*RUMFAR BAYI*
( A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 27
Wattpad @afreey101**********************
Subscribe to my YouTube channel @dija bature
"Jalal ya gyara zamansa yana kallon zainaba cike da tausayin irin tata kaddarar ..
"Ki kwantar da hankalinki kanwata kawai kici gaba da addu'a Allah ya zaba miki abunda yafi alheri kinji,ke da ma ko fara mgnr auren ki abba bayyi ba..
Zainaba tace,ah ah yaya dan Allah nidai ka taimake ni,nasan idan kayi wa abba bayani bazai ki amincewa ba..
Jalal ya rasa me zai ce mata,sbd dai magajin nan amininsa ne kuma yasan waziri ma bazai taba aminta ba ace an bawa dansa zainaba kuma taje ta auri wani can daban.."Zabba'u ce ta shigo falon da sallama..
Zainaba tace,yadai zabba'u ya na ganki ke kadai?ina juwairiyar?Zabba'u tayi fuskar tausayi..
Ranki ya dade juwairiya fa bata jin dadi tun kwana biyu da suka wuce..Hankalin zainaba e ya tashi mutuka,a take ta mike tsaye tana fadin,shine baki sanar min ba?
Zabba'u tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma itace tace min kada na fada miki dan tasan hankalinki ne zai tashi..Zainaba jiki na rawa tace,muje na ganta..
Da sauri zabba'u ta shiga gabanta, ranki shi dade kin manta bazaki iya shiga rumfar bayi ba..Zainaba taja tsaki ta koma ta zauna cikin takaici..
Jalal kuwa duk yana saurarensu,hankalinsa ba karamin tashi yayi ba shima..
Dama bata da lafiya ne?
Toh Meya same ta?
A wane hali take ciki yanzu?
Mikewa yayi kawai ba shiri yayi sallama da zainaba sama sama ya fice.."Gaba daya a ranar jalal tunanin yarda zai saka juwairiya a idonsa yakeyi..yana son yaji ko ya jikinta da sauki ko yayi tsanani?amma bashi da me bashi wannan amsar..
Da yamma magaji ne yazo yaja shi da kyal suka je yin wasan doki..(Polo )
Lkcn daya dawo sashen sa sai ya tarar da khadija a dakinsa tana zaman jiransa...
Tsaki yadan ja yana mamakin nacin wadan nan matan nasa..kullum sai sun kawo kansu wajen miji..mtsw.."Khadija kuwa tana ganinsa ta saki murmushi, ya jalal sannu da shigowa..
Jalal yace,yauwa a takaice..Khadija taje ta kamo hannunsa ya jalal wai nayi maka laifi ne?
Jalal ya kalleta,laifin me zakiyi min khadija..?Ta shagwabe fuskarta..
toh ba naga ne daga ganina da kayi ba sai ka wani daure fusaka,kamar bakayi wani farin cikin ganina ba..Jalal yayi murmushi ya shafa gefen fuskarta yace..
ba haka bane..kawai dai abubuwa ne sukayi min yawa..
Khadija ta rungume sa,kada ka damu komai zaizo maka da sauki idan akayi sabon na'din (palace counsel)...*********
"Wasa wasa juwairiya jiki sai daya kai ta har kusan kwanaki biyar bata fita daga cikin rumfar bayi ba tana ta jinya...Sai dai tana samun sako daga wajen zainaba dan har fulani kanta ta saka aka kawo me magani ta shiga har cikin rumfar bayi ta duba ta..
"Yau kam ta tashi jikinta da sauki sosai tana zaune ne kwanon abinci a gabanta tana ta faman tsakurar sa kamar bataso..
Tunani kawai takeyi yarda take jin zuciyarta kamar tayi tsuntsuwa ne taje sashen yarima ta dan gan sa..
hansai ce ta kalleta duk ta rame tace,juwairiya kodai sai na nemo miki maganin cin abincin ne?
Juwairiya tayi murmushi kada ki damu umma,kawai bakina din ne babu wani dadi shiyasa..hansai ta jinjina kai kawai.."Mai martaba ina tunanin kawai a kai mutanen nan gidan yari..
"Magaji dake zaune gefen jalal suna cikin fada ya fada..Ji yayi jalal bai ce masa komai ba,dan haka ya dago yana kallonsa..
Ya rasa meke damun abokin na sa kwana biyu haka bashi da wani nutsuwar kirki kullum se dai ya zauna shiru..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid