28

11.3K 961 104
                                    

*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 28
Wattpad @afreey101

Please subscribe to my YouTube and support my channel @ dija bature
********************
"Bayan wata daya...

'A cikin wannan watan daya gabata, ba karamin shakuwa ce ta shiga a tsakanin jalal da juwairiya ba..
Duk lkcn zata shigo kyara masa daki toh sai sun samu lkc sun sha yar firar su duk da dai ba wani mgnr kirki bace amma hakan yana saka zuciyoyin su cikin tsantsar farin ciki...

"Kamar yau ma ta shigo sashen nasa danta gyara masa dakin ta tarar da baya ciki,tayi mamaki sosai da haka har ta kammala gyaran bata ganshi ba...

Ta fito falo kenan taji kuyangi nata kananan maganganu kasa kasa..
Shiga tayi cikinsu dan taji me suke fada..jitai sunce..

"Gsky Allah yayi wa sarki jalal kyawu"kin ganshi kuwa?kamar wani balarabe..
A take duk Suka shiga leken kofar wajen shakatawar sa..
Juwairiya tabi su itama sai hango shi tayi kwance akan kujerar lilo barci ya dauke sa..fuskar sa kamar me murmushi ga cute lips dinsa da dogayen eye lashes dinsa..

Ta kura masa ido tanajin yarda bayi keta kyasa sa,a ranta kuwa cewa tayi,duk son da nake maka nasan bazan taba samun ka ba...

Jakadiya ce tazo ta kore su daga wajen..
Sannan ta kalli juwairiya tace, kije waje magaji ya turo ayi masa kiran ki..
Mamaki ne ya kamata,me kuma zatayi wa magaji?

Fita tayi tabi bayan bawan da aka aiko kiran nata..
A gaban wata bishiyar mangoro taga bawan ya tsaya....
Sai hango magaji tayi a tsaye yana sakar mata murmushi ya jin gina jikinsa da bishiyar...

Tayi saurin gaishe shi..
Ya amsa mata a sake yana fadin..
Kinyi mamakin kiran da nayi miki ko?
juwairiya ta gyada kai..
Yace dama ina so ne na baki wata yar kyauta..
Juwairiya ta dago ta kallesa..
Ya nuna mata bishiyar yace na baki wannan bishiyar mangoron...
Juwairiya ta kwashe da dariya.
Magaji yabi ta da kallo yana jin sa a wani a irin nishadi...

Kafin yace,ba wasa nakeyi ba fa?
Kinga wannan bishiyar duk lkcn(season) din mangoro toh sai kin samu wanda yafi na ko ina zaki a jikinta..kuma a yarda na lura ke mayyar mangoro ce ko?

Juwairiya tayi murmushi tace toh nagode ranka ya dade..
Magaji ya samu waje ya zauna..
Sannan ya nuna mata waje itama ta zauna a can nesa dashi..

Magaji yaja lumfashi kafin yace, na san rayuwar bauta acikin wannan masarautar ba karamin wahala ne da ita ba,amma zuciyata na son taji dan tarihin ki ko kadan ne..
Duk da nasan a tarihin bayin dake cikin masarautar nan kece kadai aka taba haifa a cikin RUMFAR BAYI...

Juwairiya taja lumfashi, hakane ranka shi dade, amma ni rayuwata babu wani labarin da zan iya bada shi.. wanda baka sani ba..
Tun ina shekara goma na fara bauta..
Magaji yaji tausayinta har cikin zuciyarsa..
Ya jinjina kai...(yana tunani a zuciyarsa,kodai ya fada mata sirrin dake zuciyarsa ne?sai kuma wata zuciyar ta hane sa)
Ya kalle ta yace..
zaki iya tafiya nagode da lkcn da kika banu..
juwairiya ta mike kawai tayi masa godiya kafin ta fice..

*******************
"Washe gari..

"Umayma ce ta kalli surayya,Allah ya kara miki yawan rai..
ina tunanin kawai yakumbo ta bamu damar zuwa wajen bokan ta,
tunda dai har wata daya ya shude babu wani alamun ciki a tattare dake..
kuma kar na fara jin kusun kusun daga bayin dake sashen gimbiya kilishi,wai ta fara mgn a rashin haihuwar ku har wannan lkcn..

Surayya cike da takaici tace,nima ina wannan tunanin umayma..kema kin sani bazan taba bari wata ta haifawa jalal yaron da zaya gaje shi ba sai ni!ta nuna kanta!ni surayya! Shiyasa har gobe bazan bar ciyar da khadija wannan maganin ba har sai na samu MAGAJIN'SARKI..

Rumfar bayi Where stories live. Discover now