*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 14
Wattpad***************
"Gidan wani babban dan kasuwa sukaje wanda yana cikin manyan yan kasuwa na duniya gaba daya..
gidane na zamani mai kyan gaske gashi makeke sosai har yaso ya tsorata su juwairiya...' Zo kuga kallo kuwa wajen su, rabi har dasu sakin baki,tana zungoro juwairiya da zabba'u..
A waje suka zauna kan wasu fararen kujeru masu kyau su kuwa su yarima suka shige ciki dan an aiko wani ya shigar dasu..."Sun dade a zaune wajen, juwairiya gaba daya zaman ya gundure ta,dan tun suna firar kyaun gidan har kowa ya gaji yayi shiru..
mikewa tayi tana dan shawagi a wajen..can ta hango wasu fure masu kyan gaske dan bata taba ma ganin irin su ba a can kasar tasu (rose flower)
Da sauri tayi wajen tasa hannu ta tsi'go daya tana murmushin ta mai kayatarwa..***************
Yarima tare da magaji na tare da wannan babban dan kasuwan dan isar da sakon mai martaba na son fara fafada kasuwancin sa a nan kasar ta chadi.Yarima ya gama bayani ya dauki cup din tea da a gabatar musu yayi dan sipping kadan...
Ya gyara zamansa...
Open glass din dake gefen su ya kalla...
Can ta hango ta rike da furen a hannu ta na dama tana murmushinta...Hakanan yaji ta burge sa sosai ga view din wajen se ya kara mata kyau a idon yarima,ya murmusa kawai yana kokarin dauke kansa ne kawai yaga wani saurayi na karasawa wajen ta...
********
"Yan mata ya kike?
Taji an fadi da hausar da bata goge sosai ba..
Ta dago ta kalleshi da rashin sani...
Lafiya ta fada tana rusunawa kasa..
Yace No ah ah basai kin rusuna min ba,kema din da mutanen nigeriyar kika zo?Juwairiya tace eh tana dukar dakai..
Ya saki wani irin shu'umin murmushi yana karewa jikinta kallo...dan ya fahimce baiwa ce ita...
Furen hannun ta ne ya fadi kasa sbd tsabar a tsorace take sosai,jikinta har rawa yakeyi ganin irin kallon da mutumin yakeyi mata har da yashi leben sa..Da sauri ta du'ka dan daukar furenta tayi gaba..
Kawai sai jin hannunsa tayi a kugunta yana shafata...
A firgice ta dago tana kallonsa cike da tsoro..
Miye....ha...ka?muryarta na rawa ta fada..Yayi mata murmushin yaudara..
Yan mata ina son irin ki sosai,zaki zauna dani?zan siye ki da kudi masu yawa na baki ga'ta da yan'ci....
Mamakin kalamansa tayi sosai...kuka ne yazo mata ba shiri dama abunda ake fada kenan?yau ta shiga ukun ta..
Shi kuwa ganin haka sai yasa hannu ya jawo ta jikinsa wai ze lallashe ta..**************
"Yarima gaba daya wutar sa daukewa tayi,fushi da takaici ya mamaye zuciyarsa ,cup din dake hannunsa ne yayi wurgi dashi da karfi...Duk su magaji suka kalleshi da sauri cike da mamaki.
Ya mike kawai cikin bacin ran da baisan me yasa yake jinsa ba yayi waje...
""""Juwairiya nata kokarin ture mutumin daga jikinta cike da tsoro,kuka takeyi sosai ganin wani irin sabon al'amarin da bata taba fuskantar irin shi ba,duk da tabon dake fuskarta amma wannan mayen mutumin sai da ya tunkare ta haka,ko su nan basa kyamatar masu tabon ne...Bata ankara ba sai ji tayi an fisgo mutumin cikin karfin gaske..
Tayi sauri ja da baya tana kallon yadda yarima ke saukar wa mutumin nan tagwayen marika..Mamaki sosai ne ya rufe ta,meyasa yarima ke taimake ta,wacece ita?ita ba kowan kowa ba banza baiwa marar galihu...
Da kyal magaji ya amshi mutumin daga hannun yarima yana mamakin karfin halin sa..gashi kuma wannan deal din da sukazo dashi da kyal ne ya zama successful tunda yarima ya gama kufsa musu...Dan kasuwan kuwa ba karamin fushi yayi ba dan kuwa kanin sane yarima ya gama jubga,su tafi kawai yace musu zasu ji daga gare sa idan yayi shawara....
Yarima ko a jininsa suka tattara sukayi gaba.
Juwairiya kuwa hawaye basu dauke mata ba su rabi ne ke ta lallashinta...

YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid