AHALI GUDA PART 1 PAGE 3

6 0 0
                                    

*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART ONE'''

*PAGE 3️⃣*

_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾

'''GIDAN ALHAJI SAMINU.

Karbar Wayar Farhan tayi ta tashi tashiga cikin gidansu don zata faffadawa Ray maganganu.

Syed cewa yakeyi
SYED: mene hakane Farha...

Amman ko sauraronsa batayi ba ta shige cikin gidansu.

SYED: Kallon Mahmoud yayi da cewa mutafi

MAHMOUD: wayannaka fa?

SYED: Barshi kawai muje Mahmoud. Inji Syed.

Tashi sukayi suka fito suka shiga Mota, Muje gidansu Ray Syed ya fada.

Mahmoud din kuwa cikin Mamaki
MAHMOUD: yace amman kacema Farhan bazaka kara zuwa wajenta ba ai ko?

SYED: Yanzu kuma nace Muje Mahmoud baka ganin takirani a waya ita kuma ta karba nasan mezatace mata?

Ba gwara naje na bata hakuri ba!

MAHMOUD: Hakane amman meyasa Farhan take hakane wai?

SYED: Wallahi Mahmoud rashin kwantar da hankalinta akan irin wadannan abubuwan shine yake matukar bani mamaki.

Saboda na fada mata cewar babu wani abu tsakanina da Rayheelah.
Kaima kuma kasani.

But still tana ganin kaman boye mata nakeyi.

Nifa na fara tsoron auren nan Mahmoud.

MAHMOUD: Haba, Yazakace haka..
Itafa duk wannan abinda takeyi don kaine takeyi.

Saboda kuma tana sonka ne takeyi. Kuma zata daina kawai haka Allah yayita ne.

Syed girgida kansa yayi sannan yace SYED: Muje gidansu Rayheelah.

GIDAN ALHAJI SANI MALIYA.

Alhaji Sani Maliya Attajirin mai kudi ne.

Yakan fita kasar Wajene domin kasuwancinsa.

Alhaji Sani Maliya yanada Dansa guda daya tilo da kuma matarsa sai sauran 'ya'ya da yake rikewa 'ya'yan 'yan uwansa.

Sunan Dansa Fayz ya kasance shine ke rike da duk wata dukiya da mahaifinsa ke juyawa.

Fayz yanada matukar hankali, Ilimi da sanin ya kamata.

Fayz bai taba batama mahaifinsa rai ba domin yana matukar kaunar mahaifinsa kuma baya taba musu dashi akan komai.

Fayz ne shida Amininsa Abbas suna tattaunawa akan kasuwancinsu.

ABBAS: Toyanzu kayan sunzo ko basuzo ba?

FAYZ: Haba Abbas tinjiya nake sanar dakai cewar kaya suna hanya kuma zasuzo yau ko gobe.

ABBAS: To ai gani nayi ya kamata ace sunkaraso domin kayannan fa yau kwanansu hudu a hanya.

FAYZ: Amman Abbas ai kayanmu suntaba sati a hanya kokuwa dondai kwana hudu kawai ina ganin ai mujira kawai.

Fayz na magana wayarsace ke ringing inda Abbas yaga An rubuta My Wife.

Fayz din cikin Murmushi ya daga wayar tasa da cewa
FAYZ: Hello Matata Abin Alfahari na.

RAYHAN: "Bawani nan Kullun saika barni cikin kewanka da tina ninka sannan kadingamin dadin baki."

FAYZ: Ba haka bane Rankishidade nima a koda yaushe kina raina babu wani abuda nakeyi batare da kinfadomin ba.

RAYHAN: "To kacemin zakazo bakazo ba, kuma ni inaso na ganka"

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now