*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 29
Wattpad @afreey101_SORRY-am sorry fans jiya ban samu nayi muku update ba sbd school,kuyi hakuri da wannan..#teamjuwairiya #teamyarima #teamRumfarbayi_
Please subscribe to my channel on YouTube @ dija bature
****************"Juwairiya ce ta saka hannu ta amsa sarkar daga hannunsa ganin yayi shiru na tsawon wani lkc.
a tunanin ta ko fushi ne yayi dan taki amsar kyautar tasa..Jalal yayi firgigit yana kallonta cikin kwayar idonta..
Juwairiya ta sakar masa murmushi itama tace..
nagode sosai ranka shi dade Allah shi kara budi da tsawon rai..
Jalal ya rausayar da kai bai ce komai ba..
Sai hannu daya saka ya sake karbar sarkar daga wajenta sannan ya dawo zuwa bayanta ya tsaya..
Yana kokarin saka mata sarkar ne yake fadin..
"Kici gaba da hakuri juwairiya ki bani wani lkc zan sanar dake amsar tambayar ki nan ba da dadewa ba..."Umayma dake labe can bayansu tana leke dan ganin da wanda juwairiya take tsaye..taja tsaki..mtsw
Dan Duhu ne a wajen sosai sai inuwar su kawai take iya gani..gashi kuma mutumin ne a bayan juwairiya ta dan kare shi..Tsaki taja tana shirin juyawa ne kawai ta hango rawanin sa..
Gabanta ne ya shiga fadowa..
Dan kuwa babu wani mai dau'ra rawani haka face SARKI JALALLUDEEN,duk wanda yake kan mulki kawai ake yiwa wannan na'din rawanin...Ta shiga girgiza kanta ,inaaa ai ko kallo ma juwairiya bata ishe sa,namiji kamar jalal yana kuma matsayin sarki bazai kula mace kamar juwairiya ba..
Tabi inuwar da kallo tabbas sarki jalal dogon namiji ne kamar haka..
Cike da tunani kala kala ta juya da sauri tabar wajen...har tana hadawa da tuntube...* * * *
An tashi taro lafiya kowa yayi hanyar sa dan zuwa sauke gajiya..
Ni kuwa afrah nace bari na dan leko muku dakin sababbin ma'auratan."""""Lkcn da turaki ya karaso sashensa.. bayi jar sun gama shirya samira cikin kayan barcinta masu saukin gaske..
Ga kamshi tanayi sbd gyaran data sha.. an rufe mata fuska da mayafi dayaji ado sosai..
Yana shigowa dakin ya hangota a zaune kan gado mai rumfa irin na da din nan..Zuciyarsa ce yaji tayi masa wani iri,idan yana tuna irin mafarkin da yakeyi na son kasancewa da wacce zuciyarsa ke muradi..
Amma gashi sbd kawai suna jinin sarauta an tauye musu wannan hakkin..Tsaki yaja kawai ya samu waje akan kujera ya zauna abunsa ..
Samira taji shiru na wani dan lkc..
Ahankali ta bude mayafinta sai hango shi tayi a zaune ya dafa kai..Lumfashi taja tana tuna kalaman kakarta..
"Samira Kada kice dan mijin da aka hada ki dashi baya sonki ki zauna hakan ya riga damunki har ki jawowa kanki wani ciwo,yarda akayi miki dole shima fa haka aka yi masa,dan haka inaso ki zauna ku fahimci junanku kin gane?"
Samira ta sauko daga kan gadon ahankali ta dawo wajensa ta zauna..
Turaki yayi saurin dagowa ya kalleta..
Babu laifi samira kyakkyawa ce gata kuma da fara'a sosai dan murmushi yaga tana yi masa..
Jiyai tace..
Ka kwantar da hankalinka,nasan baka sona ko?Turaki ya kura mata ido,ita kuma wannan ya take?kai tsaye tana fadin tasan baya sonta?
Katse mishi tunani tayi da cewa..
Nima kuma bana sonka..!Se dayaji kalamanta har zuci..
Samira ta murmusa taci gaba da cewa dan haka kada wani abu ya dame ka,ai zamu iya kasancewa kawaye ko?Turaki ya samu kansa da gyada mata kai..
Samira ta mika masa karamin yatsan ta toh yimin alkawari..
Turaki ya samu kansa da sakin murmushi yana mamakin yarinta irin ta samira..
Samira ta daure fuska..
Bani mana..
Ganin bashi da niyyar yin abunda tace, yasa ta fisgo hannunsa da kanta ta kulla alkawarin kawancen nasu..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid