*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction )
Na Afrah bhai
Page 23
Wattpad @afreey101_"@ Ayshat maghili,Admin TEAM RUMFAR BAYI group thanks for the effort love😚"_
*****************
"Khadija ta saki murmushi, ai abunda ma yafi albishir tazo min dashi..
Zainaba ta gyara zamanta,Allah ko?sannu yar lelen goggonta..
Khadija ta kwashe da dariya..
Kafin tace,wai ina Mustapha ne?kinsan dai da an gama mgnr bikin su ya turaki da hamza kanki za'a dawo ko?Zainaba ta lumfasa,nima damuwata kenan wlh,kuma gashi kinsan halin abba da shegen son auren hadin nan daya burgeni ko kadan..
Khadija ta dan zungureta,ni ai auren hadin ba karamin taimaka min yayi ba,ke kinsan in ba dan shi ba ai bazan taba samun ya jalal dina ba..Zainaba tace ke kenan,ni kin ganni nan ma kadaici duk ya ishe ni a cikin yan kwanankin nan, tun dauke min juwairiya da mijin ki yayi..
Khadija ta tabe baki..
Kema dai zainaba da rigima kike, kawai ki bari sai lkcn auren ki yayi sai ki zabe ta a matsayin kyautar ki daga wajen mai martaba..
Zainaba ta sa dariya,wlh kin kawo shawara kawata..
Suka saka dariya a tare..***************
"Umayma da kanta takai juwairiya har wajen surayya. .
Surayya ta kalle ta cike da kyamata tace..
Ki shirya zamu shiga madafa dake yanzu..
Juwairiya tadanyi mamaki amma ta share tace toh ranki ya dade .."Tunda suka shiga madafar suka soma aiki ba kama hannu yaro..
Surayya kam na hakimce akan kujera tana basu orders cike da isa..Har sun kusa kammala aikin juwairiya dake gefe ta jinjina kai ganin irin delicacies din da aka shiryawa yarima..
tana mamakin yarda mutum daya zai iya cinye duk wadannan abincin..
Abinci har kusan kala goma sha biyar?ina zai kaisu?
Aiko duk tsokali daya yayi a duka se cikinsa ya koshi..
Tadan tabe baki,ko dayake duk bajinta ce ake son a yi masa..Juyowar da zatayi kawai ta hango wata baiwa na barbada wani gari acikin tukunyar miya..
Da sauri ta karasa wajenta..
Baiwar tayi saurin kakkabe hannunta tana kallon juwairiya da kananun idanunta tace,lafiya?Juwairiya tace,me kika zuba acikin tukunyar nan yanzun nan?
Baiwar ta watsa mata harara tace,zargi kikeyi?toh babu abunda na zuba sai gishiri..tana gama fadin haka tayi gaba da sauri..Juwairiya taji gabanta ya fadi..
Meye ta zuba a abincin yarima?ta tambayi kanta..
Hankalinta ne yadan tashi dan ita kam bazata so a cuci yarima ba...
Umayma ce tazo tayi kiranta akan surayya tace su fara kai abincin can babban falon jalal..****************
Rabi ce ta shigo sashen khadija da gudun ta..
A daki ta tarar da khadija a zaune gefen gado..
Ta samu waje a kasa ta zauna tana lankwashe kafafunta tace..Albishirinki ranki ya dade?
Khadija ta saki murmushi bani in sha..
Rabi tace yanzun nan muka gama da mgn da wannan baiwar da muka saka aiki acikin bayin gimbiya surayya..Kuma Ta tabbatar da min cewa tayi yarda muka bukaci tayi...
Khadija ta kwashe da dariya cike da murna sosai..
Tace naji dadin albishir din nan sosai..
Dan Babu wacce zata samu yabawar jalal sai ni ni kadai kuma...
Su uwar gida manya,dole ne asha kunya da wulakanci ayau..Ta kalli rabi,Allah yasa dai ta zuba dan'tsamin nan dayawa acikin abincin dan bana so ko kadan girkin wannan matar yakai cikin cikin ya jalal dina..
Rabi tace kada ki damu ranki ya dade na tabbata tayi komai kamar yarda muka tsara..***************
"Su juwairiya sun gama jidar abincin zuwa sashen jalal..
An gana gyara falon tsab kamar za'ayi wata uwar liyafa..Kuyangi biyu akabari sai surayya data sha wata uwar kwalliya tana zaune gefe tana jiran fitowar yarima..
Kallon su juwairiya tayi,tace duk zaku iya tafiya..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid