AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 2'''
✨ *PAGE 12* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
'''SECRET PLACE.
(BOYAYYEN WAJE).RAY: Dpo Alex suppose to be arrested by now then.
DPO SHAGARI: Amm! Ray the reason why i called you is for you to listen and understand me.
Bayan barin wajen lobby a Asibiti naje wajen yaran da muka kama.
Bayan sun daku a wajenmu sun tabbatarmin da cewar kudi wani yabasu domin su amsa cewar sune sukayima lobby haka.
An basu 1million each akan su amsa cewar sune sukayi mata haka kuma suce saurayin tane tare da abokansa.
Kinga yayin hakan sunan Alex ya fita daga suspect sannan case din ya sauya akan cewar sunada alaqa da juna dana Christina.
A takaice dai yanzu Christina na wajen Alex kuma domin goge hujja shine ya tura a kashe Lobby saboda tasan komai alaqarsa da Christina kuma zata iya tonawa.
Ray girgida kanta tayi sannan tace
RAY: Nasani nasani Dpo nasan cewar Alex yanada hannu a duka wannan.This is the reason why i don't like him, i hate him he's too dangerous.
Dpo Christina tanada cikin Alex a tattare da ita.
Alex yaso a zubda cikin amman christina taqi domin bataso.
Alex ya bata kudade domin ta yarda amman taki karba tace ita shi takeso ya aureta.
Alex bayason Christina he used her then dumped her hakan yasa ya saceta tana raye kota mutu only him knows that.
Nasami duka wasu bayanai a wajen lobby hakan yasa na tinkari Alex da maganar.
Duk yadda akayi bayan ya gano Lobby ce ta sanar dani hakan yasa akayi mata wannan abin.
And i have all the evidences Dpo.
Magunguna da komai da Alex ya siyo domin Christina tasha ta zubda cikinta.
Dpo wannan ya isa duka a kama Alex.
DPO SHAGARI: We don't have to rush Ray, Mubi komai a tsakanake.
Kitina waye Alex kitina Dan waye Alex, Ga Mommy ki wannan case ba karami bane.
Ray inaso nakama Alex tareda taimakonki dakuma hada dukkanin wasu hujjoji dangane da wannan case.
Wannan rubutu ne na Lobby da tayi akansa.
Sannan Duka wasu bayanai na nadesu, abinda za'ayi yanzu i need all the evidences you have.
Saida taimakonki Lobby zata sami adalchi sannan saida taimakonki Christina zata dawo.
Haka saida taimakonki Alex zai shiga hannu zan fada miki yadda za'ayi.
DA DADDARE.
GIDAN CHAIRMAN FAYZ.
Fayz ne ya shigo cikin farlonsa.
Najma ce zaune ita kadai sai kamshi takeyi abinta.Kamar kullun tasowa tayi domin tarbar mijinta
NAJMA: Sannu da zuwa Mijina Najma ta fada.FAYZ: Hmm yauwa sannunki Matata, nasameki lafia? Ina fatan kina cikin koshin lafia?
NAJMA: Ina lafia lau Mijina Fadar Najma.
Karasowa sukayi Farlo Fayz ya zauna kan kujera.
Yauma ka gajiko? Nace kadaina aiki da yawa saboda banason kana wahala.
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
General FictionLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.