22

11.6K 1K 110
                                    

          *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 22
Wattpad @afreey101

_gaskiya ina godiya sosai,my wattpad fans are rlly d best,hakama fans din rumfar bayi na whatsapp duk ina ganin comments dinku  Allah bar zumunci amin_

"Ahankali ya bude idanuwansa...

ya kalli fuskar surayya da barci  me nauyi ya dauke ta,
sannan ya saka hannu ahankali ya janyeta daga jikinsa ya sauko da kafafun sa kasa ya zauna a gefen gadon yana dafe kansa da duka hannayensa...

   Muryar jakadiya ce yaji yana sallamar bayin dake waje....
    Haka nan ya samu kansa da mikewa ya zura kaya a jikinsa..sannan ya saka takalmansa ya fito daga dakin..

Jakadiya da tsananin mamaki take kalle sa dan a duk tunaninta ya dade da yin barci.
tace,da fatan dai lafiya ko ranka ya dade?
Jalal yadan murmusa mata sannan yace,
lafiya kalau jakadiya zan dan fita ne na dawo ba da dadewa ba.
Ya sake yin kasa da muryarsa yace.. fitar sirri ce wannan dan haka ki rufa min asiri kinji?dan yasan jakadiya na iya sanar wa kilishi..

Jakadiya tayi murmushi, toh amma  bari na saka a kira maka shamaki se yayi maka rakiyar ko?
Jalal ya girgiza kai,ah ah ki barshi kawai ni kadai zan fita,bana son ma kowa ya san fitar kin gane?
jakadiya ta jinjina kai kafin ta karasa ta bude masa kofa ya fice..

************
"Tunda suka ba'ro sashen sarki suke ta buga sauri...
kasancewar dare ne babu wani isasshen haske a hanyar..
  Juwairiya da aka baro can baya ta daga murya tace..
Wai baza ku jirani bane..?
Wata baiwa dake cikinsu tace,kema ki daga kafa dan Allah kina tafiya kamar wata me tausayin kasar kinsan dai dare ne atooh..

  Juwairiya kamar zatayi kuka ta karawa tafiyar ta ta sauri,dan ita kam tana tsoron duhun nan sosai..

     Sun sha kwana kenan kawai taji an damko hannunta da karfi....
A mutukar tsorace ta kware baki zata saka ihu..sai ji tayi wani abu me shegen taushi ya rufe mata baki,sannan aka shiga janta da karfi...
    Fitsari ne kawai batayi ba sbd tsananin tsoron da fargabar data shuga...

   Can bayan wani kango aka sake ta duhu ne sosai a wajen dan haka tayi yunkurin guduwa tana laluben hanya...

Sai ji tayi kawai taci taro da mutum bum!
Lumfashi me tsayi taja dan ko ba'a fada mata ba tasan waye...
Kamshin sa kawai data ji yasa ta gane YARIMA NE....

Jalal ya sake kama hannunta suka dawo saitin da kawai dan haske a wajen..
  Yana sakin hannunta ta dago da sauri suka hada ido dashi..

  Jalal ya harde hannayensa yana kara matsawa gabanta..
  Tadan ja baya kadan..tana fadin..
Ka ka kayi hakuri ranka shi dade..
  Yarima yaja burki yana fadin,hakurin me zanyi?

Juwairiya ta girgirza masa kai..
Jalal yace,"nazo ne dan ki fada min amsar ki ta dazun?
  Ta dan ware ido,amsata wace kenan?ranka shi dade..?

Yarima ya gyada kai yana matse lebensa na kasa..
Dariya yaso ya bata,wato dan kawai yaji amsatar ta ne.. shine ya fito da a cikin daren nan?sannan kuma har ya baro matarsa a daki?ya biyo ta ita baiwa?.

  Ina jinki?ya fada yana gyara tsayuwarsa...
Juwairiya ta rasa me zata ce masa,bakinta ya shiga rawa....
Ni ni ai babu wani zabi a gare ni,duk inda kuka kaini ai dolene naje nayi aikina..

    Mgnr  da tayi ne yasa jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa,wato ita baiwar su ce duk inda suka ajiyeta a nan zata zauna..

  Juwairiya jin yayi shiru...
sai ta dan sace kallon sa da gefen idonta..
   Wai me yasa yarima ya fiya kyau ne haka?taji zuciyarta na tambayar ta..
  Jitai yace..
"Ki shiga dakina gobe ki gyara min shi"(hakanan ya tsinci kansa da fadin hakan,dan zuciyarsa na mutukar kwadayin ganinta a kullum)

Rumfar bayi Where stories live. Discover now