****************
"Du'bu da kan'ta ta sa'wa jaririyar suna JUWAIRIYA a take rumfar bayi ta hau shewa da murna, dan'yen dabino suka kwaso daga rumbu suka hau rabawa junan su cike da tsantsar farin ciki dan a ganin su tamkar wata babbar kyauta ce Allah ya kawo musu..
"A haka Rayuwa taci gaba da tafiya a inda jakadiya da hansai har ma da du'bu da laure suka ci gaba da kula da JUWAIRIYA dukkanin baiwar dake cikin rumfar bayi tana mutukar son'ta,a haka labari dai har yaje kunnen GIMBIYA KILISHI wato uwar gidan mai martaba kenan.
'Macece mai shegen son milki da kuma son a girgirmama ta,gata shu'unar mace dan kuwa gaba daya masarautar ta daura babu mahalukin da ake bawa girma kamar ta idan aka cire sarki Abdul-Jabbaru, yaran'su biyu kacal da mai martaba' akwai dan ta yarima JALALLUDEEN shine me jiran kujerar mulki wato heir apparent to the throne kenan, sai HAMZA kaninsa,ganin gimbiya kilishi ita kadai ce Allah ya bawa kyautar ya'ya maza a kaf duka matayen sarki idan ma an hada har da kwarkwarorinsa (concubines )'gimbiyata kilishi kawai ce bata da diya mace'
shiyasa rashin mutumcin nata ya kara girma sannan tsanar sabowar amaryar mai martaba ya shigeta sosai'
dan kuwa itama FULANI DIYYA wato amaryar mai martabar kenan daya auro daga masarautar bauchi tana di'ra ta santalo dan yaron ta namiji daya dilo wato TURAKI (ABDULLAH )sai diyarta ZAINABA.ita kam macece mai son jama'ar ta,indai har kina cikin rumfar ta toh fa lallai ne dole ki so ta dan tana mutukar kyautatawa na kasa da ita balle ga bayin ta,shiyasa kaf masarautar tafi dukkanin matar sarki farin jini da kuma karbowa a wajen Bayi..
****wannan kenan *****"Shekaru nata tafiya a inda yanzu JUWAIRIYA na da shekara goma da haihuwa.
'Yarinya ce mai karanbani sosai bata ji,sai dai tasan iyakarta,dan kuwa kullum zaka ganta tana guje gujenta a cikin rumfar bayi wanda hakan yake saka bayin dake ciki annashuwa.
ummanta wato hansai tana kokarin bata tarbiyya irin tasu ta bayi marassa ga'lihu,haka kuma kamilu na mutakar son JUWAIRIYA dan dama ya dade yana neman haihuwa Allah bai basa ba.
(kamilu da hansai bayin Allah ne da kaddara ta fado musu aka siyar dasu a matsayin bayi ga masarautar ta daura)"Tunda juwairiya ta ta'so bata taba ko da lekawa ne cikin masarautar ba dan kullum tana cikin rumfar bayi' gashi bata da abokin wasa dan duk bayin dake ciki da safiya tayi suke ficewa zuwa wajajen uwayen gidansu. .
Kamar kullum yau ma hansai ta gama shiryawarta dan tafiya wajen uwar dakinta wato GIMBIYA KILISHI,ta kalli juwairiya dake zaune ta kura mata idanuwanta masu haske,kamo hannun ta hansai tayi tace kici gaba da hakuri juwairiya kinji abbanki zai zo miki da halawa anjima,juwairiya ta saki dan murmushi sannan tace,umma muje na miki rakiya,hansai ta murmusa sannan ta kamo hannunta, suna kaiwa bakin kofa ta sake hannun juwairiya sannan ta shafa kanta kafin ta fice.
Hansai na tafiya juwairiya tayi saurin karasawa gaban babban kofar ta leka abunda bata taba yi ba kenan sbd gargadin da ummanta tayi mata..Ware ido tayi ganin jama'a da yawa nata zurga zurgar su ga wani haske da har kashe mata ido yakeyi ga kuma iska me dadi dake kadawa..
Da sauri ta karasa cikin dakinsu ta dauko mayafin ummanta,ta boye shi a cikin doguwar rigar dake jikinta .
A hankali ta karasa madafa waton inda ake shirya wa sarki abincinsa, ta leka nan ta tarar da bayin dake dahuwa suna ta aikinsu,ta juya da sauri ta lulluba mayafin a kanta sannan da gudu ta saka kafa ta fice daga rumfar bayi..**********
"Tafiya kawai takeyi tana kalle kalle sai washe baki takeyi dan bata taba ganin mutane masu yawa haka ba balle jinsin maza dan kuwa a rumfar bayi babu namiji a ciki.
"wani dan zomo ne ta hango fari dashi tas,ba karamin burgeta yayi ba,ta shiga binsa da gudu batayi aune ba taji tayi karo da mutum bum!
Da sauri taja da baya..."Baki da hankali ne?ina kika bar idanuwanki da har zaki taremin hanya ta!!
Taji an fada da wata murya me cike da isa da iko..
Dagowa tayi da sauri dan son ganin waye wannan me muryar..yake magana kamar yana kirga lafuzan sa.Caraf idanunsu suka sarke dana juna..
Wani dan saurayi ne da kalla zai kai shekara sha biyar..
Juwairiya ta kafe shi da ido dan tunda take bata taba ganin me kyau irin nasa ba,ahankali ta fara fahimtar irin kallon kyama da kaskancin da yakeyi mata..
hakan yasa ta shiga bin shigar shi da kallo..Sanye yake da kayan alfarma kayane masu tsada ga zinari ta ko ina sai kyalli yake..
Ta kalli yaron dake kusa dashi at least shi ze kai 11 years,shima din cikin kayan alfarma yake..Bakya jina?
Tayi saurin ja da baya kadan sannan tace,a tunani na mu biyune da laifin..
'tunda idan ni bani da ido ai kai kana dashi ba sai ka kauce min ba?
Cike da tsantsar mamaki suke kallonta..
Wacece ita da har zata ringa maida masa magana haka?Juyawa yayi cike da fusata..cikin daga murya yace,wai ina sarkin Lumbu ne! Sallama kana ina!
wayace musu su ringa barin ya'yan bayi masara galihu suna shigowa nan!Cikin sauri wani mutune yazo ya zube a gaban sa,Allah ya huci zuciyar YARIMA ayi min afuwa ayi min gafara!nayi laifi ka yafewa wannan bawan naka...
Wanda aka kira da Yarima ya yamutse fuska sannan ya kalli na gefensa,HAMZA me kake ganin zamuyi dasu?
Hamzan ya tabe baki,kawai mu kaita ga GIMBIYA tunda dai kowa ya sani BAYI basu da ikon shigowa cikin lumbun TAKAWA (wato sarki)..RANKA SHI dade ayi musu afuwa..
Sukaji an fada daga bayan su..'A tare duk suka juyo suna kallon shi..
Saurayi ne dan shekara 12 kyakkyawa ne sosai rike da hannun yar budurwa da bazata wuci sa'ar juwairiya ba..Yarima ya daure fuska, saboda me zaka neman musu gafara TURAKI?
Turaki yai murmushi sbd a tare muke da ita kulangar ZAINABA ce..
Hamza da yarima suka ja tsaki sannan suka zo zasu wuce ta gefen juwairiya ta dago suka hada ido da yarima ya banka mata harara, ta bi shi da kallon mamaki har ya fice yana jin zafin halayen ta a garesa ...."Da sauri juwairiya ta karasa wajensu turaki ta dukar da kai tace,na gode ranka shi dade..
Da kallo yabi fuskarta,daga ina kike?dan ban taba ganinki a cikin masarautar nan ba..
RUMFAR BAYI ta bashi amsa,ya jinjina kai,zainaba ta kalli yayanta,yaya turaki ina sonta!
Da sauri suka kalli zainaba cike da mamakin furucinta ..Turaki yace,zainaba ke da kika ki amincewa da kowacce baiwa?zainaba tayi murmushi sannan ta juya da gudu tayi tafiyarta..
Turaki ya juya ga juwairiya data bi bayan zainaba da kallo..Kiyi gaggawar komawa inda kika fito dan na lura ba ki gama fahimtar wasu dokokin masarautar nan ba,yana gama fadar haka yayi ficewarsa...
A sanyaye juwairiya ta koma cikin rumfar bayi gaba daya taji bata ma kwadayin sake fita dan kuwa duk mutanen da ke waje basu da mutumci ita kam zaman ta a Rumfar bayi yafi mata dadi inda kowa yake da same rights dinsa.......
Wannan kenan!

CZYTASZ
Rumfar bayi
HistoryczneA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid