*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 21
Wattpad @afreey101_juma'at mubarak all may Allah forgive us our sins amin_
****************
"Washe gari""Juwairiya na gani a zaune ta buga uban tagumi,yanzu menene mafita a gareta?
Ta shiga kallon yarda bayi ke ta wani rawar jiki suna gyara jikinsu dan kawai su samu yarima ya zabe su a cikin sababbin masu mishi hidima asashen sa..
Ita kuwa ya zatayi yanzu?tasan da cewa indai har tana ganin shi a kullum toh zuciyarta bazata taba samun sukuni ba,gashi kuma abun haushin ma yasan konewar fuskarta duk karya ce..
Laure ce ta dafa kafadarta,a sanyaye ta dago ta kalleta,laure tace taso muje,juwairiya ta mike suka shige cikin dakin jakadiya..
Hansai ta kalle ta tace, haba yar umma wannan hade rai har haka?
Juwairiya ta turo baki..
Jakadiya tace,ki kwantar da hankalinki juwairiya,na tabbata mai martaba bazai dauke ki ba ma,hansai tace,ni fa mamakin ma wadancan yaran nake da suke ta rawar jiki..Laure tace ki kyele su duk so suke me martaba ya dauke su ko sunje su samu waje a can kinsan wasu da shegen kwadayin abun duniya suke...
Jakadiya ta girgiza kai,matsalar dai itace,duk lkcn da sarki ya ga wata baiwa daga cikin su kuma ya kyasa ta har ya kuma kwana da ita toh daga ranar zata zama SA'DAKARSA,wasu ma a haka suke karatar rayuwar su bai sake waiwayen su ba,masu rabon haihuwa kawai ne ba'a mantawa dasu a tarihi,toh wannan rayuwar har wani abun kwadayi ce?
Juwairiya dake sauraren jakadiya taji jikinta duk yayi sanyi ,wato dai ita baiwa ba zata taba samun damar zama mata kamar kowacce mace ba?sai dai amatsayin kwakwara?
Hayaniyar da sukaji ne daga waje yasa su duk mike duka,laure ta kalli juwairiya,
ki kwantar da hankalinki diyata,wannan tabon na fuskar ki kawai ya isa me martaba yaki zabar ki..
Juwairiya ta jinjina kai tana tausayin iyayen nata,
Wato su a nasu tunanin wannan tabon ne ze taimake ta?lallai da sun san da cewa jalal yasan komai da basu saka rai a kan shi ba.."Suna fitowa suka tarar da bayi duk an ja layi,
kowaccen su na ta addu'ar samun nasara dan aiki a sashen sarki kamar wani garin girma ne suka samu..
Du'bu ce tazo taja hannun juwairiya ta kai ta cikin layin itama..
****************
"A waje kuwa...Sarki jalal ne tare dasu shamaki dakuma wasu fadawan ana ta kwararo masa kirari..
"Zaune yake a wata kujerar alfarma ga kuma lema (umbrella) an rike masa yana shan iskan inuwa abunsa..
Fuskarshi a daure tamau sai shan kamshi yakeyi abu ga jinin sarakai...
A haka bayin suka ringa fitowa set by set.
duk wacce tayi masa kalar tsabta sai yayi wa shamaki kwatancen ta a kunne shi kuma shamakin yaje ya sanar wa uwar soro itake zuwa ta dauko su ta kai gefe...Set dinsu juwairiya ne zasu fita yanzu,gabanta nata faduwa,zuciyarta ta kasu kashi biyu.
Kallo daya zakayi mata ka fahimci a tsorace take sosai ..Fitowar ta yayi daidai da saukar da idanuwanta akan fuskar yarima..
Ji tayi duk karfin ta yana so ya kare..
Ta dauke kai da sauri taja kafarta taje ta tsaya akan layin.Shamaki ne ya dan duka wajen kunnen yarima yace..
Allah ya kara maka yawan rai ga wasu nan sun sake fitowa suma..
Jalal kamar bayaso ya dago da kansa..Caraf ya kyallo ta a cikin su..
Ya lumshe ido ya bude su ahankali,se yanzu ne yake jin dadin wannan selection din.
bai wani bata lkc ba ya sanar ma shamaki wacce yake so acikinsu..
Shamaki ba karamin mamaki yayi ba dan kuwa sai yarima ya dauki kusan minti sha biyar bai zaba ko daya ba, amma ji yanzu ko minti daya bai dauka ba ya zabo wancan..
![](https://img.wattpad.com/cover/192065469-288-k379718.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
Rumfar bayi
Fiksi SejarahA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid