*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 37
Wattpad @afreey101*********************
""""Har jalal ya koma masaukinsa bai bar sakin murmushi me kayatarwa ba..
Magaji kam har ya fara gyangyadi yaji dawowarsa..
Yayi saurin mikewa yana kallonsa..cikin mamakin yace
Allah ja zamanka wai ina kaje ne haka..naji shiru tun dazu..Jalal ya dafa kafadarsa kawai yana sakar masa murmushi..
ya shige cikin daki yana ji inama daya kulle idonsa ya bude yaga har safiya tayi..
"A wajen juwairiya ma tana shiga sashen nata sukaci karo da hanne tana kokarin fita neman ta jin har lkcn shiru bata dawo ba..
Sai gani tayi juwairiya ta wuce ta bata ko lura da ita ba..tana rungume da hannayenta se murmushi takeyi...
Tayi saurin bin bayanta tace,uwar dakina!
Juwairiya tayi firgigit ta juyo ta kalleta..
Hanne ta kyalkyace da dariya..
Juwairiya ta turo baki tayi ciki da gudun ta
har ta kwanta a kan gadonta me laushi murmushi ne ke fita daga bakinta..
Ta jawo filo ta rungume sa tsam tana tunano fuskar jalal da yarda yake lumshe idanuwansa idan yana mgn..Lallai Allah me yarda yaso,wai ace sarki kamar jalal mai ji da kyau da farin jini a wajen mata shine ya so Baiwar kamar ta?a wancan lkcn..
Idonta ta murza,tabbas tayi dacen masoyi...
Wanda ya sota batan mulki ko wani abu data mallaka ba..Tunani sosai ta zurma har barci mai dadin gasken yayi awon gaba da ita.
**********
"Washe gari..
"Da sassafe jalal ya tashi yayi shirinsa tsab..
dan ba karamin kagara yayi garin ya waye ba..Koda magaji ya farka se ya tarar dashi har ya kammala komai shi kawai yake jira..
Magaji ya mike cikin mamaki yana fadin..
AMALE badai duk zangin komawa iyalin bane haka?Jalal ya harare sa..yace
Kayi ka shirya bani lkcn batawa malam.
Magaji yace,toh ranka ya dade...an gama.."A wajen Juwairiya kuwa..
Har makara tayi sallar asuba sbd irin dadin da barcin yayi mata..
har tayi wanka ta shirya amma ta rasa hanyar da zata samu haduwa da jalal dan ta fada masa amsar sa..
Tasan ko tace bata jinsa a ranta toh karya ne takeyi..Hanne ce ta shigo dakin tace da ita..
Uwar dakina yanzu nan gimbiya amina ta aiko wai kije sashen ta ku karya a can tare..Juwairiya ta jinjinar da kai sannan ta mike ta saka alkyabba a saman kayan jikinta suka fito daga cikin sashen..
Har sun fara tafiya juwairiya ta kalli hanne..tace..
Wai ni hanne Ta ina ne sashen bakin yake?
Wata hanya hanne ta nuna mata..
Juwairiya tace,muje ki rakani toh..Hanne tayi saurin shan gabanta..
Ah ah ranki ya dade ba girman bane ace kinje har can don neman sa ba..
Juwairiya taji kunya ta kamata,tace toh ya zanyi?hanne
Ina so ne na fada wani abu kuma kinga babu yarda zamu hadu dashi yau sbd komawa zayyi kasar su.Hanne taja hannunta zuwa bayan wani gini tace,jirani a nan ranki ya dade ina zuwa...da gudu tabar wajen juwairiya tabi ta da kallo..
"""" Juwairiya na nan a tsaye tana jiran dawowar hanne sai ji tayi an kamo hannunta daga baya..
Kamshin sane kawai ya daki hancinta..
Ta saki murmushi babu shiri..
Jalal ya rankwafo da kansa wajen kafadarta yace cikin(husky voice)..Yanzu har kina da ikon sakawa a kira miki sarki kamar ni ko..
Juwairiya ta juyo da sauri suka hada ido dashi..Jalal se da gabansa ya fadi ganin irin kyan da tayi....
Yace...
Fadi inajin ki..da gani bakin nan naki akwai mgn ko..?juwairiya ta rufe fuskarta da tafin hannunta..
tace toh ni me zance?.
Jalal yayi dariya..
Kunya ta kikeji ne haka?
Juwairiya ta gyada masa kai..
Yasa hannunsa ya cire hannayenta daga kan fuskar ta yace..
Toh bari na taimake ki..
KINA SONA?
juwairiya ta kura masa ido kafin tayi kasa da kanta da sauri tana murmushi..
Jalal ya sauke ajiyar zuciya..
Naji dadi sosai..sai ki shirya komawa KASAR DAURA cikin yan kwanankin nan..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid