*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 31
Wattpad @afreey101Please subscribe to my channel on YouTube @ dija bature
*****************"A gaban dun'bin jama'a waziri ya Yan'tar da baiwa juwairiya kamar yarda al'adar masarautar tasu take..
"Wani irin lumfashi me nauyi ta sauke....
farin ciki sosai ya ziyarci zuciyarta bata taba jin irin wannan yanayin ba a duk rayuwarta..
Jalal kansa sai da yaji wani irin sanyi acikin zuciyarsa,yau kam zai zama tahiri babba a wajensu,daga inda yake yana kallon yarda juwairiya ke ta sakin murmushi hakan ba karamin dadi yayi masa ba..Hansai da sauran bayi ne suka shiga congratulating din juwairiya cike da murna su,suna ji dama ace sune aka yantar,dan a wajensu idan aka yantar da baiwa kamar an sake haihuwar ta zata fara sabowar rayuwa me cike da yanci da farin ciki.
Addu'a akayi taro ya watse...
"Jalal na fitowa daga fa'da ya koma sashen sa ya saka jakadiya ta turo masa juwairiya can bayan sashensa su hadu yana da mgn mahimmiya da yake yayi mata..
Jakadiya ta jinjinar dakai tana tuna lkcn da suka sanar mata taimakon da turaki yayi mata da kuma furucin da yayi na sonta,ko yanayin fuskarta se da jakadiya ta fahimci juwairiya bata son turaki,jalal ne a zuciyarta.."Zainaba ba karamin murna tayi ba ta makakkale juwairiya a jikinta,tana jin dadin yarda zata iya hada jikinta da ita a yanzu..
samira ce ta karaso wajensu tare da khaleed dan uwanta, dukkanin su mamakin kamanni ta sukeyi da Ammi har lkcn.
samira tace,na taya ki murna sosai..
Juwairiya ta murmusa cike da farin ciki tace nagode kwarai..
Khaleed ya kura mata ido yana tunanin zancen su da sarki jalal yau da asuba Allah yasa yarinyar ta amince..
Wani bawa ne yazo wajen yayi kiran samira,tayi musu sallama ta kama gabanta.."A daki samira ta tarar da turaki a zaune..
Ta karasa wajensa tace..
Gani ance min kana kirana..
Ya dago ya kalleta..kafin yace..
Nayi tunani akan maganar ki ta jiya..
Surayya tace, kuma me ka yanke hukunci akai..zaka tilasta mata auranka ne,ko kuwa ?Turaki yace bazan taba yiwa juwairiya dole ba..dan haka bashi ne niyya ta ba..
Samira ta saki murmushi tace,naji dadin yarda ka zauna kayi tunani me kyau haka ,
yantar da ita da kayi ma ya isa ka taimaka mata sosai..
sai dai fa ni wlh wannan juwairiyar tana min kama da AMMI sosai..Turaki ya gyara zama..
Me kike nufi?wacece kuma Ammi?
Samira tadan muskuta..
Ammi amaryar mai martaba ce wato kakana..
Turaki ya girgiza kai,babu alakar da zata hada Juwairiya da ita gsky dan kuwa iyayen juwairiya a cikin masarautar nan suka haife ta kuma naji lbrn yan asalin kasar daura ne..
Samira ta jinjina kai hakane nima nayi wannan tunanin...*******
"Jakadiya ce ta samu juwairiya ta sanar mata da sakon jalal..
Kallon jakadiya tayi a dan tsorace..dan bata zaci tasan me ke tsakanin ta da yarima ba..Jakadiya tajawo ta zuwa gefe tace..
Kada ki damu juwairiya ina bayanku keda AMALE..yanzu kije yana kiran ki..Juwairiya na daga kafarta taji wani irin faduwar gaba,muryoyi ta shiga ji a kunnen ta kamar ana kwala mata kira..
Waige waige ta shiga yi..
Fuskokin su laure,hansai,rabi,zabba'u, zainaba kawai take kallo dake wajen tana jin wani irin abu yana tokare mata wuya..Gaba daya jikinta ya hau rawa..
Jakadiya tace,kije mana kinsan ba'a barin Amale jira..
juwairiya ta gyada kai,tana tafiya ne kawai amma gaba daya zuciyarta a dakule take..ji takeyi gaba daya gangar jikinta bata kaunar zama acikin masarautar.."Jalal kuwa na zaune akan wani dan dakali yana ta faman zuba ido..
Duk ya rame sbd tunanin da saka a gaba yanayi duk lkcn da yake shi daya..Yanzu dai addu'ar shi daya ce Allah yasa ta amince da (plan)dinsa...
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid