancene ya rike hannun Daibat da cewa nagane kuskurena.
Dan Allah zaki aure?
DAIBAT: Baka bukatar Amsata, Indai zaka iya zama dani a matsayin matar aure...
Ta fadi cike da murmushi da hawayenta.
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
General FictionLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.