*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 34
Wattpad @afreey101******************
"Ammi ce da kanta ta saka juwairiya a gaba suka ringa shiga bangare bangare na cikin masarautar dan gaisawa da matan mai martaba da kuma ya'yansa..
Daga karshe Ammi ta kaita wani tsohon sashe na mahaifiyar ta zarah'u ..
Hawaye ne suka shiga zuba daga idanuwanta..ba karamin tausayawa irin rayuwar da sukayi ita da mahaifiyar ta ba takeyi ba...
Kallon dakin takeyi cike da tausayin irin rayuwar da mahaifiyar tayi a baya..
Ammi ta dafa kafadarta,ki ci gaba da yi mata addu'a kinji?Juwairiya ta gyada kai sannan tayi wa ammi tambayar dake ta cin ta a rai tun jiya..ta saukar da kai kasa tace..
"Ammi yanzu shi sarki Abu-turab din har yanzu bai gano sharri akayiwa ummar ba?
Sannan har yanzu suna tare da matarsa hindu ne?Ammi ta kamo hannunta suka zauna a gefen gadon dake gefen su..
Ta kalli juwairiya tace, kin san indai mutum baya da hakkin wani...
Toh Allah sai ya san yarda yayi gaskiya ta fito koma daren dadewa..Wannan bafaden dai daya taimakawa zarah'u ta tsira daga hannun wadan nan mutane shine ya bayyanar da komai..
Duk da dai ba karamin wahala da azabtuwa yayi ba a wajen wadannan mutanen..
Sai da zarah'u tayi kusan sati daya da bacewa sannan Allah ya kubotar da wannan bawan..Kai tsaye yan farautan da suka taimake shi sukayi fadar sarki abu-turab dashi..
Shi kuwa ya fayyace wa sarki duk abunda ya faru da zarah'u sannan ya sanar masa da sa hannun HINDU aciki..
Abu-turab a take a rikice susuce..
Ya saka aje a kawo masa hindu da duk mutanen da suke da sa hannun aduk abubuwan da akayi wa zarah'u..
Hindu na jin asirinta ya tuno ba karamin rikice wa tayi ba..
sbd tashin hankali da kuma mugun hali irin nata sai sakawa tayi yayanta ya taimaka mata ta gudu daga masarautar gaba ki daya....Toh a cikin ikon Allah kwana biyu da guduwar ta ta sai gashi an kawo gawarta har cikin masarautar kano..
wai yan fashi ne suka tare su a hanyar su ta shiga kasar nijar suka kwashe musu duk kudin dake garesu sannan suka kashe su..Abu-turab bai amsa gawar hindu ba,yace aje can akai wa yan uwanta shi babu ruwan shi da ita tunda ya dade da sakinta..
Abu-turab ya saka mutane dayawa dan neman zarah'u hakama mu ma a nan amma shiru babu wani labari akanta....Mahaifiyar sa ce ta matsa masa akan sai ya sake wani auren..
Toh a lkcn mijin AMINA ya rasu sai mai martaba ya bashi ita,abu-turab bai wani musa ba aka daura musu aure bayan shekara daya kenan da batan zarah'u...
a halin yanzu kuwa har sun hayayyafa sannan kuma ya kara aure bayan ita,ya auri diyar sarkin AZARE JAMILA ....Juwairiya taja lumfashi lallai ta tausayawa iyayen nata..
Ammi tace,kada ki damu idan kika kara kwana biyu zamuje ki gansa kinji?
Juwairiya ta gyada kai..
Mikewa sukayi suka bar sashen..********
*Masarautar daura...*"Bakin ciki ne da takaici suka taro sukayi wa surayya yawa..
Ace wai a halin yanzu ko kallo bata ishi jalal ba?
Sai dai ta ringa samun labarai daga wajen umaymah wai a kullum sai ya gayyaci khadija zuwa sashensa sannan yaje ya dauke ta su riga fita yawon shan iska da yamma...Surayya ta dunkule hannu ta naushi gadon da take a kai..
"Dole ne na san abunyi dolene na tashi tsaye ta nemo wa kanta mafita....."Jalal ne zaune a kan gadonsa yana tunanin ko a wane hali juwairiya take ciki yanzu?ba karamin kewar ta yayi ba,kodai ya shirya ne yaje zazzau din..?

YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid